Toggle menu
24K
663
183
158K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Quran/3 > Quran/3/Rijayar_Lemo_Tafsir > Quran/3/Rijayar_Lemo_Tafsir2

Ma'arif Al-Qur'an tafsir of verses 3:1 to 3:4 [1]

The first verse of this section presents a rational proof of the Oneness of Allah (don nuna babu mai iya kawo kamarsa); the second verse, the reported proof 1, followed by an answer to some doubts nursed by disbelievers towards the later part.

1. In the terminology of Islamic theology, a proof based on rational argument is called rational proof while a proof based on a verse of divine book or on a declaration made by an authority or a report narrated by a trustworthy person is called a reported proof.

The first word, Alif Lam Mim (الم ) at the head of the first verse be-longs to the special set of words used by the Qur'an (mu'ujizar Alƙur'ani) which are words of hidden meaning and are known as Mutashabihat متشبھات ، the real meaning of which is a secret between Allah and His Messenger ﷺ ، and the details of which appear a little later in the section. In the words لا إله إلا ھو (Allah: there is no god but He) which follow immediately, the doctrine of the Oneness of Allah has been put forth as a categorical declaration. It means that there is absolutely nothing worthy of worship other than Allah.

Then come the words الْحَيُّ الْقَيُّومُ (the Alive, the All-Sustaining) which lay out a rational proof of the Oneness of Allah. The essence of the argument is that worship means to present oneself before somebody in utter submission and humility. It, therefore, requires that the one who is being worshipped must occupy the highest point of honour and power and who has to be most perfect from all angles. From this it is obvious that anything which cannot sustain its own being, rather is dependent upon somebody else for its very existence, could hardly claim to have any honour or power in its own right. Therefore, it is crystal clear[2] that all things in this world which have no power to come into being by themselves, nor can they sustain it - be they idols carved in stone, or water, or trees, or angels and apostles - none of them is worthy of worship. The only Being worthy of worship is the One who has always been Alive and Present and shall always live and sustain. Such a Being is none but Allah; there is none worthy of worship but Him.

You are reading a Tazkirul Quran tafsir for the group of verses 3:1 to 3:4 [3]

The Creator and Sustainer of the universe is not a mechanical God. He is, in fact, a live and conscious Being.

He has sent guidance for man throughout the ages, including the Torah and the Bible, which were revealed to the former prophets. But man has always put different constructions upon divine teachings. Thus, through his self-styled interpretations, he has divided one religion into many. Ultimately, in accordance with God’s plan, the final book in the form of the Quran was sent down to man. The Quran is not only a genuine book of guidance but also serves as the criterion or standard of right and wrong. It tells us which is the true religion and which is the religion devised by human beings through misinterpretation.

Now those who, denying the book of the Almighty, refuse to abandon the religion devised by human beings, are deserving of His punishment. These are the people to whom God granted eyes, but who failed to see the light (sent by God in the form of this book). These are the people to whom their Creator granted minds, but who failed to understand the truth when it came to them in the form of arguments. Bowing to the truth required them to bow to the Prophet and to God, and they thought that by surrendering to the Supreme Being and His Prophet they would diminish in stature. To save their petty ‘greatness’, they refused to bow to the Truth.

Tafsirin ayoyin 1-5 na Surar Ali Imran

Allah ya bude wannan Sura da harrufa kamar yadda ya yi a Baqara, domin bayanin mu'ujizar Alƙur'ani, don nuna babu mai iya kawo kamarsa, duk kuwa da cewa magana ce da ta kunshi haruffa na Larabawa irin wadanda suke rubutu da su.

Sannan Allah ya yi bayanin Allantakarsa da cewa, shi ne abin bauta na gaskiya, wanda daga cikin siffofinsa, shi ne Rayayye, mai cikakkiyar rayuwa, wadda ta siffantu da dukkan siffofi na kamala, Tsayayye da Zatinsa, ba shi da bukata a wurin wani cikin halittarsa, kuma shi ne mai tsayawa da taimakon kowa da komai, don haka kowa yana da bukata a wurinsa.

