Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:aikin gida

Discussion page of aikin gida

Glosbe's example sentences of aikin gida [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar aikin gida:
    1. Sojan da ya ci yaƙi zai iya kawo wani bawa gida don ya taimaka wa matarsa da aikin gida.
      A victorious soldier might bring a foreign captive home as a slave to provide his wife help with chores. [2]

    2. Sau da yawa yana da wuya a yi musu wa’azin saƙon Mulki domin suna zama a wuraren da masu arziki suke zama inda ’yan aikin gida ne suke buɗe ƙofa.
      It is often difficult to share the Kingdom message with them because they live in affluent areas where maids answer the door. [3]

    3. Aikinta na ’yar aikin gida ya ƙunshi yin aiki na sa’o’i masu yawa da kuma yin tafiya mai gajiyarwa a motar haya da ke cike da mutane.
      Her job as a maid involved working long hours and making tiring journeys in packed urban transportation. [4]

    4. Hakan ya sa in gama aikin gida kuma mu tafi taro a kan lokacin da muka tsara.”
      This allows me to finish my housework and get myself ready to leave for the meetings at a set time.” [5]

    5. Yadda matasa suke taɗi da tsofaffi cikin ikilisiya da yadda suke aikin gida zai nuna cewa za su iya kula da hakki mai girma da kyau a rayuwa ta gaba.—Luka 16:10.
      The way in which youths interact with older ones in the congregation and the way they take care of simple chores at home will indicate that they can likely care well for greater responsibilities later on in life. —Luke 16:10. [6]

    6. Za a zaɓa misalai daga wurare dabam dabam, haɗe da na abubuwa masu rai da marasa rai, kayayyakin aikin gida, ko kuma abin da ya faru na kwanan baya a yankin.
      Illustrations can be chosen from many other sources, including animate and inanimate objects, household items, or a current event well-known in the community. [7]

    7. Da akwai kuma waɗanda suke tunanin cewa zuwa a yi aiki a waje yana kawo kuɗi, amma aiki a gida ko kuma wasu aikin tsabtace gida ba su da riba.
      There also are those who reason that going out to work pays the bills, whereas housework or other cleaning chores are of no financial value. [8]

    8. Evelyn ta soma aikin sharan gida, ni kuma na samu aikin shara na tsakar dare a gidan abinci na ’yan Italiya.
      Evelyn cleaned houses, and I found a late-night cleaning job in an Italian restaurant. [9]

    9. Jeanine ta zaro wata matsala kuma: “Kalubale ne ƙwarai na ƙi ba da aikin zama shugaban gida wa yaro domin ya cika gurbin da maigidan ya bari.
      Jeanine brings up another problem: “It can be a real challenge to reject the tendency to make your son the head of the household so as to make up for the absence of a husband. [10]

    10. An soma aikin wa’azi gida-gida na ranar Lahadi a shekara ta 1927.
      Regular house-to-house work on Sundays was organized in 1927. [11]

    11. Ƙari ga haka, suka ba da kansu ga aikin sake gina wani gida ya zama Majami’ar Mulki.
      In addition, they expended themselves in the work of remodeling a local residence into a fine Kingdom Hall. [12]

    12. Kafin a sani, yin wa’azi gida-gida ya zama aikin da aka fi sanin Kiristoci na gaskiya da shi. Hakan ma yake a yau.
      Before long, preaching from house to house became a hallmark of those faithful Christians —as it is till this day. [13]

    13. Iyayena sun ƙara min aikin da nake yi a gida don kada na riƙa fita waje.
      My parents increased my chores in an attempt to keep me indoors. [14]

    14. A watan Janairu na shekara ta 1943, ba da daɗewa ba bayan na kai gida, na kuma soma aikin wa’azi.
      In January 1943, soon after I reached home, I again began to share in the preaching work. [15]

    15. Za mu iya gani kamar yin aikace-aikacen gida da makaranta da aikin karɓan albashi da yin cefane da kuma sauransu ba za su iya shafan dangantakarmu da Allah ba.
      Housework, schoolwork, secular work, shopping, and the like might on the surface seem to have little to do with spiritual concerns. [16]

    16. Da ake bincika yaron, likitar Janina* ta tambayi Dorota game da irin aikin da ɗanta yake yi a gida.
      During the examination, the doctor, Janina,* asked Dorota about her son’s duties at home. [17]

    17. Da suka iso ɗakin bene, babu ɗaya cikin manzanni 12 da yake so ya wanke ƙafafu masu ƙura na wasu—aikin bawa ko kuwa mace a gida.
      On arriving in the upper room, not one of the 12 apostles took the initiative to perform the customary service of washing the dusty feet of the others —the menial task of a servant or of a woman in the household. [18]

    18. Hakika, ɗalibai suna bukatan su yi karatu da kuma aikin da aka ba su na gida idan suna son su ci jarabawa.
      Naturally, students need to study and do their homework to pass the exams. [19]

    19. To, idan ya kamata ka yi aikin da aka ba ka na gida, amma ka yi wasu ne cikinsu kawai fa?
      What if you were supposed to do your homework but you did only part of it? [20]

    20. Duk da haka, aikin da suke yi da kuma ayyukan gida sun sa ba su da isashen lokacin yin wa’azi.
      Yet, their work schedule and jobs around the home left little time for field service. [21]

    21. IYAYENA: Idan kai yaro ne, yaya biyayyata take ga iyayena—ina amsa musu da ladabi, ina yin aikin da suka ba ni, ina dawowa gida lokacin da suka ce, ina kauce wa tarayya da ayyuka da suka ƙi?
      MY PARENTS: If still a minor, am I obedient to my parents —answering respectfully, doing assigned chores, coming home at whatever time they set, avoiding associations and activities that they warn against? [22]

    22. 15 Ana iya gama gina gida, amma duk da haka aikin zai ci gaba.
      15 Construction of a house may be completed, yet work goes on. [23]

    23. Sau da yawa, irin aikin da suke yi yana sa su bar gida tun daga safiya har yamma.
      Often, their job requires that they be away from home for most of the day. [24]

    24. Ta yaya addu’a take da nasaba da aikin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida?
      How is prayer related to the work of conducting home Bible studies? [25]

    25. Dubbai sun bar gida da iyalai don su shiga aikin wa’azi na ƙasar waje a ƙasashen da sukan koyi sabon yare da al’adu.
      Thousands have left home and family to take up missionary service in lands where they have had to adapt to new languages and cultures. [26]


Retrieved June 23, 2019, 6:12 pm via glosbe (pid: 20809)