Noun
f

- 'yar ƙofa a garu da aka yi daga ƙasa don ruwa ya riƙa shigewa ta ciki. kofar da aka yi a jikin kasan bango don ruwan da aka yi amfani da shi amma ba a son sa a wurin ya fice waje, musamman daga mawanki ko kuma ruwan sama.
- magudanar ruwa. <> a water gutter.
- kwararo, watau ƙaramar hanya a gari. <> a narrow path.
- saƙaƙƙiyar waya mai ƙananan ƙofofi da aka alkinta ana amfani da ita wajen takaɗa gari.
- kwano amma gindinsa siririyar waya ce mai kofofi duk jikinta don tankade gari, wato abin da ya wuce ta kofofin gari ne wanda ya kasa wucewa kuwa tsaki ne.
- wani lokacin kuma ba busasshen gari ake tankadewa da ita ba sai dai tace wanda aka jika shi da ruwa, kamar na yin koko
- indararo daga saman gini. Lafazi: Rariyar hannu = kashe kuɗin da mutum ya samu ta hanyar watsar da abin da aka saya don babu tsari. sieve.