Daga cikin taimakonsa da rahamarsa ga bayinsa, shi ne ya aiko musu da Annabi SAW, ya kuma saukar masa da Alkur'ani, wanda yake cike da gaskiya, kuma yake gaskata littattafan da suka gabace shi. Kuma Allah ya saukar da Attaura ga Annabi Musa (alaihissalam) da Linjila ga Annabi Isa (aS) tun kafin saukar da Alkur'ani. Allah ya saukar da littattafan nan ne dukkansu saboda shiriyar da mutane. A cikinsu Allah ya saukar da bin da yake bambancewa tsakanin ƙarya da gaskiya da tsakanin shiriya da ɓata, saboda haka Allah ya yi alkawarin azaba mai tsanani ga wadanda suka kafirce wa ayoyinsa a ranar gobe kiyama. Allah SWT babu wanda zai iya rinjayar sa, kuma babu abin da zai gagare shi, kuma shi mai gaggawar daukar fansa ne ga wanda ya saba masa.


Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kasancewar dalilin saukar ayoyin farko na wanna Sura shi ne jayayyar da Nasaran Najrana suka yi da Annabi SAW dangane da sha'anin Annabi Isa (aS), sai ya zamana ya dace a bude wannan Sura da wadannan haruffa, wadanda suke ishara zuwa ga kalubalantar masu karyata Alkur'ani.
  2. Faɗar Allah SWT cewa: "Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai shi..." mayar da martani ne ga Nasara masu cewa Annabi Isa (aS) Allah ne.
  3. Siffofin nan na Allah guda biyu, (Rayayye da Tsayayye da Zatinsa) hada su wuri guda yana nuna siffantuwar Allah da dukkan siffofi na kamala. 'Rayayye' yana nufin kamalar siffofinsa duka, 'Tsayayye da Zatinsa' yana nufin kamalar ayyukansa gaba daya, don haka sun kunshi kamalar Zati, da kamalar ayyuka.
  4. Attaura da Linjila shiriya ne ga mutane a lokacinsu, amma bayan saukar da Alkur'ani, babu wata shiriya da ta rage sai ta Alkur'ani kadai.
  5. Musulunci shi ne addinin gaskiya, wanda ya hada bautar Allah shi kadai da kuma imani da annabawan Allah gaba daya.

Tarjama da Tafsirin aya 5-9

A wadannan ayoyin, Allah yana bayanin gamammen iliminsa, wanda ya kewaye komai, don babu wani abu da yake ɓuya a gare shi, a sama yake ko a ƙasa. Shi ne yake halittar ku bisa kamanni daban-daban a cikin iyayenku yadda ya ga dama, don haka shi ne kadai ya cancanta a bauta wa; ba shi da wani abokin tarayya. Shi ne Mabuwayi a cikin mulkinsa; ba mai iya ja da shi ko ya fi karfinsa, kuma shi mai hikima ne a cikin ayyukansa da shari'unsa, babu wani tasgaro a cikinsu ko kadan. Shi ne wanda ya saukar wa wannan Annabi Alkur'ani, wanda ya kunshi ayoyin da suke a fili, ma'anoninsu a bayyane suke, babu wani abu mai rikitarwa tare da su, ma'anoninsu a bayyane suke, babu wani abu mai rikitarwa tare da su, su ne kuma tushen wannan littafi, kuma su ne mafiya yawa a cikinsa. A cikinsa kuma akwai wadansu ayoyi wadanda ma'anarsu take da rikitarwa ga wasu mutane. To amma sai a samu wadansu karkatattun mutane masu cutar kauce wa gaskiya a zukatansu, suna bibiyar wadannan ayoyi masu rikitarwa, suna barin ayoyin da ma'anoninsu suke a fili, ba don su sami wani abu da za su kafa hujja da shi a kan soye-soyen zukatansu. Su kuwa wadannan ayoyi masu rikitarwa, babu wanda ya san hakikanin fassararsu sai Allah. Malamai masu zurfin ilimi na Alkur'ani su ma sukan san tafsirin ma'anonin ayoyin, amma ba za su iya sanin hakikanin al'amarin ba, da yadda karshen zai kasance, domin wannan Allah ne kadai ya san shi. Malamai masu zurfin ilimi sukan shelanta imaninsu da wadannan ayoyi masu rikitarwa. Duk kuma ayoyin na Alkur'ani daga Allah ne, amma ba kowa ne yake wa'azantuwa ba sai masu lafiyayyen hankali.

