Line 449: | Line 449: | ||
# Duk wanda zai juya wa addinin Allah baya; to wannan mutum mabarnaci ne, ko da kuwa ya kirawo kansa mai gyara. | # Duk wanda zai juya wa addinin Allah baya; to wannan mutum mabarnaci ne, ko da kuwa ya kirawo kansa mai gyara. | ||
# Halaccin yin la'ana ga duk wanda ya saɓa wa gaskiya, amma ta fuskar aikinsa, ba ta ambaton sunan wani ba. | # Halaccin yin la'ana ga duk wanda ya saɓa wa gaskiya, amma ta fuskar aikinsa, ba ta ambaton sunan wani ba. | ||
== Tarjama da Tafsirin Aya Ta 64-68 == | |||
# Ka ce: "Ya ku Ma'abota Littafi, ku taho ga wata kalma mai daidaitawa tsakaninmu da ku cewa, kar mu bauta wa kowa sai Allah, kuma kar mu haɗa Shi da wani, kuma kada wani sashi a cikinmu ya riƙi wani sashi a matsayin abin bauta ba Allah ba." Idan kuwa sun ba da baya, to ku ce: "Ku shaida cewa, lalle mu Musulmi ne." --[[Quran/3/64]] | |||
# Ya ku Ma'abota Littafi, don me kuke yin jayayya game da Ibrahim, alhalin ba a saukar da Attaura da Linjila ba sai bayan shuɗewarsa? Yanzu ba za ku hankalta ba? --Quran/3/65 | |||
# Ga ku nan ku wadannan kun yi jayayya kan abin da kuke da ilimi a kai, to don me kuma kuke jayayya a kan abin da ba ku da ilimi a kansa? Kuma Allah Yana sane ku ba ku sani ba. --Quran/3/66 | |||
# Ibrahim bai taɓa zama Bayahude ba, sannan bai taɓa zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin ɓarna ne, Musulmi, kuma bai kasance ɗaya daga cikin mushrikai ba. --Quran/3/67 | |||
# Lalle mafi kusancin mutane da Ibrahim su ne wadanda suka bi shi, sai kuma wannan Annabin, da kuma wadanda suka yi Imani. Kuma Allah shi ne Majiɓincin al'amuran muminai. | |||
Bayan an kira Ma'abota Littafi zuwa ga addu'ar tsinuwa amma sun ƙi yarda, sannan an kawo musu hujjoji iri-iri wadanda suka nuna bacin addinin da suke kai, sun kuma kasa kare ɓatansu, kuma Allah ya riga ya san yadda Annabi yake maukar tausayin su, yana kwadayin shiriyarsu, sai Allah ya umarce shi da ya kirawo su gaba daya zuwa ga kalma ta bai-ɗaya, wadda kowa da kowa zai daidaita a kanta, kuma za su hada kai a kanta. Wannan kalma ita ce kadaita Allah da bauta, watau kada a bauta wa wani ba shi ba, mala'ika ne, ko wani annabi, ko waliyyi, ko wani gunki. Kada kuma su dauki wasu iayen giji, suna bauta musu ba Allah ba, har su riƙa halatta musu haram ko su haramta musu halal su kuma yarda. To idan sun bijire, sun ƙi yarda da wannan kiran; to ku muminai ku kafa su shaida cewa, ku Musulmi ne, kuma za ku ci gaba da bin wannan addinin da Allah ya zaɓa muku. | |||
Sannan Allah ya fuskantar da maganarsa ga Yahudawa da Nasara cewa, don mene ne suke jayayya game da lamarin Annabi Ibrahim; kowanne yana da'awar cewa a kan addininsa yake, Yahudawa suna cewa shi Bayahude ne, Nasara ma suna cewa shi Banasare ne, alhalin yadda gaskiyar al'amarin take, litafin Attaura da littafin Linjila, ba a saukar da su ba sai bayan mutuwarsa da lokaci mai tsawo. Yanzu ba za su yi aiki da hankulansu ba, su gane cewa, abin da suke fada karya ne? To ga shi yanzu su Yahudu da Nasara suna jayayya a kan abin da suke da ilimi a kansa na al'amarin addininsu, da abin da aka ambata a littafansu. To amma me ya sa zza su rika jayayya a kan abin da ba su da ilimi a kansa na lamarin Annabi Ibrahim, da addinin da ya rayu a kansa? Allah kam iliminsa ya kewaye komai, ya san abin da su ba su sani ba, amma su ba su san komai ba daga abin da Allah ya sani. | |||
Allah kuma ya bayyana musu gaskiyar al'amarin Annabi Ibrahim ya karyata maganar cewa shi Bayahude ne, ko Banasare. Allah ya tabbatar da cewa, Annabi Ibrahim tsaye yake ƙyam a kan addinin gaskiya, ba ruwansa da duk wata barna da shirka, yana bin umarnin Allah cikin ikhlasi, kuma ba ya cikin masu hada Allah da wani, masu bautar gumaka. | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |