Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:perform

Discussion page of perform

(John 11:41, 42; 12:9-11, 17-19) In a touching way, it also reveals the willingness and desire of Jehovah and his Son to perform the resurrection.

(Yohanna 11:41, 42; 12:9-11, 17-19) A hanya mai-taɓuwa fa, ya bayana niyya da kuma sha’awar Jehovah da Ɗansa don tafiyadda tashin matattu.



In fact, the territory assigned to Amos may have been similar to that in which some of us perform our ministry today.

Babu shakka, yankin da aka ba Amos yana kama da waɗanda yawancinmu muke wa’azi ciki a yau.



Many will say to me in that day [when God executes judgment], ‘Lord, Lord, did we not prophesy in your name, and expel demons in your name, and perform many powerful works in your name?’”

A cikin wannan rana [sa’ad da Allah zai yi hukunci] mutane dayawa za su ce mani, Ubangiji, Ubangiji, ba mu yi annabci da sunanka ba, da sunanka kuma muka fitarda aljanu, da sunanka kuma muka yi ayyuka dayawa masu-iko?”



(b) What resurrections did Jesus perform?

(b) Waɗanne mutane ne Yesu ya tayar daga matattu?



Thus, we have no basis for expecting God to perform miraculous healings for us or our loved ones.

Saboda haka, bai kamata mu riƙa sa rai cewa Allah zai warkar da mu ko ƙaunatattunmu da suke rashin lafiya ta hanyar mu’ujiza ba.



Yet, if we are modest, we will not always expect others to perform as we would like them to.

Duk da haka, idan muna da filako, ba za mu zaci cewa wasu kullum su yi yadda muke so ba.



What miracle did Elisha perform in Shunem?

Wace mu’ujiza ce Elisha ya yi a Shunem?



The desire of those fearing him he will perform, and their cry for help he will hear, and he will save them.

Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; Za ya kuma ji kukarsu, ya cece su.



Many will say to me in that day, ‘Lord, Lord, did we not prophesy in your name, and expel demons in your name, and perform many powerful works in your name?’

A cikin wannan rana mutane dayawa za su ce mini, Ubangiji, Ubangiji, ba mu yi annabci da sunanka ba, da sunanka kuma muka fitarda aljanu, da sunanka kuma muka yi ayyuka dayawa masu-iko?



• What grand public service did Jesus perform?

• Wace hidima ce mai girma ga jama’a Yesu ya yi?



Do they see you perform lowly tasks?

Suna ganin kuna ƙananan ayyuka?



In Britain, upwards of 1,500, including more than 300 women, were imprisoned for declining to perform war duties.

A ƙasar Britaniya, maza 1,500 tare da mata fiye da 300 ne aka jefa kurkuku don sun ƙi yin aikin soja.



Why did Jesus perform all those miracles?

Me ya sa Yesu ya yi dukan waɗannan mu’ujizan?



3 A builder is chosen who will follow the blueprints and perform the restoration.

3 An zaɓi maginin da zai bi zanen kuma ya gyara ginin.



The March 1, 1935, issue of The Watchtower raised another moral issue: “It has likewise been noticed that some take part in the field service and perform other duties in the organization while under the influence of [alcohol].

Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris 1935, ta tattauna wani batu dabam da ya shafi ɗabi’ar mutanen Allah. Ta ce: “An lura cewa wasu suna zuwa wa’azi ko kuma yin wasu hidimomi a cikin ikilisiya bayan sun sha [giya].



16:13) All those men relied on God’s spirit to help them, and that spirit empowered them to perform feats that they could not have done in their own strength. —Josh.

16:13) Dukan waɗannan mutane sun dogara ga taimakon ruhun Allah, kuma wannan ruhun ya taimaka musu su yi ayyukan da ba za su iya yi da ƙarfinsu ba. —Josh.



Jehovah used Elisha to do really wonderful things —to perform miracles!

Jehobah ya sa Elisha ya yi abubuwa masu ban al’ajabi.



What miracle did Jesus perform near the city of Nain, and how may this incident affect us?

Wace mu’ujiza ce Yesu ya yi a kusa da birnin Nayin, kuma yaya wannan aukuwar za ta shafe mu?



He may thus have seen Jesus perform his first miracle, that of turning water into wine at the wedding feast in Cana.

Mai yiwuwa, ya ga sa’ad da Yesu ya yi mu’ujizarsa ta farko, wato juya ruwa zuwa inabi a bikin auren da aka yi a Kana.



18 True, Jehovah does not perform such miracles in behalf of his people today, but he does bless their acts of faith.

18 Gaskiya ne cewa Jehobah ba ya yin mu’ujizai a madadin mutanensa a yau, amma sa’ad da muka bi umurninsa, muna samun albarka.



Though he did perform those miracles, the focus of Jesus’ ministry was not on gathering converts by means of emotional sessions of miracle working.

Ko da yake ya yi mu’ujizai, ainihin wa’azin da Yesu yake yi bai mai da hankali a kan tara mabiya ta hanyar aikin mu’ujiza ba.



Months passed while David lived a double life, no doubt continuing to perform his official functions.

Dauda ya ci gaba da yin hidimarsa a matsayin sarki na watanni masu yawa kuma bai gaya wa kowa game da zunubinsa ba.



Jehovah has already used Elijah to perform a prolonged miracle to reward the faith of this humble widow.

Jehobah ya yi amfani da Iliya ya yi mu’ujiza da za ta daɗe don ya albarkaci bangaskiyar wannan gwauruwa mai tawali’u.



We cannot perform miracles, but we can show love, humility, and compassion —qualities that help to draw people to the truth.

Ba za mu iya yin mu’ujizai ba, amma za mu iya nuna ƙauna, tawali’u, da kuma juyayi, wato halayen da za su taimaka wajen jawo mutane zuwa gaskiya.



Hence, Adam was not like a machine that can perform only what it is designed or programmed to do.

Saboda haka, Adamu ba kamar inji ba ne da yake yin abin da aka ƙera shi ya yi kawai.