It would be wise to meditate on how one false step could lead to another and then to serious wrongdoing.
Abin hikima ce a yi bimbini a kan yadda zunubi ɗaya zai iya kai ga yin zunubi mai tsanani.
18 Our love for Jehovah moves us to meditate on his creative works and other marvelous deeds.
18 Ƙaunarmu ga Jehobah za ta sa mu yi bimbini a kan abubuwan da ya halitta da kuma ayyukansa.
If you ever doubt that Jehovah cares for you, meditate on such Bible passages as Psalm 34:17-19; 55:22; and 145:18, 19.
Idan har kana shakka cewa Jehobah yana kula da kai, ka yi tunani a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki kamar Zabura 34:17-19; 55:22; da kuma 145:18, 19.
(John 17:3) Meditate, or think deeply, on what you learn from God’s Word, asking yourself: ‘What does this teach me about Jehovah God?
(Yohanna 17:3) Ka yi bimbini ko kuma tunani sosai, a kan abin da ka koya daga Kalmar Allah ka tambayi kanka: ‘Menene wannan yake koya mini game da Jehobah Allah?
As we do so, meditate on how you personally can deepen your love for these spiritual treasures.
Sa’ad da muke binciken, zai dace mu yi tunani a kan darussan da za mu koya da za su taimaka mana mu ci gaba da ɗaukan waɗannan abubuwan da muhimmanci.
And you allow Jehovah to talk to you, as it were, when you regularly read his written Word and meditate on it.
Idan kana karanta Kalmar Allah kullum kuma kana yin bimbini a kai, tamkar kana ba wa Jehobah damar tattaunawa da kai.
19:14) How important it is that we take time to meditate on what we read, so that Bible truths sink deep down into the heart!
19:14) Yana da muhimmanci mu ɗauki lokaci mu yi bimbini a kan abin da muka karanta, domin gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta kahu sosai a cikin zuciyarmu!
Instead, we should meditate on reassuring words about Jehovah’s enduring love for us.
A maimakon haka, zai dace mu yi bimbini a kan furucin Jehobah game da irin ƙaunar da yake yi mana.
Indeed, we receive the very best instruction from God, such as when we read and meditate on real-life Bible accounts.
Babu shakka, muna amfana sosai idan muka karanta labaran mutanen da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma muka yi bimbini a kan su.
14 To enhance our appreciation for the honor of bearing God’s name, it is good for us to meditate on its meaning.
14 Domin mu fahimci dalilin da ya sa gata ne sosai a kira mu da sunan Jehobah, muna bukatar mu san ma’anar sunan.
Then pause at times to meditate on what you read.
A wasu lokatai, ka dakata ka yi bimbini a kan abin da ka karanta.
This gives me something fresh to meditate on during the day.” —Marie, baptized 1935.
Wannan yana ba ni wani sabon abin da zan yi bimbini a kai a ranar.”—Marie, ta yi baftisma a shekara ta 1935.
Why do we need to meditate on admonition from God?
Me ya sa muke bukata mu yi bimbini a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?
9 During this Memorial season, it is good to meditate on how we are using our life.
9 A wannan lokacin Tuna da Mutuwar Yesu, yana da kyau mu yi bimbini a kan yadda muke amfani da rayuwarmu.
Their delight is in the law of Jehovah, and they meditate on it day and night.
Suna karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yi bimbini a kan sa dare da rana.
(Galatians 3:24, 25) Rather than changing his mind, God used the Sabbath as a temporary arrangement to teach people that they should regularly take time to meditate on spiritual matters.
(Galatiyawa 3:24, 25) Maimakon ya canza shawara, Allah ya yi amfani da Assabaci a matsayin shiri na ɗan lokaci don ya koya wa mutane cewa su keɓe lokaci don yin bimbini a kan abubuwa na ruhaniya.
• Why should we meditate on Jehovah’s thoughts?
• Me ya sa ya kamata mu yi bimbini a kan batutuwan Jehobah?
As we consider these points, it will be helpful to meditate on our relationship with God and discern how we can honor him as our Father.
Yayin da muke tattauna waɗannan batutuwan, zai dace mu yi tunani sosai game da dangantakarmu da Allah da kuma yadda za mu girmama shi a matsayin Ubanmu.
Our appreciation for Bible truth will grow when we meditate on ways we benefit from applying it in our lives.
Idan muka yi bimbini a kan yadda yin amfani da Kalmar Allah yake taimaka mana, za mu riƙa ƙaunar Kalmar Allah sosai.
(Psalm 51:10) We can meditate on the benefits of avoiding things that are morally wrong or physically debilitating.
(Zabura 51:10) Za mu iya bimbini a kan amfanin guje wa abubuwa da ba su da kyau ko kuma na raunana jiki.
If we meditate ahead of time, we can make our prayers specific and meaningful, thus avoiding the practice of repeating phrases that feel familiar and spring readily to mind.
Idan mun yi bimbini tun kafin lokaci, za mu iya sa addu’armu ta kasance mai ma’ana kuma takamammiya, ta haka za mu guji maimaita furci da muke tunawa da sauri.
2 Meditate on What?
2 Yin Bimbini a Kan Me?
Persecuted for their faith, they prayed: “Sovereign Lord [Jehovah], you are the One who made the heaven and the earth and the sea and all the things in them, and who through holy spirit said by the mouth of our forefather David, your servant, ‘Why did nations become tumultuous and peoples meditate upon empty things?
Da yake ana tsananta musu don bangaskiyarsu, sun yi addu’a: “Ya Mamallaki [Jehovah], Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da ke cikinsu, wanda ta Ruhu Mai Tsarki, ta bakin kakanmu Dawuda baranka, ka ce, ‘Don me al’ummai suka husata? Kabilai kuma suka yi makidar al’amuran wofi?
(See also the box “How to Meditate.”)
(Ka duba akwatin nan “Yadda Za Mu Riƙa Yin Bimbini.”)
Taking time to meditate appreciatively on ‘Jehovah’s dealings’ can instill in us the desire to cultivate this godly quality. —Read Psalm 77:12.
Ɗaukan lokaci don mu yi bimbini cikin godiya a kan ‘aikin Jehobah’ zai sa mu yi sha’awar koyan wannan hali da Allah yake nunawa.—Karanta Zabura 77:12.