Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:divinity

Discussion page of divinity

15 When we dedicate ourselves to God through Christ, we express a determination to use our life in doing the divine will as set forth in the Scriptures.

15 Yayin da muka keɓe kanmu ga Allah ta wurin Kristi, muna furta ƙudurinmu ne mu yi amfani da ranmu a yin nufin Allah yadda yake a cikin Nassosi.



It is vital to keep in mind, however, that when there is no divinely provided principle, rule, or law, it would be improper to impose the judgments of our own conscience on fellow Christians in what are purely personal matters. —Romans 14:1-4; Galatians 6:5.

Amma, yana da muhimmanci mu tuna cewa lokacin da babu ƙa’ida, ja-gora, ko doka daga Allah, ba zai yi kyau ba mu ɗora abin da muka tsai da shi a lamirinmu wa Kiristoci ’yan’uwa a abin da yake sarai al’amura na kanmu ne.—Romawa 14:1-4; Galatiyawa 6:5.



Never should we assume that we are beyond the reach of divine forgiveness.

Kada mu taɓa tunani cewa mun wuce Allah ya gafarta mana.



Their number being seven signifies divinely determined completeness.

Tun da adadinsu bakwai ne yana nufin cika da Allah ya ƙudura.



11 We are also made stronger by divine education at our Christian meetings, assemblies, conventions, and in our theocratic schools.

11 Abubuwan da muke koya a taronmu na Kirista da manyan taron da kuma makarantun da muke zuwa suna ƙarfafa mu sosai.



What was to happen when divine judgment was executed upon Judah, and how should knowledge of that affect us?

Menene zai faru lokacin da aka zartar da hukuncin Allah a kan Yahuza, yaya ya kamata sanin wannan ya taɓa mu?



21 Individuals who do not conduct themselves in harmony with divine requirements are ‘vessels lacking honor.’

21 Mutane da ba sa bi da kansu su jitu da farillan Allah ba ‘kaya ne don ƙasƙantaccen aiki.’



The Bible historian Luke reported: “It was first in Antioch that the disciples were by divine providence called Christians.”

Ɗan tarihi Luka ya rubuta cewa: “A cikin Antakiya fa aka fara ce da masu-bi Krista.”



9 The arrival of Jesus as the Messiah made it necessary to have new divine direction and a further revealing of Jehovah’s purpose.

9 Bayan Yesu ya zo a matsayin Almasihu, Jehobah ya ba da sababbin dokoki kuma ya ba da ƙarin bayani game da nufinsa.



That same force helps true Christians today to grasp divine truths, making “even the deep things of God” more accessible and clearer to our limited minds. —2 Pet.

Ƙari ga haka, ya taimaka wa Kiristoci a yau su fahimci “zurfafan al’amuran Allah,” wato koyarwar Littafi Mai Tsarki masu wuya.—2 Bit.



All who desire divine approval today must exercise similar faith, dedicate themselves to Jehovah God, and undergo Christian baptism in symbol of an unreserved dedication to the Most High God.

Dole ne dukan waɗanda suke son samun amincewar Allah a yau su kasance da irin wannan bangaskiyar, su keɓe kansu ga Jehovah Allah, kuma su yi baftisma ta Kirista alamar keɓe kai babu ragi ga Allah Mafi Girma.



Living for self without regard for divine law might seem attractive to many, but the bad consequences of such a course are inescapable. —Gal.

Yin rayuwa don kanmu ba tare da daraja dokar Allah ba yana iya yin kyau a gaban mutane da yawa, amma ba za a iya guje wa mugun sakamakon irin wannan tafarki ba.—Gal.



(b) How does divine warfare differ from human warfare?

(b) Ta yaya yake-yake na Allah ya bambanta da na mutane?



Aware that ‘the substance of God’s word is truth’ and that we cannot direct our own steps independently, we gladly accept divine direction. —Psalm 119:160; Jeremiah 10:23.

Sanin cewa ‘cibiyar dokar Allah gaskiya ce,’ kuma ba ma iya kiyaye takawarmu da kanmu, ya sa mun yarda da ja-gorar Allah.—Zabura 119:160; Irmiya 10:23.



What would happen if the people of Israel did not heed divine warnings?

Menene zai faru idan mutanen Isra’ila suka ƙi su bi gargaɗin Allah?



Though all of them hope for divine healing under God’s Kingdom, they are not waiting until God relieves them of their problems before trying to do something in his service.

Ko da yake dukansu suna sa rai za su warke a ƙarƙashin Mulkin Allah, ba sa jira har sai lokacin da Allah ya sauƙaƙa masu wahalarsu kafin su yi wani abu a hidimarsa.



14-16. (a) What convinced a Muslim, a Hindu, and an agnostic of the divine origin of the Bible?

14-16. (a) Mene ne ya sa wasu mutane uku suka gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne?



3 Of course, the number of those associated with Jehovah’s Witnesses is not a criterion for determining if they enjoy divine favor; nor do statistics impress God.

3 Babu shakka, adadi mai yawa na mutane da suke tarayya da Shaidun Jehovah ba shi ne magwaji ba na sanin ko za su more alherin Allah; ba kuwa yawan adadi ne yake burge Allah ba.



Understanding this divine attribute, though, gives us many reasons for drawing closer to Jehovah.

Amma fahimtar wannan hali na Allah tana ba mu dalilai na kusantar Jehovah.



(Acts 14:11-13) When he was in Philippi, Paul had an encounter with a servant girl who practiced divination.

M. 14:11-13) Sa’ad da yake Filibi, Bulus ya sadu da wata yarinya mai duba. (A.



26:52) Jehovah will use his Son to carry out divine justice in the future.

26:52) Jehobah zai yi amfani da Ɗansa wajen zartar da hukuncinsa a nan gaba.



For example, according to Professor Gamble, when Augustine on one occasion heard the voice of a child in a neighboring house saying: “Take and read, take and read,” Augustine took that to be a divine command to open the Bible and read the first text that he saw.

Alal misali, Shehun malamin ya ce, akwai wani lokaci da Augustine ya ji wani yaron maƙwabcinsa yana cewa: “Ɗauka ka karanta, ɗauka ka karanta.” Sai Augustine ya yi zato cewa Allah ne yake gaya masa ya buɗe kowace aya ta Littafi Mai Tsarki ya karanta.



Do you clearly discern the evidence of divine guidance?

Shin ka gane tabbacin cewa Allah yana ja-gora kuwa?



Why should you continue to accept divine discipline?

Me ya sa ya kamata ka ci gaba da yin na’am da horon Allah?



17 In view of the divine prophecy of Genesis 3:15, Satan may have been desperate as he looked for an opportunity to attack the vulnerable Israelites.

17 Babu shakka, annabcin da ke Farawa 3:15 ya sa Shaiɗan ya so ya kai hari ga Isra’ilawa don a ganinsa ba su da kāriya.