Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:dealing

Discussion page of dealing

A Christian would want to act in harmony with God’s will when dealing with animals.

Kirista zai so ya bi daidai da nufin Allah lokacin da yake bi da dabbobi.



What will help us to exhibit mildness when dealing with secular authorities?

Mene ne zai taimaka mana mu nuna tawali’u ga masu iko?



• How can we follow Jesus’ example when dealing with the shortcomings of others?

• Ta yaya za mu bi misalin Yesu sa’ad da muke bi da kasawar wasu?



But how many have been taught its meaning, especially the first part of the prayer dealing with God’s name and Kingdom?

Amma mutane nawa ne aka koya musu ma’anarta, musamman sashe na farko na addu’ar da take magana a kan sunan Allah da kuma Mulkinsa?



Rely on God’s Spirit in Dealing With Life’s Changes

Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa



During his ministry, Jesus gave his disciples the key to dealing with various problems in their lives.

A lokacin hidimarsa, Yesu ya ba almajiransa mabuɗin magance matsaloli dabam dabam a rayuwarsu.



The Bible says: “If any one of you is lacking in wisdom [especially in dealing with trials], let him keep asking God, for he gives generously to all and without reproaching, and it will be given him.”

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima [musamman a lokacin da yake fuskantar gwaji], bari ya yi roƙo ga Allah, wanda yake bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.”



4 The Bible writer James says that the tongue is “an unruly injurious thing” that “is full of death-dealing poison.”

4 Yakubu marubucin Littafi Mai Tsarki ya ce harshe abu ne mai “mugunta” kuma ‘cike yake da guba mai matarwa.’



We must be absolutely convinced that God’s way of dealing with our problems is always best.

Amma, ya kamata mu gaskata cewa hanyar da Allah yake bi da matsalolinmu shi ya fi kyau.



But spiritual darkness is death dealing.

Amma duhu na ruhaniya yana da haɗari ƙwarai.



What guidance does Proverbs provide about trusting in God and dealing wisely with others and with oneself?

▪ Wane ja-goranci ne littafin Misalai ya yi tanadinsa game da dogara ga Allah da kuma yin amfani da hikima sa’ad da muke sha’ani da wasu da kuma a yadda muke kula da kanmu?



Christian overseers are urged to set a good example of long-suffering in dealing with their brothers

An aririci Kiristoci masu kula su nuna misali mai kyau na tsawon jimrewa a bi da ’yan’uwansu



Consider how you can benefit from the principles found in the Scriptures when dealing with your parents, when handling money, and when you are alone.

Ku yi la’akari da yadda za ku iya amfana daga ƙa’idodin da ke cikin Nassosi sa’ad da kuke sha’ani da iyayenku, sa’ad da kuke tsai da shawara game da yadda za ku kashe kuɗi, da kuma sa’ad da kuka kaɗaita.



But in reality they were dealing with the Universal Sovereign, Jehovah, who is far, far greater than any human governor.

Amma kuma, suna sha’ani da Mamallakin Dukan Halitta, Jehovah, wanda ya fi dukan wani gwamna.



Jehovah therefore set a perfect example in dealing in an evenhanded way with all ethnic groups.

Jehobah ya kafa misali mai kyau ta wajen ƙin nuna bambanci a yadda yake bi da dukan ƙabilu.



119:105) It is a tremendous help when we are dealing with problems or are making decisions about our choice of friends, entertainment, employment, dress, and so forth.

119:105) Tana taimakawa sosai sa’ad da muke bi da matsaloli ko kuma sa’ad da muke tsai da shawarwari game da zaɓan abokai, nishaɗi, aiki, tufafi, da sauransu.



Why did Jehovah handle matters as he did when dealing with the nation of Israel as a whole?

Me ya sa Jehobah bai gafarta wa al’ummar Isra’ilawa ba?



It is heartwarming to see the humility Jesus showed in dealing with his disciples.

Yana dadada rai mu ga yadda Yesu ya nuna tawali’u a sha’aninsa da almajiransa.



How did Jehovah show mercy in dealing with Solomon, but what should we remember about that?

Ta yaya Jehobah ya bi da Sulemanu da jin ƙai, amma mene ne ya kamata mu tuna game da hakan?



A drug-dealing friend had taken up reading the Bible while in prison, and we had a lengthy discussion about religion, the Church, and Satan’s role in the world.

Wani abokina mai sayar da mugayen ƙwayoyi ya soma karanta Littafi Mai Tsarki sa’ad da yake kurkuku, kuma muka tattauna sosai game da addini, Coci, da matsayin Shaiɗan a duniya.



“I ask questions until I feel that I understand what they are thinking and what they are dealing with in their life,” says Anne, a mother of two boys.

Anne, wata uwa mai yara maza biyu, ta ce: “Nakan yi tambayoyi har sai na ga cewa na fahimci abin da suke nufi da kuma abin da suke fama da shi a rayuwarsu.”



What important precedent did Jesus and the apostles set for us in dealing with pressures and opposition?

Wane muhimmin misali Yesu da manzanni suka bar mana a yadda za mu bi da matsi da kuma hamayya?



10 Jesus set an outstanding example in dealing with those who said or did unpleasant things to him.

10 Yesu ya kafa misali mai kyau wajen yin sha’ani da waɗanda suka faɗa ko yi abubuwa da ba su da kyau a gare shi.



I try to imitate their approach when dealing with my daughters.

Ina koyi da haka sa’ad da na ke yi wa ’ya’yana horo.



By following reasonable legal procedures even when dealing with a relative and fellow believer, Jeremiah set an example for us.

Irmiya ya kafa mana misali ta wurin bin mizanan doka sa’ad da ake sha’ani da dangi da ɗan’uwa mai bi.