Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:inheritance

Discussion page of inheritance

The apostle Peter told fellow believers that they would receive “an incorruptible and undefiled and unfading inheritance” that is “reserved in the heavens” for them.

Manzo Bitrus ya gaya wa ’yan’uwa masu bi game da wannan sarautar “gādo mara-ruɓewa, mara-ƙazantuwa, wanda ba shi yanƙwanewa” wanda aka “ajiyayye a sama dominku.”



How can we safeguard our inheritance?

Yaya za mu kiyaye gādonmu?



Abraham’s offspring received the promise of a precious inheritance

’Ya’yan Ibrahim sun samu alkawarin gadō mai tamani



Some Who Despised the Inheritance

Wasu da Suka Yi Banza da Gadōn



Jehovah said that he was to be their share in the sense that rather than receiving a land inheritance, they were entrusted with a priceless privilege of service.

Jehobah ya ce zai zama rabonsu a azanci na cewa maimakon su karɓi gadon ƙasa, an ba su gatar yin hidima mai tamani.



Our inheritance of sin is also the underlying cause of sickness.

Zunubi da muka gāda ne ainihi ya sa muke rashin lafiya.



How did Abraham, Isaac, and Jacob show appreciation for their inheritance?

Ta yaya Ibrahim, Ishaku, da Yakubu suka nuna godiya ga gadōnsu?



After the kings of the land of Canaan are defeated under the leadership of Joshua, the individual tribes of Israel go to their inheritance and take possession of the land.

Bayan sun ci sarakunan ƙasashen Ka’anan da yaƙi a ƙarƙashin shugabancin Joshuwa, kowace ƙabilar Isra’ila ta tafi inda gadōnta yake kuma ta gaji ƙasar.



Jacob said: ‘I will, but first promise me that I can have your inheritance.’

Sai Yakubu ya ce: ‘Zan ba ka idan ka sayar mini da gādonka na haihuwa.’



Moses said: “You continue to live, because [Jehovah] loved your forefathers so that he chose their seed after them and brought you out of Egypt in his sight with his great power, to drive away nations greater and mightier than you from before you, so as to bring you in, to give you their land as an inheritance as at this day.” —Deuteronomy 4:37, 38.

Musa ya ce: “Domin kuma [Jehovah] ya ƙaunaci ubanninka, domin wannan ya zaɓi zuriyassu a bayansu, kuma da zatinsa, da ikonsa mai-girma ya fishe ka daga ƙasar Masar; domin shi kori al’ummai daga gabanka, waɗanda suka fi ka girma da ƙarfi, shi shigo da kai, shi ba ka ƙasarsu abin gado, kamar da ya ke yau.”—Kubawar Shari’a 4:37, 38.



(2 Samuel 7:4-17; Matthew 1:6, 16) According to this psalm, God tells his Son: “Ask of me, that I may give nations as your inheritance and the ends of the earth as your own possession.” —Psalm 2:8.

(2 Sama’ila 7:4-17; Matiyu 1:6, 16) Bisa wannan zabura, Allah ya gaya wa Ɗansa: “Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai, dukan duniya kuma za ta zama taka.”—Zabura 2:8.



No wonder we cherish our inheritance!

Muna da dalilai masu kyau na nuna godiya sosai don gādonmu!



Take comfort, then, in the psalmist’s words: “Jehovah will not forsake his people, nor will he leave his own inheritance.” —Psalm 94:14.

Ka ƙarfafa daga kalmomin mai Zabura: “Ubangiji ba za ya yarda mutanensa ba: ba kuwa za ya yi ɓari da gadōnsa ba.”—Zabura 94:14.



Usually these were blood relatives, but some engagements and marriages were prohibited because of inheritance rights.

Waɗannan dangin na kurkusa ne, amma ana ƙin wasu riƙo da aure saboda damar samun gadō.



But those walking with God meet his standards for clean worship and are aware that “no fornicator . . . has any inheritance in the kingdom of the Christ and of God.” —Ephesians 5:5; James 1:27.

Amma waɗanda suke bin Allah kuma suke cika mizanansa don bauta mai tsarki sun san cewa “ba wani fasiki . . . [da] ke da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.”—Afisawa 5:5; Yakubu 1:27.



How to Share in the Promised Inheritance

Yadda Za a Sami Gadō da Aka Yi Alkawarinsa



11 On a later occasion while Jesus was teaching his followers how to cope with opposition, a man interrupted, saying: “Teacher, tell my brother to divide the inheritance with me.”

11 Daga baya, sa’ad da yake koyar da mabiyansa yadda za su bi da hamayya, wani mutum ya katse masa magana kuma ya ce: “Malam, ka ce ma ɗan’uwana shi raba gadō da ni.”



Ask of me, that I may give nations as your inheritance and the ends of the earth as your own possession.”

Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al’ummai, dukan duniya kuma za ta zama taka.”



2:6) They occupy this spiritual position because they have been ‘sealed with the promised holy spirit, which is a token in advance of their inheritance,’ that is, ‘the hope reserved for them in the heavens.’ —Eph.

2:6) Sun sami wannan matsayin domin an yi musu ‘hatimi da ruhu mai tsarki na alkawari wanda shi ne tabbacin gādonsu,’ wato “begen da ke cikin sama” da aka ajiye dominsu.—Afis.



4:6 —In what way could a repurchaser “ruin” his inheritance by doing the repurchasing?

4:6—A wace hanya ce mai fansa yake ‘ɓata’ gadonsa domin ya yi fansa?



God-fearing parents recognize that their children are “an inheritance from Jehovah.”

Iyaye masu jin tsoron Allah sun fahimci cewa yaransu “gādo ne daga wurin Ubangiji.”



“By faith Abraham . . . obeyed by going out to a place he was to receive as an inheritance; he went out, although not knowing where he was going.” —Hebrews 11:8

“Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim ya yi biyayya ya kama hanya zuwa wata ƙasa wadda aka yi masa alkawari cewa zai karɓi gādonta. Shi kuwa ya kama hanya ko da bai san inda za shi ba.” —Ibraniyawa 11: 8, Juyi Mai Fitar da Ma’ana



The man to whom she spoke responded that if Jesus made this promise, the earth must be an inheritance worthy of the name and not a devastated or uninhabitable heap.

Mutumin da take wa magana ya amsa cewa idan Yesu ya yi wannan alkawari, yana nufin duniya ta cancanci a gāje ta, kuma ba wurin da aka ragargaje ba ne ko kuma kango da ba a zama a ciki.



(1 Kings 19:19-21; 2 Kings 2:12) Hence, just as the literal firstborn received two parts of his father’s inheritance, Elisha asked for and received two parts of spiritual inheritance from Elijah.

(1 Sarakuna 19:19-21; 2 Sarakuna 2:12) Saboda haka, kamar yadda ɗan fari na zahiri yake samun kashi biyu na gadon ubansa, Elisha ya roƙi kashi biyu na gado ta ruhaniya daga Iliya.



(Psalm 37:16; 73:3, 12) They are like the unreasonable rich man Jesus mentioned in an illustration when asked to arbitrate in a matter involving an inheritance.

(Zabura 37:16; 73:3, 12) Sun yi kama da mutum mai arziki marar azanci da Yesu ya ambata a wani kwatanci sa’ad da aka gaya masa ya tsai da shawara a kan batun samun gadō.