Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:block

Discussion page of block

Glosbe's example sentences of block [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar block:
    1. “Abundant peace belongs to those loving your law, and for them there is no stumbling block.” —PS.
      “Salama mai-yawa tana ga waɗanda suke ƙaunar shari’arka; ba kuwa wani dalilin tuntuɓe garesu.”—ZAB. [2]

    2. Recall that in discussing one’s choice to eat certain foods, Paul cautioned his fellow Christians: “Keep watching that this authority of yours does not somehow become a stumbling block to those who are weak.”
      Ka tuna cewa a tattauna zaɓen mutum ya ci wani irin abinci, Bulus ya yi wa ’yan’uwa Kiristoci gargaɗi: “Amma ku yi hankali kada wannan iko naku ya zama abin tuntuɓe ga raunana.” [3]

    3. Paul counseled us: “Make this your decision, not to put before a brother a stumbling block or a cause for tripping.”
      Bulus ya gargaɗe mu: “Kada kowa ya sa abin tuntuɓe a cikin tafarkin ɗan’uwansa, ko kuwa dalilin fāɗuwa.” [4]

    4. Just as Amaziah tried to silence Amos, so certain priests, prelates, and patriarchs of our day try to block the preaching work of Jehovah’s servants.
      Kamar yadda Amaziya ya yi ƙoƙari ƙwarai domin ya hana Amos, haka ma wasu firistoci, limamai, da ubanni na zamaninmu suke ƙoƙarin su hana aikin wa’azi na bayin Jehovah. [5]

    5. How can we prevent an offense from becoming a stumbling block?
      Mene ne zai taimaka mana don kada laifin da wani ya yi mana ya sa mu tuntuɓe? [6]

    6. The tiny atom —the very building block of all things— is so small that a single drop of water contains one hundred billion billion atoms.
      Atam ɗan mitsitsi—dutsen da aka gina kome da shi—mitsitsi ne sosai da ɗigon ruwa yana ɗauke da atam biliyan biliyan har guda ɗari. [7]

    7. A “stumbling block” refers to an action or circumstance that leads a person to follow an improper course, to stumble or fall morally, or to fall into sin
      Sa mutum “tuntuɓe” yana nufin yin wasu abubuwan da za su sa shi ya yi abin da bai kamata ba ko kuma ya yi zunubi [8]

    8. In fact, the stumbling block may not exist any longer.
      Wataƙila ma, abin da ya sa su tuntuɓe ba ya nan kuma. [9]

    9. For Those Loving Jehovah, “There Is No Stumbling Block”
      Ba “Dalilin Tuntuɓe” ga Masu Ƙaunar Jehobah [10]

    10. 5, 6. (a) How is there “no stumbling block” for a Christian, and what will help him to “get up”?
      5, 6. (a) Me ya sa Kirista ba shi da “dalilin tuntuɓe,” kuma me zai taimaka masa ya “tashi” sa’ad da ya faɗi? [11]

    11. 24:45-47) However, apostates speak their own wisdom, and their words are valueless, a stumbling block to any who might listen.
      24:45-47) Amma, ’yan ridda suna furta na su hikimar, kuma kalamansu duk banza ne, suna hana wasu sauraro. [12]

    12. I have come to block your way, because you should not be going to curse Israel.
      Na zo ne in tare maka hanya, domin kada ka je ka la’anci Isra’ila. [13]

    13. Would you get into a taxi and tell the driver to circle the block repeatedly until his car ran out of fuel?
      Shin za ka shiga tasi kuma ka gaya wa direban ya riƙa zagayawa da kai har sai mansa ya ƙare? [14]

    14. In what sense is there no stumbling block for those loving Jehovah’s law?
      A wace hanya ce masu ƙaunar dokar Jehobah ba su da “dalilin tuntuɓe”? [15]

    15. “As soon as we Jews from Dachau came into the block, the other Jews began to hide everything they had so that they would not have to share with us. . . .
      “Da zarar mu Yahudawa daga Dachau muka shigo cikin sansanin, Yahudawa da suke wurin suka soma ɓoye komi da suke da shi don kada su ba mu. . . . [16]

    16. She was sitting on the porch of a modest country home —a wood and cinder-block structure with a rusted tin roof.
      Tana zaune a kan dakali a gaban wani gida da aka gina da katako da kuma bulo kuma rufin ya riga ya yi tsatsa. [17]

    17. This is Jehovah’s message —and no false god or lifeless idol can block its fulfillment: “Here I am raising up the Chaldeans, the nation bitter and impetuous, which is going to the wide-open places of earth in order to take possession of residences not belonging to it.
      Wannan saƙon Jehovah ne—kuma babu allah na ƙarya ko gunki mara rai da zai iya hana shi cikawa: “Gama, ga shi, ina tada Chaldiyawa, wannan al’umma mai-zafin rai, mai-garaje; waɗanda suna tafiya suna ratsa ratar duniya, domin su gāji mazaunan da ba nasu ba ne. [18]

    18. The psalmist wrote that for those loving Jehovah’s laws “there is no stumbling block.”
      Mai Zabura ya rubuta cewa waɗanda suke ƙaunar dokar Jehovah “ba kuwa wani dalilin tuntuɓe garesu.” [19]

    19. You are a stumbling block to me, because you think, not God’s thoughts, but those of men.” —Matt.
      Kai mai sa tuntuɓe ne a gare ni, gama kana tunani kamar mutum ne, ba kamar Allah ba.” —Mat. [20]

    20. What in my life could become a stumbling block, and how can I keep from stumbling myself or others?
      Mene ne nake yi da zai iya sa wasu tuntuɓe, kuma ta yaya zan guji sa kaina da kuma wasu yin tuntuɓe? [21]

    21. In contrast, for those ‘loving Jehovah’s law,’ no stumbling block exists that can permanently knock them out of the race for life. —Read Psalm 119:165.
      Hakan yana nufin cewa muna iya sake soma yin tseren rai madawwami.—Karanta Zabura 119:165. [22]

    22. However, when they neared Bithynia, Jesus again used the holy spirit to block them.
      Amma, sa’ad da suka yi kusa da birnin Bitiniya, Yesu ya sake amfani da ruhu mai tsarki don ya hana su. [23]

    23. Over time, unresolved problems may become barricades that block communication.
      Da shigewar lokaci, matsalolin da ba a magance ba za su hana sadarwa. [24]

    24. On the other hand, if it was set up as “a sacred pillar” or as “a showpiece,” it became a stumbling block to Jehovah’s people.
      A wani ɓangare kuma, idan aka yi amfani da shi aka gina ‘al’amudi,’ ko kuma ‘siffa,’ sai ya kasance cikas ga mutanen Jehobah. [25]

    25. 6:31, 32) Jesus’ words imply that even so-called normal things like food and clothing can become a burden or a stumbling block if not kept in their proper place.
      6:31, 32) Yesu ya taimaka mana mu fahimci cewa abubuwa kamar abinci da tufafi suna iya zama abin nauwaitawa idan sun fi kasancewa da muhimmanci a gare mu. [26]


Retrieved August 07, 2020 10:23 PM