Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Glosbe's example sentences of age [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar age:
    1. In 1952, Ádám, who by now was 29 years of age and married with two children, was arrested and charged when he once again refused military service.
      A shekara ta 1952, Ádám, ɗan shekara 29 a lokacin ya yi aure da yara biyu, aka kama shi aka tuhume shi da laifin ƙin aikin soja. [2]

    2. How might betrayal find a niche in a marriage, and why is a person’s age not an excuse for that to happen?
      Mene ne yake jawo cin amana tsakanin ma’aurata kuma me ya sa shekarar mutum ba hujja ba ce? [3]

    3. Do not throw me away in the time of old age; just when my power is failing, do not leave me.”
      Kada ka yashe ni cikin kwanakin tsufa; kada ka yarfarda ni lokacin da ƙarfina ya ƙare.” [4]

    4. 9 Because of age, experience, or natural abilities, some elders may be more efficient than others, or they may be endowed with greater insight.
      9 Domin yawan shekaru, fahimi, da kuma iyawa, wasu dattawa za su fi wasu, ko kuma za su kasance suna da fahimi ƙwarai. [5]

    5. “Even to one’s old age I am the same One; and to one’s gray-headedness I myself shall keep bearing up.” —ISAIAH 46:4.
      “Har tsufarku kuma, ni ne shi, har zuwa furfuranku kuma ni zan ɗauke ku.”—ISHAYA 46:4. [6]

    6. At a young age, Timothy began a life devoted to the Christian ministry
      Timotawus ya soma hidima ta cikakken lokaci tun yana matashi [7]

    7. When a couple truly love each other, they remain together even if a physical relationship is no longer possible because of the infirmities of old age or because one of them is incapacitated.
      Idan mata da miji suna ƙaunar juna da gaske, za su zauna tare ko idan babu sha’awa ta jiki kuma domin raunana ta tsufa ko kuma ɗaya cikinsu ya naƙasa. [8]

    8. Beginning at age seven and throughout her years in elementary school, this young girl invited her teachers to the Kingdom Hall whenever she had an assignment in the Theocratic Ministry School.
      Tun lokacin da take ’yar shekara bakwai har ta kare makarantar firamare, wannan yarinyar tana gayyatar malamanta zuwa Majami’ar Mulki duk lokacin da take da aiki a Makarantar Hidima ta Allah. [9]

    9. The Scriptures give no age requirements for baptism.
      Nassosi ba su ba da ainihin shekarar da za a kai kafin a yi baftisma ba. [10]

    10. To help people grasp the age of the universe as estimated by scientists, one planetarium features a time line 360 feet (110 m) long.
      Don a taimaki mutane su fahimci shekarun sararin samaniya yadda ’yan kimiyya suka kimanta, wata na’ura ta zana taswirar lokaci mai tsawon ƙafa 360. [11]

    11. Born on September 28, 1925, in Pike County, Kentucky, U.S.A., Brother Jaracz symbolized his dedication to Jehovah at the age of 15, on August 10, 1941.
      An haife shi a ranar 28 ga Satumba, 1925, a garin Pike Country, Kentucky, a Amirka, kuma Ɗan’uwa Jaracz ya nuna ya keɓe kansa ga Jehobah ta wajen yin baftisma sa’ad da yake ɗan shekara sha biyar, a ranar 10 ga Agusta, 1941. [12]

    12. For example, Rex, who is now 89 years of age, has been a full-time evangelizer since 1931.
      Alal misali, Rex, shekararsa 89, yana hidima ta cikakken lokaci tun shekara ta 1931. [13]

    13. (Psalm 145:16) As we age, our desires change.
      (Zabura 145:16) Sa’ad da muke girma abubuwa da muke so suna canjawa. [14]

    14. 31:1) Young Josiah became king when he was only eight years of age.
      31:1) Josiah ya zama sarki sa’ad da yake ɗan shekara takwas. [15]

    15. In 1916, Brother Russell died at only 64 years of age, leaving many of God’s people in shock.
      Ɗan’uwa Russell ya rasu a shekara ta 1916, yana da shekara 64, kuma rasuwarsa ta gigita bayin Allah da yawa. [16]

    16. According to that verse, upon Solomon’s death his son Rehoboam became king at age 41, his mother being “Naamah the Ammonitess.”
      Kamar yadda ayar ta nuna, bayan Sulemanu ya rasu, ɗansa Yerobowam ya zama sarki sa’ad da yake ɗan shekara 41, kuma sunan mahaifiyarsa ‘Naamah ce, Ba-ammoniya.’ [17]

    17. But advancing age may now limit what they can do, so adjustments become necessary.
      Amma wataƙila yanzu ba za su iya yin aikin da suka saba yi ba don su soma tsufa. [18]

    18. In spite of this, I continued to make spiritual progress and was baptized in 1951 at the age of 17.
      Duk da haka, na ci gaba da bauta wa Jehobah kuma aka yi mini baftisma a shekara ta 1951 sa’ad da nake ’yar shekara 17. [19]

    19. He began serving as a regular pioneer at age 17 and was appointed as a ministerial servant at 18.
      Ya soma hidimar majagaba na kullum sa’ad da yake ɗan shekara 17, kuma ya zama bawa mai hidima sa’ad da yake shekara 18. [20]

    20. (James 1:27) Sadly, at the age of 53, Sozos died of a brain tumor.
      (Yaƙub 1:27) Amma abin baƙin ciki shi ne, da Sozos ya kai shekaru 53 sai ya rasu sanaddiyar ciwon kansa na ƙwaƙwalwa. [21]

    21. Is the Bible outdated in our modern age?
      Shin Littafi Mai Tsarki tsohon yayi ne? [22]

    22. And even until old age and gray-headedness, O God, do not leave me.”
      I, har lokacinda na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah.” [23]

    23. To what extent should age be a factor?
      A wane lokaci ne ya kamata a yi la’akari da shekaru? [24]

    24. In some countries, children begin preschool at an early age, sometimes when they are only two years old.
      A wasu ƙasashe, yara sukan soma makaranta sa’ad da suke ƙanana, a wasu lokatai ma sa’ad da suke ’yan shekara biyu kawai. [25]

    25. What a marvelous hope —sickness and old age will be no more, you can live on to enjoy the fruits of your labor, and there will be peace with the animals!
      Lalle sa zuciya ne mai girma—ciwo da tsufa ba za su ƙara kasancewa ba, za ka rayu ka more riban aikinka, salama za ta kasance tare da dabbobi! [26]


Retrieved June 23, 2019, 12:12 pm via glosbe (pid: 7777)