An karbo daga A'isha (rA) ta ce: "Annabi SAW ya karanta wannan ayar, sai ya ce: "Idan kika ga wadanda suke bibiyar ayoyi masu rikitarwa a cikin Alkur'ani; to su ne wadanda Allah ya ambata, don haka ki guje su." (When you see such verses, avoid them, for it is they whom Allah has pointed out (in the mentioned verses)[4]).

Malamai masu zurfin ilimi addu'a suke yi ko da yaushe, suna rokon Allah kada ya karkatar da zukatansu su saki shiriya bayan Allah ya shiryar da su, ya yi musu rahama, ya kara m usu imani da tsayuwa a kan gaskiya, domin Allah shi ne mai yawan kyauta da ihsani ga bayinsa. Kuma suna addu'a suna cewa:

"Ya Allah, kai ne za ka tara mutane a rana Alkiyama, ranar da babu shakka a zuwanta, domin yin hukunci da sakayya ga kowa a kan aikinsa, don haka ka gafarta mana a wannan ranar, ka yi mana afuwa."

Sun kuma yi Imani da cewa, lalle Allah ba ya saba alkawarinsa na cewa, wanda duk ya yi imani da shi, ya bi Manzonsa; to zai gafarta masa.

An karbo daga Abdullahi dan Amru ya ce, Annabi SAW ya ce:

Abdullah b. Amr b. al-'As reported that he heard Allah's Messenger (ﷺ) as saying:

"Lalle zukatan 'yan'adam duka suna tsakanin yatsu biyu ne

Verily, the hearts of all the sons of Adam are between the two fingers


daga yatsun Allah Mai rahama, tamkar zuciya daya,

out of the fingers of the Compassionate Lord as one heart.


yana sarrafa su yadda ya ga dama."

He turns that to any (direction) He likes.


Sannan sai Annabi SAW ya yi addu'a yana cewa: "Ya Allah Mai sarrafa zukata, ka sarrafa zukatanmu a kan da'arka."

Then Allahs Messenger (ﷺ) said: O Allah, the Turner of the hearts, turn our hearts to Thine obedience. [5]


Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Jan hankalin dan'adam a kan ya kyautata halayensa, da ayyukasa, domin Allah Mahaliccinsa yana ganin sa, babu abin da yake ɓuya a gare shi.
  2. Yana daga cikin alamomin karkacewar zuciya, bibiyar ayoyin Alkur'ani masu rikitarwa, don mutum ya saka kansa ko wasu cikin shakka.
  3. Idan mai karatu ya yi wakafi a daidai (illallahu) to hakan yana nuna a cikin Alkur'ani akwai abin da babu wanda ya san fassararsa sai Allah. Fassara a nan, ko kuma 'tawili', kamar yadda ya zo a ayar, ana nufin karshen al'amari, ko kuma yadda hakikanin al'amarin zai kasance. A nan akwai jarrabawa da Allah yake yi wa bayinsa game da abubuwan da ba za su iya fahintar su da tsurar hankalinsu ba. Shin za su ce sai sun gano su ta haka, ko kuwa za su sallama wa Allah SWT su tsaya a matsayinsu?
  4. Babu masu jayayya da abin da ya zo daga Allah sai masu karamin sani, wadanda ba su yi zurfi ba a cikin ilimi. Wannan yana nuna falalar yin ilimin shari'a mai zurfi, domin yana taimakawa wajen samun tsayuwa a kan gaskiya.
  5. Daga wannan aya za mu fahimci cewa akwai abin da ake kira 'ilimi', akwai kuma kafuwa da zurfi cikin ilimin, don haka mai neman ilimi kada ya hakura da dan kadan, ya yi kokarin kafuwa da zurfi a cikinsa.
  6. Babu mai amfana da wa'azuzzukan Alkur'ani sai masu hankali. Duk sa'adda hankalin mutum ya karu; to fahintarsa ga Alkur'ani za ta karu, duk sa'adda ka ga ba ya wa'azantuwa da Alkur'ani; to hakan yana nuna karancin hankalinsa ne.
  7. Zuciya tana da hali guda biyu, halin daidaita da kuma halin karkata, don haka mutum a ko da yaushe yana bukatar ya rika rokon Allah da kada zuciyarsa ta karkace, domin ba a hannunsa take ba, tana hannun Allah ne, shi ne yake yin yadda ya ga dama da ita, don haka kada mutum ya rudu da kansa, ya dogara a kan imaninsa, sau tari an sami mai imanin da ya tabe, ya saki hanya.
  8. Idan mutum ya samu kubuta daga fitinar shubuha, da fitinar sha'awa; to ya gama samun manyan bukatunsa biyu na duniya da lahira, su ne shiriya da rahama.

