Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:sincere

Discussion page of sincere

(Mark 12:28-31) Paul exhorts us to make sure that the love we show as Christians is sincere.

(Markus 12:28-31) Bulus ya aririce mu Kiristoci mu tabbata cewa ƙaunar da muke nunawa ta gaskiya ce.



Studying was thus of no profit because they were not sincere, teachable. —Deuteronomy 18:15; Luke 11:52; John 7:47, 48.

Saboda haka, nazari bai kasance da amfani ba domin ba su da gaskiya, ba sa son su koya.—Kubawar Shari’a 18:15; Luka 11:52; Yohanna 7:47, 48.



13 In the late 1800’s, a number of sincere individuals were searching for an understanding of “the pattern of healthful words.”

13 A ƙarshen shekarun alif da ɗari takwas, sahihan mutane da yawa suna neman su fahimci “kwatancin sahihiyan kalmomi.”



What a joy it is to help sincere people understand and appreciate the hope offered by the Scriptures!

Abin farin ciki ne mu taimaka wa mutanen da suke son gaskiya su fahimci kuma su so begen da ke cikin Nassosi!



No matter how heartwarming such experiences may be, however, it is clear that such sincere efforts will not eradicate poverty.

Ko da irin waɗannan labarai suna daɗaɗa rai, a bayane yake cewa irin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce ba za su kawar da talauci ba.



Speaking to those whose worship was not sincere, Jesus quoted Jehovah as saying: “This people honors me with their lips, yet their heart is far removed from me.”

Sa’ad da yake yin magana ga waɗanda bautarsu ba ta fito daga zuciyarsu ba, Yesu ya yi kaulin Jehobah yana cewa: “Wannan al’umma tana girmamana da leɓunansu; Amma zuciyarsu tana nesa da ni.”



During the 1800’s, though, a few sincere students of the Bible scrutinized that teaching and saw that it had no support in God’s Word.

A tsakanin shekara ta 1800 da 1900, wasu masu nazarin Littafi Mai Tsarki sun bincika wannan koyarwar kuma sun gano cewa ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ne.



A sincere word of encouragement can help the elderly find “cause for exultation” in their sacred service, thus avoiding frustrating comparisons with what other Christians are able to do or with their own past accomplishments. —Galatians 6:4.

Sahihan kalamai masu ƙarfafawa suna iya taimaka wa tsofaffi su ‘sami taƙama’ a tsarkakkar hidima, da haka, wannan zai kau musu da sanyin gwiwar gwada abin da wasu Kiristoci suke yi da kuma abubuwan da suka cim ma a dā.—Galatiyawa 6:4.



1 Peter 1:22 How do these words show that our love for fellow believers must be sincere, genuine, and warm?

1 Bitrus 1:22 Ta yaya waɗannan kalmomin suka nuna cewa ƙaunarmu ga ’yan’uwa masu bi dole ta kasance ta gaske, kuma mai daɗaɗawa?



How does this fit in with the adoration that many sincere believers bestow on Mary?

Ta yaya wannan ya jitu da bauta da yawancin sahihan masu bi suke yi wa Maryamu?



• Show a sincere personal interest in people.

• Ka nuna ka damu sosai da mutane.



What a privilege it was to meet these sincere people, most of whom cannot read or write or speak Spanish but who want to learn about the true God and worship him!

Gata ne mai girma mu sadu da waɗannan mutane masu son gaskiya, waɗanda ba su da littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki a yaren da za su iya karantawa amma suna so su koyi gaskiya game da Allah kuma su bauta masa!



SUMMARY: Speak in a natural, sincere way that conveys how you feel about the topic and your listeners.

ABIN DA ZA KA YI: Ka yi magana a sake yadda zai nuna cewa kana son batun da kake tattaunawa kuma ka damu da masu sauraronka.



Yes, when we study God’s Word with a sincere heart and an open mind, we learn more than enough about Jehovah to be convinced that he always does what is just and right.

Hakika, sa’ad da muka yi nazarin Kalmar Allah domin muna son mu san shi, muna ƙara koyan abubuwa da yawa game da Jehobah da zai sa mu tabbata cewa koyaushe yana aikata abin da ke daidai.



We have a firm basis to be confident that the “Hearer of prayer” answers sincere prayers offered by millions of humans.

Muna da dalilai masu ƙarfi na tabbata cewa mai “jin addu’a” ne, yana amsa addu’o’i da miliyoyin mutane suka yi da zuciya ɗaya.



(Revelation 7:9; John 10:16) These were, not anointed members of “the Israel of God,” but sincere men and women with an earthly hope, who loved Jehovah and who wanted to serve him just as the anointed did.

(Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Waɗannan ba shafaffu ba ne da suke cikin “Isra’ila na Allah,” amma sahihan maza da mata da suke da begen zama a duniya da suke ƙaunar Jehovah kuma suna son su bauta masa yadda shafaffu suka yi.



A word of sincere appreciation goes a long way toward helping your wife to feel valued. —Proverbs 31:28.

Furta kalmomin godiya na gaske yana taimakawa sosai wajen sa matarka ta ji tana da daraja.—Misalai 31:28.



Of course, the Bible lays down clear principles that all sincere Christians observe.

Hakika, Littafi Mai Tsarki ya tsara ƙa’idodi da dukan Kiristoci na gaskiya suke bi.



(Colossians 3:22) Who would not appreciate having such a sincere person working for him?

(Kolossiyawa 3:22) Waye ba zai yi farin ciki ba ya sami irin wannan mutum yana masa aiki?



If so, you are like the sincere ones Jesus met and helped.

Idan haka ne, kana kamar waɗanda suke son gaskiya da Yesu ya sadu da su kuma ya taimake su.



They may be sincere about strong feelings that well up in their hearts.

Za su iya kasancewa da motsin rai na gaske da ya cika zuciyarsu.



Of course, Jesus’ disciples would have sincere questions or disagreements among themselves at times.

Hakika, almajiran Yesu sukan yi tambayoyi ko kuma jayayya tsakaninsu wasu lokatai.



But he is still trying to disrupt the worship that sincere Christians render to God.

Amma yana ƙoƙarin ya hana bautar da Kiristocin gaske suke yi wa Allah.



Your sincere, enthusiastic recounting of what you gained or the aspects you found interesting will likely make such more impressive to others.

Idan ka lissafa abin da ka amfana ko kuma sashen da yake da amfani ƙwarai a gare ka, zai iya zama da taimako ga wasu.



In this way, representatives of the slave faithfully distributed rich spiritual food to sincere Christians.

Ta haka, wakilan bawan suka rarraba abinci na ruhaniya mai kyau ga sahihan Kiristoci.