Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:forgive

Discussion page of forgive

Glosbe's example sentences of forgive [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar forgive:
    1. According to one scholar, the Greek word rendered “freely forgive” “is not the common word for remission or forgiveness . . . but one of richer content emphasizing the gracious nature of the pardon.”
      Wani manazarci ya ce kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a nan tana nufin gafartawa daga zuci kuma a yalwace. [2]

    2. What do we learn from this miracle?— We learn that Jesus has the power to forgive sins and to make sick people well.
      Menene muka koya daga wannan mu’ujiza?— Mun koyi cewa Jehovah yana da iko ya gafarta zunubi kuma ya warkar da mutane masu rashin lafiya. [3]

    3. When we freely forgive others, we preserve unity and peace, thereby safeguarding relationships.
      Idan muka gafarta wa mutane, za mu kasance da haɗin kai da salama kuma hakan zai ƙarfafa abotarmu da mutane. [4]

    4. But Jesus taught that we should forgive those who do wrong to us.
      Amma Yesu ya koyar da cewa ya kamata mu yafe wa waɗanda suka yi mana laifi. [5]

    5. 16 Jehovah promised regarding those in the new covenant: “I shall forgive their error, and their sin I shall remember no more.”
      16 Jehovah ya yi alkawari game da waɗanda suke cikin sabon alkawari: “Zan gafarta muguntarsu, ba ni kuwa ƙara tuna da zunubinsu ba.” [6]

    6. With full faith in Jehovah’s willingness to extend mercy to repentant ones, David said: “You, O Jehovah, are . . . ready to forgive.” —Psalm 86:5.
      Da cikakkiyar bangaskiya cewa Jehovah yana shirye ya yi jinƙai ga wanda ya tuba, Dauda ya ce: “Kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa kuwa.”—Zabura 86:5. [7]

    7. The king’s mercy should have motivated his slave to forgive a fellow slave.
      Ya kamata wannan bawan ya ji tausayin ɗayan bawan kamar yadda sarki ya ji tausayinsa. [8]

    8. 17 Jehovah will forgive and forget your past errors if you are truly repentant and accept his mercy.
      17 Jehobah zai gafarta maka dukan kurakuranka idan ka tuba da gaske kuma ka gaskata cewa zai yi maka jin ƙai. [9]

    9. Mr 2:6-12 —Jesus proved that he has authority to forgive sins by healing the paralytic (“Which is easier” study note on Mr 2:9, nwtsty)
      Mk 2: 6-12 —Yesu ya nuna cewa yana da ikon gafarta zunubai sa’ad da ya warkar da wani mai ciwon inna (nwtsty na nazarin littafin Mk 2:9) [10]

    10. (b) Choosing to forgive when there is a sound basis for doing so brings what blessings?
      (b) Gafartawa sa’ad da da dalilin yin haka tana kawo wace albarka? [11]

    11. But this is the lesson we need to remember: God forgives us only if we forgive people who do wrong to us.
      Amma wannan shi ne darasi da muke so mu riƙa tunawa: Allah zai yafe mana ne idan mun yafe wa mutane da suka yi mana laifi. [12]

    12. (Ro 14:13-15) Finally, if someone sins against us, we can be quick to forgive.
      (Ro 14: 13-15) Na uku shi ne, mu riƙa saurin gafarta wa ’yan’uwanmu idan suka yi mana laifi. [13]

    13. 15 Forgive freely.
      15 Ku riƙa gafarta wa juna. [14]

    14. When we make mistakes, we want God to forgive us.
      Sa’ad da muka yi kuskure, muna so Allah ya gafarta mana. [15]

    15. What will you do if someone asks you to forgive him?
      Me za ka yi idan wani ya roƙe ka ka yafe masa? [16]

    16. In turn, the one who was offended should readily forgive the repentant wrongdoer.
      Hakanan kuma, wanda aka yi wa laifi ya kamata ya gafarci mai laifin. [17]

    17. Are we “ready to forgive,” or are we sometimes inclined to hold a grudge?
      Shin muna “hanzarin gafartawa kuwa” ko kuma a wasu lokatai muna riƙe shi a zuciya? [18]

    18. If we confess the specific sin to Jehovah, he will mercifully forgive us through the office of our High Priest, Jesus Christ.
      Babban Firist, Yesu Kristi, zai taimaka mana don Jehobah ya gafarta mana idan muka tuba. [19]

    19. If we were the person who is asking to be forgiven, we would want the other person to forgive us, wouldn’t we?— So we should do the same for him.
      Idan mu ne muke roƙo a yafe mana, za mu so mutumin ya yafe mana, ko ba haka ba?— Saboda haka, ya kamata mu ma mu yafe wa wasu. [20]

    20. Jesus then made this point: Jehovah will not forgive the one who does not forgive his brother.
      Yesu ya bayyana wannan darasin: Jehobah ba zai gafarta wa wanda bai gafarta wa ɗan’uwansa ba. [21]

    21. (1 Corinthians 7:28) Still, couples who observe the Bible’s moral standards try to forgive and to work out their difficulties together.
      (1 Korantiyawa 7:28) Duk da haka, ma’aurata da suka bi mizanan Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a suna ƙoƙari su gafarta wa juna kuma su warware matsalolinsu tare. [22]

    22. We found that the formula for happiness, both in marriage and in the congregation, is to respect headship, forgive freely, maintain humility, and display the fruitage of the spirit.
      Mun fahimci cewa abin da ke kawo farin ciki a aure da kuma a ikilisiya shi ne daraja waɗanda ke ja-goranci da gafartawa da nuna tawali’u da kuma kasance da halayen da ruhu mai tsarki ke haifarwa. [23]

    23. But while Jehovah is willing to forgive repentant sinners, he expects us to put up a strong fight against our sinful tendencies. w16.07 3:16, 17
      Ko da yake Jehobah yana gafarta wa waɗanda suka tuba da gaske, amma yana so mu riƙa aiki tuƙuru don mu guji yin zunubi. w16.07 3:16, 17 [24]

    24. What can help us to forgive others, and why must we do so?
      Menene zai taimaka mana mu gafarta wa wasu, kuma me ya sa za mu yi hakan? [25]

    25. It is comforting to know that Jehovah is willing to forgive our sins if we are truly repentant, but it is sobering to realize that sins often bring dire consequences.
      Abin farin ciki ne mu sani cewa Jehovah a shirye yake ya gafarta mana zunubanmu idan muka tuba da gaske, amma abin baƙin ciki ne mu ga mummunar sakamakon da zunubin ya jawo. [26]


Retrieved October 13, 2020, 11:16 pm via glosbe (pid: 11172)