Tarjama da Tafsirin aya 10-11

Bayan Allah SWT ya ambaci ranar lahira, ya kuma tabbatar da cewa, rana ce da babu kokwanto ga zuwanta, ya kuma ambaci halin muminai na neman gafara da afuwar Allah a wannan ranar, sai kuma a wadannan ayoyi Allah SWT ya kawo bayanin kafirai da yadda halinsu zai zamanto a wannan ranar. Allah Ta'ala ya bayyana cewa wadanda suka kafirce wa Allah da ayoyinsa, kuma suka karyata manzanninsa, suka nuna musu kiyayya, kuma suka bijire wa addinin Allah; to wadannan dukiyoyinsu da 'ya'yansu ba za su taɓa yi musu amfani ba, kuma ba za su kubutar da su daga azabar Allah ba, yayin da ta zo musu. Makomarsu ita ce wutar Jahannama, su ne makamashinta da za a rika rura ta, kuma za su dawwama a cikinta har abada, babu ranar fitarsu. Wannan sunnar Allah ce wadda ba ta canzawa. Al'amarin wadannan daidai yake da al'amarin Fir'auna da jama'arsa da sauran al'ummomin da suka karyata Allah da manzanninsa, su ma haka Allah ya halakar da su saboda zaluncinsu, haka da ma Allah yake, mai tsananin ukuba ne ga duk wanda ya bijire masa, ya ki tuba ya dawo gare shi.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kada mutum ya rudu da da yawan dukiya ko 'ya'ya ko wani kyale-kyale na duniya, su sa shi ya yi ta saɓawa Allah; ranar da azabar Allah ta zo masa, duk wadannan abubuwa ba za su amfane shi da komai a wurin Allah ba.
  2. Mumini yana amfana da dukiyarsa da 'ya'yansa a lahira idan ya tafiyar da su kamar yadda Allah ya tsara masa.
  3. Duk kafirci a wurin Allah iri daya ne, na da da na yanzu, babu bambanci.
  4. Zunubban bayi su ne suke jawowa Allah ya halaka su, amma ba don zalunci ba. Allah ba azzalumin kowa ba ne. Sunnar Allah yana gudanar da ita a kan kowa a kowane wuri, kuma a kowane zamani, don haka babu inda mai laifi zai gudu ya kubuta.

Tarjama da Tafsirin aya 12-14

A wadannan ayoyi, Allah yana umartar Manzonsa (SAW) da ya faɗawa kafirai cewa, muminai sai sun yi rinjaye a kansu a rayuwarsu ta duniya, sannan idan ranar alƙiyama ta tsaya, a tarkata su gaba daya cikin wutar Jahannama, domin ita ce shimfidar da suka tanadar wa kawunansu tun a nan duniya. Tir kuwa da wannan shimfida.

