Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:approval

Discussion page of approval

11:2-6 —If because of having heard God’s voice of approval John already knew that Jesus was the Messiah, why did he ask if Jesus was “the Coming One”?

11:2-6—Idan saboda muryar Allah na amincewa da ya ji ya sa Yohanna ya san cewa Yesu ne Almasihu, me ya sa ya yi tambaya ko Yesu ne “mai-zuwan nan”?



However, it is not the approval of humans that we seek.

Duk da haka, ba ma neman amincewar ’yan Adam.



All who desire divine approval today must exercise similar faith, dedicate themselves to Jehovah God, and undergo Christian baptism in symbol of an unreserved dedication to the Most High God.

Dole ne dukan waɗanda suke son samun amincewar Allah a yau su kasance da irin wannan bangaskiyar, su keɓe kansu ga Jehovah Allah, kuma su yi baftisma ta Kirista alamar keɓe kai babu ragi ga Allah Mafi Girma.



How will applying his counsel help us to merit Jehovah’s approval?

Ta yaya bin wannan shawarar zai taimaka mana mu samu amincewar Jehobah?



There is no way we can have God’s approval except through Jesus Christ.

Babu yadda za mu sami tagomashin Allah sai ta wurin Yesu Kristi.



The king who would have Jehovah’s approval needed to pursue such study to develop and retain the right heart attitude.

Wannan sarki da zai sami tagomashin Jehovah yana bukatar ya yi irin nazarin nan kuma ya kasance da zuciyar kirki.



The anointed ones and those with an earthly hope will indeed “stand” in that day with God’s approval.

Shafaffu da kuma “taro mai-girma” za su “tsaya” domin Allah ya amince da su.



• Why should we seek God’s approval?

• Me ya sa za mu biɗi amincewar Allah?



Those moments were painful, but they resulted in feelings of peace and approval.” —James 5:16.

Ko da yake na ji nauyin neman taimako, amma yanzu na sami kwanciyar hankali da kuma lamiri mai kyau.”—Yaƙub 5:16.



Jehovah’s approval is seen in how he blesses his people with increase, guidance in important decisions, better comprehension of Bible truths, safeguards against annihilation at the hands of their enemies, and peace of mind and heart. —Isa.

Ana ganin alamar cewa Jehobah ya amince da rukunin bawan a yadda yake yi wa mutanensa albarka ta wajen sa adadin mutanensa su ƙaru da yadda yake ja-gorance su su tsai da shawarwari masu muhimmanci da yadda yake sa su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai da yadda yake kāre su don kada magabtansu su halaka su da kuma yadda yake ba su kwanciyar hankali.—Isha.



16 In some cultures, parents, older ones, and teachers rarely express wholehearted approval of younger ones, thinking that such praise might make them complacent or proud.

16 A wasu al’adu, da kyar iyaye, tsofaffi, da malamai su yabi matasa da dukan zuciyarsu, suna tunani cewa irin wannan yabo zai iya sa su zama ragwaye ko masu girman kai.



3 Satan the Devil does not want us to seek God’s approval.

3 Shaiɗan ba ya so mu sami amincewar Jehobah.



(1 John 2:15-17; 3:15-17) If not corrected, such pursuits and traits can result in the practice of serious sin and the eventual loss of Jehovah’s approval.

(1 Yohanna 2:15-17; 3:15-17) Idan ba a lura ba, irin halayen nan da biɗe-biɗe za su sa mutum zunubi kuma ya yi rashin amincewar Jehovah.



Nehemiah’s prayer attests to the truthfulness of King David’s words: “You yourself will bless anyone righteous, O Jehovah; as with a large shield, with approval you will surround them.”

Addu’ar Nehemiya ta tabbatar da gaskiyar kalmomin Sarki Dauda: “Za ka albarkaci mai-adilci; Ya Ubangiji, da tagomashi za ka kewaye shi kamar da garkuwa.”



But as a husband, he finds that he must use some of that time and energy to care for his wife and thus gain her approval.

Amma yanzu da ya zama maigida, ya ga cewa wajibi ne ya yi amfani da wasu cikin lokacinsa da kuzarinsa don ya kula da matarsa kuma ya faranta mata rai.



8 Gaining God’s approval involves the proper exercise of our free will.

8 Samun amincewar Allah ya ƙunshi yin amfani da ’yancinmu yadda ya dace.



When we endure faithfully and thus realize that we have God’s approval, this has the profound effect of adding to and strengthening our initial hope.

Yayin da mun jimre cikin aminci kuma ta haka muka gane cewa Allah ya amince da mu, wannan yana da amfani sosai na ƙara kuma na ƙarfafa sa zuciyarmu da muke da ita a farko.



Accordingly, Jesus knew that he had his Father’s love and approval.

Saboda haka, Yesu ya san cewa Ubansa ya amince da shi kuma yana ƙaunarsa.



Zealously sharing in Jehovah’s work brings his approval and blessing.

Saka hannu a aikin Jehobah da himma na kawo amincewarsa da albarka.



Will we show greater concern for gaining Jehovah’s approval than for seeking material security?

Shin za mu fi damuwa da samun abin duniya fiye da samun amincewar Jehobah?



Remember: To have God’s approval, we must endure. —Rom.

Ka tuna cewa: Idan muna so Allah ya amince da mu, wajibi ne mu jimre. —Rom.



Children draw strength and courage from parental approval

Yara suna ƙarfafa kuma suna kasancewa da gaba gaɗi idan iyayensu sun amince da su



For instance, just after Jesus was baptized, marking the start of his ministry, he heard his Father’s voice expressing approval and confirmation of His love for him.

Alal misali, sa’in da aka yi wa Yesu baftisma, alamar soma hidimarsa, ya ji muryar Ubansa da yake tabbatar da amincewarsa da ƙaunar Uban gare shi.



13:17) By doing so, we benefit ourselves as recipients of Jehovah’s approval and blessing. —Isa.

13:17) Ta yin hakan, za mu amfani kanmu a matsayin waɗanda za su samu amincewar Jehobah da kuma albarkarsa.—Isha.



Commendation and approval are to a child what sunshine and water are to a plant.

Yabo da kuma amincewa ga yaro sun yi daidai da yadda ruwa da hasken rana suke yi wa shuki.