Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:submit

Discussion page of submit

However, this psalm also indicates that there is a period of time when earth’s rulers, along with their subjects, are given an opportunity to submit to Christ’s rule.

Amma, wannan zaburar ta nuna cewa an ba masu mulka duniya da kuma talakawansu lokaci mai tsawo don su miƙa wuyansu ga sarautar Kristi.



Moreover, we should “put [our] mouth in the very dust,” that is, humbly submit to trials, recognizing that what God allows to happen is permitted for good reason.

Bugu da ƙari, ya kamata mu “sa bakin[mu] cikin ƙura” wato, mu jimre wa gwaji, mu fahimci cewa da dalili mai kyau ne Allah yake ƙyale abu ya faru.



(Psalm 62:8; Proverbs 3:5, 6) Those who truly honor him recognize that as the Creator of heaven and earth, he is the Universal Sovereign, and they lovingly submit to him as the Sovereign of their lives.

(Zabura 62:8; Karin Magana 3:5, 6) Waɗanda suke girmama shi da gaske sun fahimci shi Mahaliccin sama ne da duniya, Mai Ikon Mallakar Dukan Sararin Halitta, kuma suna yi masa biyayya domin shi ne wanda yake da Iko a kan rayukanmu.



Korah was not willing to submit humbly to direction

Kora bai da tawali’u kuma ya ƙi bin ja-gora



Loyally Submit to Godly Authority

Ka Miƙa Kai Da Aminci Ga Ikon Allah



Then let us continue to pray earnestly to our loving God, Jehovah, and humbly submit to the direction of his holy spirit and the counsel of his Word.

Bari mu ci gaba da addu’a ga Allah mai ƙauna, Jehovah, kuma mu yi biyayya cikin tawali’u ga ja-gorar ruhunsa mai tsarki da gargaɗin Kalmarsa.



To walk in the law of Jehovah means to submit ourselves willingly to divine guidance.

Yin tafiya cikin shari’ar Jehobah yana nufin bin ƙa’idodinsa da zuciya ɗaya.



• What effect does Christ’s leadership have on the family life of those who submit to it?

• Yaya shugabancin Kristi yake shafar rayuwar iyalan da suka miƙa kai gare shi?



What blessings did the prophet Isaiah foretell for those who submit to the elder arrangement?

Wace albarka annabi Ishaya ya annabta ga waɗanda suka sarayar da kai ga tsarin dattawa?



During an official memorial speech on January 27, 2003, the president of the State Parliament of Baden-Württemberg, Peter Straub, commented: “All those who suffered persecution because of their religious or political beliefs and who were willing to accept death rather than submit deserve our great respect, such respect as is hard to express in words.

A lokacin wani jawabi na tuni a ranar 27 ga Janairu, 2003, shugaban Majalisar Wakilai na Baden-Württemberg, Peter Straub, ya ce: “Dukan waɗanda suka sha tsanani domin addininsu ko kuwa domin siyasa, kuma sun gwammace su mutu da su miƙa kansu, sun cancanci mu daraja su sosai, kuma ba za mu iya furta wannan darajar da kalamai ba kawai.



Whenever a translation team needs help in understanding the source text or is not sure about how a translation technique should be applied in a specific case, they can electronically submit their question to this desk.

A duk lokacin da mafassara ba su fahimci abin da suke fassarawa ba ko kuma ba su san dabarar da za su yi amfani da ita a fassarar ba, za su iya aika tambaya ta na’ura zuwa wannan sashen.



In fact, living up to our dedication and baptism means that we recognize the legitimacy of spirit-appointed authority in the congregation and willingly submit to it.

Babu shakka, aikatawa cikin jituwa da keɓewar kanmu da kuma baftisma yana nufin fahimtar dacewar iko da ruhu ya naɗa a cikin ikilisiya da kuma miƙa kai da son rai ga ikon.



We can do so even in our present imperfect state if we continue striving to submit to the transforming power of his Word.

Za mu iya bauta wa Jehobah duk da ajizancinmu idan muka ci gaba da barin Kalmar Allah ta kyautata halayenmu.



Women, Why Submit to Headship?

Mata, Me Ya Sa Za Ku Miƙa Kai Ga Shugabanci?



True, some politicians invoke God’s blessing on their efforts to achieve peace and security, but how can God bless those who do not submit to his way of ruling? —Ps.

Hakika, wasu ’yan siyasa sun roƙi albarkar Allah a kan ƙoƙarce-ƙoƙarcensu don su cim ma salama da kwanciyar hankali, amma yaya Allah zai albarkaci waɗanda suka ƙi miƙa kai ga sarautarsa?—Zab.



How will learning to submit to theocratic arrangements help to train us for life in the new world?

Ta yaya bin ja-gorar ƙungiyar Jehobah yanzu zai taimaka mana mu yi shiri don yin rayuwa a sabuwar duniya?



By conducting their daily lives in obedience to God’s laws, they show him their willingness to submit to his way of ruling both now and in the new world.

Ta wurin rayuwarsu na kullayaumi cikin biyayya da dokokin Allah fa, suna nuna shiryawarsu su yi biyayya da hanyar sarautarsa yanzu da kuma cikin sabuwar duniyan.



They dedicate themselves to Jehovah and submit to water baptism, thus making it public that they have eliminated from their lives the practices that displease God.

Sun keɓe kansu ga Jehobah sun kuma yi baftisma, domin su nuna cewa sun rabu da ayyukan da Allah baya so.



If I truly submit to Christ as Head of the congregation, then, as indicated in the following scriptures, what will I be doing?

Idan da gaske ina biyayya ga Kristi shi Shugaban ikilisiyar, to, kamar yadda aka nuna cikin nassosi na gaba, menene zan riƙa yi?



When the Christian husband deals with his wife tenderly, considerately, attentively, unselfishly, it is easier for his wife to submit to his headship.

Sa’ad da maigida Kirista ya bi da matarsa cikin ƙauna, sanin ya kamata, yana sauraronta, ba ya son kai, yana da sauƙi matarsa ta miƙa kai ga shugabancinsa.



By showing love for one another, we loyally submit to “the law of the Christ”

Ta wajen ƙaunar juna, muna bin “shari’ar Kristi” cikin aminci



4 Only humble people will submit to God’s will.

4 Mutane masu tawali’u ne kaɗai suke yin nufin Allah.



13 You can submit to the direction of holy spirit by applying the information provided for God’s people.

13 Za ka iya miƙa kai ga ja-gorancin ruhu mai tsarki ta wajen yin amfani da bayanin da aka yi tanadinsa ga mutanen Allah.



8 The anointed share in Christ’s sufferings and are willing to submit to a death like his.

8 Shafaffun Kiristoci sun sha wuya kamar yadda Yesu ya sha, shi ya sa suka yarda za su mutu kamar yadda ya mutu.



However, he recognizes our free will and wants us to submit to him voluntarily. w16.06 2:1, 2

Amma ya san muna da ’yancin yin abin da muke so kuma yana so mu bauta masa da son ranmu. w16.06 2: 1, 2