Allah SWT kuma ya bayyana wa kafirai ko kuma muminai cewa, sun ga alama a fili da ta nuna muminai ne za su yi rinjaye a kan kafirai, kuma Allah ya yi alkawarin zai daukaka addininsa, kuma ya karfafi Manzonsa. Wannan alama ita ce, kungiyoyin mayaka biyu da suka hadu don kafsa yaki a tsakaninsu. Kungiyar farko muminai ne, masu yaki don daukaka kalmar Allah, su ne Annabi da Musulmi a yakin Badar; daya kungiyar kuma kafirai ne, suna yaki ba don Allah ba, su ne Quraishawa kafiran Makka a ranar Badar. A lokacin, muminai suna ganin kafirai a ido, sun ninka su gida biyu, Wannan kuwa ya ƙara musu dogaro ga Allah da neman taimakonsa, wanda yin hakan yana daga cikin dalilan samun nasara. To yadda Allah ya ba wa wadannan muminai 'yan kadan nasara a kan abokan gabarsu masu yawa, akwai darasi da wa'azi ga duk wanda Allah ya ba shi basira da hangen nesa.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Da a ce Musulmi za su koma ga addininsu na Musulunci, su yi riko da koyarwarsa ta aqida da ibada da kyawawan halaye da kyakkyawar mu'amala; to da Allah ya ba su nasara da rinjaye a kan duk wani mai gaba da su, kamar yadda ya yi wa musulmin farko, har suka mallaki gabashin duniya da yammacinta.
  2. Yaki shi kadai ba zai sa a sami nasara ba, har sai idan ya kasance don Allah aka yi shi, kuma an kiyaye dokokin Allah a cikinsa.
  3. Yawan sojoji ko mayaka ba shi ne yake sa a sami cin nasarar yaki ba; ana samun nasara ne da taimakon Allah da daukinsa.
  4. Wajibi ne mu dauki darusa daga rayuwar al'ummomin da suka gabace mu, mu aikata abin da suka yi Allah ya taimake su ya ba su nasara, mu nesanci aikin da wasunsu suka yi, sai Allah ya halakar da su a duniya da lahira.
  5. Duk mutumin da ba ya wa'azuntuwa; to wannan alama ce da take nuna raunin basirarsa da hangen nesansa.

Tarjama da Tafsirin aya 15-17

Bayan da Allah SWT a baya ya nuna cewa, dukiya da 'ya'ya ba za su amfani wadanda suka kafirce masa ba, sai kuma a wadannan ayoyin yake gargadi ga wadanda kyale-kyalin rayuwar duniya za su shagaltar da su, har su manta da lahira. Allah ya bayyana cewa, ya sanya wa mutane son wasu abubuwa na sha'awa, kamar mata da 'ya'ya maza da tara nau'ukan dukiyoyi iri-iri, kamar zinare da azurfa, da kiwatattun dawakai da rakuma da shanu da kananan dabbobi da gonakin noma. Allah ya bayyana duk wadannan abubuwan na more dadin duniya ne, daga karshe su tafi su bar su, kuma a wurin Allah kadai ake samun kyakkyawar makoma da sakamako mai yawa marar yankewa.

Allah SWT kuma ya bayyana wa Annabinsa SAW cewa, akwai abin da ya fi wadannan kyale-kyali kayan sha'awar na duniya a wurin gidaje manya-manya, wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu, ga kuma tsarkakan mata a cikinsu. Kuma wannan ni'imar ta har abada ce, ba mai yankewa ba, za su yi ta zama a cikinta har abada. Tare da wadannan ni'imomin kuma akwai wata babbar ni'ima, wadda ta zarce kowace ni'ima girma, ita ce samun yardar Allah SWT.

