Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bottles

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Noun

Singular
bottle

Plural
bottles

Tilo
ƙwalaba

Jam'i
ƙwalabe or kwalabai or kwalbobi

 
Bottles
  1. The plural form of bottle; more than one (kind of) bottle. <> ƙwalabe, jam'in ƙwalaba ko ƙwalba.

    1. However, when I began receiving the literature in the bottles, I knew that you had not forgotten me!”
      Amma, da na fara samun littattafai a cikin ƙwalabe, na san cewa ba ku manta da ni ba!”

    2. The men would have given them bottles of soft drinks and danced around them all the way home.
      Da sun ba su kwalaben lemo, su kuma raka su gida da rawa.

    3. They then threw the bottles into the river.
      Sai su jefa ƙwalaben cikin kogi.

    4. Such bottles can hold large quantities of water, depending on the size of the animal.
      Waɗannan goruna suna iya riƙe ruwa mai yawa, bisa ga girman dabban.

    5. When not in use, these bottles might shrivel up if hung near a fire in a room lacking a chimney.
      Sa’ad da aka ƙi yin amfani da ita, salkar na iya yin yaushi idan aka ajiye ta a ɗakin da ke cike da hayaki.

    6. (Psalm 119:83, 86) In Bible times, bottles made of animal hide were used to hold water, wine, and other liquids.
      (Zabura 119:83, 86) A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ana amfani da salkuna domin a zuba ruwa, inabi, da sauran abin sha.

    7. Skin bottles have earned a reputation for keeping water cool, even in the intense heat of the desert sun.
      An san waɗannan gorunan fata da iya riƙe ruwan sanyi har ma a lokacin zafin rana na hamada.

    8. By 16 years of age, I was drinking between 10 and 15 bottles of beer each day, and before long I started taking drugs.
      Ina shan kwalaben giya 10 zuwa 15 a rana a lokacin da nake shekara 16, kuma ba da daɗewa ba, sai na soma shan ƙwayoyi.

    9. She will involve him in child care, patiently showing him how to change diapers or prepare feeding bottles —even though he may seem clumsy at first.
      Ya kamata ta sa shi ya saka hannu wajen kula da jaririn, ta nuna masa a hankali yadda ake haɗa abincin jaririn ko kuma canja masa famfas, ko da da farko maigidan bai yi hakan ba da kyau.

    10. Nomads of the Sahara, such as the Tuareg, still use skin bottles, made out of the whole skin of a goat or a sheep.
      Har ila, makiyaya a hamada, kamar buzaye, suna amfani da goruna da aka yi da fatar akuya ko rago. [1]


Verb

Plain form (yanzu)
bottle

3rd-person singular (ana cikin yi)
bottles

Past tense (ya wuce)
bottled

Past participle (ya wuce)
bottled

Present participle (ana cikin yi)
bottling

  1. The third-person singular form of bottle. <> saka abu cikin ƙwalabe.