Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:beloved

Discussion page of beloved

Glosbe's example sentences of beloved [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar beloved:
    1. He wrote to the congregation in Thessalonica: “Having a tender affection for you, we were well pleased to impart to you, not only the good news of God, but also our own souls, because you became beloved to us.”
      Ya rubuta wa ikilisiya da ke Tasalonika: “Muna ƙaunarku ƙwarai da gaske ne ya sa muke jin daɗin ba da har rayukanmu ma saboda ku, ba yi muku bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga ranmu da gaske.” [2]

    2. He states: “Do not avenge yourselves, beloved, but yield place to the wrath; for it is written: ‘Vengeance is mine; I will repay, says Jehovah.’”
      Ya ce: “Kada ku ɗauka ma kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce ma fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” [3]

    3. “This is my Son, the beloved, whom I have approved.” —Matthew 3:17.
      “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.”—Matta 3:17. [4]

    4. In like manner, Jehovah God and his beloved Son have purchased Adam’s offspring and canceled their debt of sin on the basis of Jesus’ shed blood.
      Hakazalika, Jehobah Allah da Ɗansa ƙaunatacce sun sayi zuriyar Adamu kuma suka yafe musu bashinsu na zunubi bisa jinin da Yesu ya zubar. [5]

    5. After Paul had worked hard to build the faith of Christians in Philippi, he wrote to them: “Consequently, my beloved ones, in the way that you have always obeyed, not during my presence only, but now much more readily during my absence, keep working out your own salvation with fear and trembling.”
      Bayan Bulus ya yi ƙoƙari sosai ya gina bangaskiyar Kiristoci a Filibi, ya rubuta musu: “Saboda haka ya ƙaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya, haka yanzu kuma, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba wai sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.” [6]

    6. To this day, anointed Christians along with their dedicated associates, the “other sheep,” flourish as a Kingdom-preaching organization under the mighty hand of God and the leadership of his beloved Son. —Eph.
      Har yanzu, shafaffun Kiristoci tare da keɓaɓɓun abokansu, “waɗansu tumaki,” suna samun ci gaba a matsayin ƙungiyar masu wa’azin Mulki a ƙarƙashin ikon Allah da kuma shugabancin ƙaunataccen Ɗansa.—Afis. [7]

    7. Become imitators of God, as beloved children, and go on walking in love, just as the Christ also loved us and gave himself for us. —Eph.
      Ku zama fa masu koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu; ku yi tafiya cikin ƙauna, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunace ku, ya ba da kansa kuma domin ku.—Afis. [8]

    8. He realized that he had just done the very thing that Jesus had foretold, the one thing that Peter had insisted he would never do —he had disowned his beloved Master.
      Ya fahimci cewa ya yi ainihin abin da Yesu ya annabta, abin da Bitrus ya nanata cewa ba zai taɓa yi ba, ya ƙi Ubangijinsa. [9]

    9. But he certainly did not cause his beloved Son, Jesus, to suffer.
      Babu shakka bai haddasa azabar da ƙaunataccen Ɗansa Yesu, ya sha ba. [10]

    10. “Become imitators of God, as beloved children.” —EPH.
      “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.”—AFIS. [11]

    11. Yes, the death of a beloved mate can cause a variety of reactions, for widowhood really involves more than simply living without a husband.
      Hakika, mutuwar ƙaunacaccen abokin aure takan jawo damuwa dabam dabam, domin gwauranci ya ƙunshi fiye da zama babu miji kawai. [12]

    12. 18 Each section of this book has concluded with a chapter on how to “become imitators of God, as beloved children.”
      18 Kowanne sashe na wannan littafin ya ƙare da babi ɗaya ko biyu game da yadda za mu zama “masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” [13]

    13. Above all these spirit creatures, he has placed one in charge, his own beloved Son, “the firstborn of all creation.”
      A kan dukan wadannan ruhohi, ya dora shugaba, Dansa wanda yake kauna, “dan fari ne gaban dukan halitta.” [14]

    14. He had just witnessed something that pained him deeply —the destruction of his beloved Jerusalem by the Babylonians.
      Ya ga wani abin da ya sa shi baƙin ciki sosai. Babiloniyawa sun halaka Urushalima, ƙasar da yake so sosai. [15]

    15. (Isaiah 53:3; John 10:17) And he told his disciples that they too were beloved.
      (Ishaya 53:3; Yohanna 10:17) Kuma ya gaya wa almajiransa cewa su ma ƙaunatattu ne. [16]

    16. He married his beloved wife, Penny, in 1977 and raised a family.
      Ya auri wata ’yar’uwa mai suna Penny a shekara 1977. [17]

    17. (Hebrews 10:24, 25) When we gather with fellow believers at Christian meetings, we have a wonderful opportunity to praise and worship our beloved God.
      (Ibraniyawa 10:24, 25) Sa’ad da muka taru da ’yan’uwanmu masu bi a taron Kiristoci, muna samun zarafi na bauta wa Allah kuma mu yabe shi. [18]

    18. Now that my beloved Ted is no longer here and I am not as strong as I used to be, my association is more limited.
      Amma yanzu mijina ya mutu kuma ban da karfi kamar dā. Kari ga haka, ba na iya cuɗanya da mutane kamar dā. [19]

    19. The apostle Peter wrote to Christians: “Beloved ones, do not be puzzled at the burning among you, which is happening to you for a trial, as though a strange thing were befalling you.”
      Manzo Bitrus ya rubuta wa Kiristoci: “Ƙaunatattu, kada ku ga abin mamaki ne tsanani mai-zafin nan da ke wurinku, wanda ke auko muku domin ya auna ku, sai ka ce wani baƙon al’amari ya same ku.” [20]

    20. Consider all that Jehovah has delegated to his beloved Son, Jesus.
      Ka yi la’akari da dukan abin da Jehovah ya ba ƙaunataccen Ɗansa, Yesu. [21]

    21. He comes to Bethany —the hometown of his beloved friends Martha, Mary, and Lazarus— a place located about two miles [3 km] outside of Jerusalem.
      Ya zo Bait’anya—garin abokanansa ƙaunatattu Marta, Maryamu, da Li’azaru—wurin misalin mil ɗaya da rabi ne daga Urushalima. [22]

    22. Maybe it is your deceased mate, your mother, your father, or a beloved grandparent.
      Wataƙila mijinki ko matarka ko iyayenka ko kuma kakanka ya rasu. [23]

    23. He inspired Peter to write: “You, therefore, beloved ones, having this advance knowledge, be on your guard so that you may not be led astray with them by the error of the lawless people and fall from your own steadfastness.
      Ta hanyar ruhu mai tsarki, Bitrus ya ce: “Ku fa, ƙaunatattu, domin kun rigaya kun sani, ku yi hankali kada ya zama a janye ku bisa ga kuskure na masu-mugunta, har ku fāɗi daga cikin tsayawarku. [24]

    24. At the same time, we should endeavor to respect the consciences of our beloved spiritual brothers and sisters.
      Kuma, ya kamata mu yi ƙoƙari mu daraja lamirin ’yan’uwanmu ƙaunatattu na ruhaniya. [25]

    25. At his baptism, for instance, he received loving reassurance from the Father, who declared: “This is my Son, the beloved, whom I have approved.”
      Alal misali, a lokacin baftismarsa, ya samu tabbaci daga Uban, wanda ya sanar: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.” [26]


Retrieved August 07, 2020 10:22 PM