Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Moses promised Pharaoh that he would not try to see him again.

Musa ya yi wa Fir’auna alkawari cewa ba zai sake zuwa wurinsa ba.



17 Let us try to see things from Jehovah’s point of view, not just our own.

17 Bari mu yi ƙoƙari mu ga abubuwa yadda Jehobah yake ganinsu, ba bisa namu ra’ayi kawai ba.



Each time we call on a householder, we try to plant a seed of Scriptural truth.

Kowane lokaci da muka ziyarci wani, muna ƙoƙari mu dasa iri na gaskiya ta Nassi.



We should try hard to get the sense of it rather than merely expecting that there will be a change to conform to our viewpoint. —Read Luke 12:42.

Ya kamata mu yi ƙoƙari don mu fahimci ma’anar. Bai kamata mu sa rai cewa za a yi gyaran da zai jitu da ra’ayinmu ba.—Karanta Luka 12:42.



We might try to remember such verses as Ephesians 5:3 and Colossians 3:5.

Muna iya tuna da ayoyi kamar su Afisawa 5:3 da kuma Kolossiyawa 3:5.



Satan the Devil wanted to kill God’s Son, and he knew that King Herod of Jerusalem would try to kill him.

Shaiɗan Iblis yana so ne ya kashe Ɗan Allah, kuma ya sani cewa sarki Hirudus na Urushalima zai so ya kashe shi.



* The disciples, however, try to stop the children from coming to Jesus.

* Amma dai, almajiran suka yi ƙoƙarin su hana yaran zuwa wurin Yesu.



When is it appropriate to walk away from peers who try to pressure you, and why?

A wane lokaci ne ya dace ku tafi ku bar tsaranku waɗanda suke ƙoƙari su matsa muku, kuma me ya sa?



We recommend that you try studying the Bible at least once.

Muna so ka gwada nazarin Littafi Mai Tsarki ta wannan hanyar ko da sau ɗaya ne.



When others tried to prevent the little ones from approaching Jesus, he said: “Let the young children come to me; do not try to stop them.”

Sa’ad da wasu suke so su hana waɗannan yara ƙanana zuwa wurin Yesu, ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su.”



Why should we try to look for the good in others?

Me ya sa ya dace mu lura da halaye masu kyau da ’yan’uwanmu suke da su?



The service overseer should try to anticipate unusual situations and give appropriate instructions so as to minimize awkwardness.

Mai kula da hidima ya yi la’akari da abubuwa na ba-zato da za su iya faruwa, kuma ya ba da umurni da suka dace don kada matsaloli su taso.



Since we are united as “members belonging to one another,” we certainly should not be devious or deliberately try to mislead our fellow worshippers, for that is the same as lying to them.

Tun da yake mu “gaɓaɓuwa ne na junanmu,” bai kamata mu zama masu cuku-cuku ba ko kuma mu yi ƙoƙarin yaudarar ’yan’uwa masu bi, gama hakan daidai ne da yi musu ƙarya.



Because we took radical measures to try to further our cause, we were often in trouble with the authorities.

Da yake mukan ɗauki matakai masu tsanani don mu cim ma burinmu, mun riƙa samun matsala da hukuma.



Try to be aware of any tests to their faith, and help them to deal with these.

Ku san gwajin da suke fuskanta kuma ku taimaka musu su yi tsayayya da hakan.



But Jesus said: “Let the young children come to me; do not try to stop them, for the kingdom of God belongs to suchlike ones.” —Mark 10:14.

Yesu ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su: gama na irin waɗannan mulkin Allah ya ke.”—Markus 10:14.



Let us consider some Bible principles, a few examples, and some practical tips that can help all of us to try to comment more at meetings.

Bari mu tattauna wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da wasu misalai da kuma wasu shawarwari da za su taimaka mana mu riƙa yin kalami a kowane lokaci.



4 If a child is unsure about some teaching, try not to react too strongly or to respond as if you were on the defensive.

4 Ku kasance da haƙuri idan yaranku ba su tabbata da koyarwarku ba.



No matter how hard we try to do what is right, we make mistakes, sometimes serious ones. —Rom.

Duk da yadda muke ƙoƙari mu yi abin da yake da kyau, wani lokaci mukan yi kuskure mai tsanani.—Rom.



Try to imagine the full significance of Paul’s words found at 1 Corinthians 15:24, 25, 28. —Read.

Ka ƙoƙarta don ka fahimci ma’anar kalmomin Bulus da ke littafin 1 Korintiyawa 15:24, 25, 28.—Karanta.



TRY THIS: If possible, occasionally take your child with you to work and show him or her what you do to support the family financially.

GWADA WANNAN: Idan zai yiwu, ka riƙa kai yaronka wurin aiki a wasu lokatai don ka nuna wa shi ko ita abin da kake yi don tallafawa iyalin da kuɗi.



Try to have consistent rules and discipline in the two households.

Ku yi ƙoƙari ku bi tsarin da kuka kafa a iyalinku da kuma a yadda kuke hulɗa da mahaifiyar yaran.



TRY THIS: Analyze what each of your children could reasonably be expected to do that would contribute to the smooth running of your household.

GWADA WANNAN: Ka bincika abin da kowanne cikin yaranka zai iya yi don kome ya tafi daidai a gidanka.



By what means does Satan try to subvert our attitude toward immorality and violence?

Ta wurin menene Shaiɗan yake ƙoƙarin ya lalata mana hankali game da lalata da kuma nuna ƙarfi?



She says: “When treated abusively, I try to keep in mind Proverbs 19:11, which says: ‘The insight of a man certainly slows down his anger.’

Ta ce: “Ina ƙoƙari in riƙa tuna da abin da ke littafin Karin Magana 19: 11, inda aka ce: ‘Hankali yakan sa mutum ya danne fushinsa.’



0