An karbo daga Abu Sa'id Alkhudri (rA) ya ce; Manzon Allah ya ce: "Allah Ta'ala zai ce wa 'yan Aljanna: "Ya ku 'yan Aljanna." Sai su ce: "Mun amsa maka, ya Ubangijinmu," Sai ya ce: "Shin kun yarda?" Sai su ce: "Me zai sa ba za mu yarda ba, alhalin ka ba mu abin da babu wanda ka taɓa ba shi irinsa a cikin halittarka?" Sai Allah ya ce: "To zan ba ku abin da ya fi wannan da na ba ku." Sai su ce: "Ya Ubangiji, mene ne kuma ya fi wannan da ka ba mu?" Sai ya ce: "Zan haltta muku yardata, daga yanzu ba zan yi fushi da ku ba har abada."

Narrated Abu Sa`id Al-Khudri:

The Prophet (ﷺ) said, "Allah will say to the people of Paradise, "O the people of Paradise!" They will say, 'Labbaik, O our Lord, and Sa`daik, and all the good is in Your Hands!' Allah will say, "Are you satisfied?' They will say, 'Why shouldn't we be satisfied, O our Lord as You have given us what You have not given to any of Your created beings?' He will say, 'Shall I not give you something better than that?' They will say, 'O our Lord! What else could be better than that?' He will say, 'I bestow My Pleasure on you and will never be angry with you after that.' " [6]

  1. An karbo daga Abu Sa'id Alkhudri (rA) ya ce; Manzon Allah ya ce:
    Narrated Abu Sa`id Al-Khudri: The Prophet (ﷺ) said,

  2. "Allah Ta'ala zai ce wa 'yan Aljanna: "Ya ku 'yan Aljanna."
    "Allah will say to the people of Paradise, "O the people of Paradise!"

  3. Sai su ce: "Mun amsa maka, ya Ubangijinmu,"
    They will say, 'Labbaik, O our Lord, and Sa`daik, and all the good is in Your Hands!'

  4. Sai ya ce: "Shin kun yarda?"
    Allah will say, "Are you satisfied?'

  5. Sai su ce: "Me zai sa ba za mu yarda ba, alhalin ka ba mu abin da babu wanda ka taɓa ba shi irinsa a cikin halittarka?"
    They will say, 'Why shouldn't we be satisfied, O our Lord as You have given us what You have not given to any of Your created beings?'

  6. Sai Allah ya ce: "To zan ba ku abin da ya fi wannan da na ba ku."
    He will say, 'Shall I not give you something better than that?'

  7. Sai su ce: "Ya Ubangiji, mene ne kuma ya fi wannan da ka ba mu?"
    They will say, 'O our Lord! What else could be better than that?'

  8. Sai ya ce: "Zan halatta muku yardata, daga yanzu ba zan yi fushi da ku ba har abada."
    He will say, 'I bestow My Pleasure on you and will never be angry with you after that.' "

Kuma Allah mai ganin duk bayinsa ne, muminai da kafirai, da mutanen kirki da na banza, yana sane da halin da kowannensu yake ciki, don haka mai yi musu sakayya ne a kan ayyukansu kyawawa da munana.

Sannan sai Allah SWT ya ambaci wadanda suka cancanci samun waccan ni;ima da ya mbata ta lahira. Ya nuna cewa, su ne masu kamun-ƙafa a wurinsa da imanin da suka yi da shi, da littafinsa da Manzonsa, suna rokon sa da ya yi musu baiwar gafarar zunubansu, ya kuma tsare su shiga azabar wuta. Sannan ya ƙara ambatar wasu siffofin nasu da cewa, su masu hakuri ne, wajen aikata da'a da barin sabon Allah, da hakuri a kan kaddara marar dadi, kuma masu gaskiya ne a maganganunsu da ayyukansu, masu da'a ne ga Allah, masu ciyar da dukiyoyinsu don Allah a duk inda ya zama wajibi, ko ta hanyar neman lada, sannan masu neman gafarar Allah ne a karshen dare.

An karbo daga Abu Huraira (rA) ya ce, Manzon Allah SAW ya ce: "Ubangijinmu Tabaraka wa Ta'ala yana sauka a sama ta kusa a kowane dare, yayin da sulusin karshe na daren ya yi saura, yana cewa: "Wane ne zai roƙe ni, in amsa masa, wane ne zai tambaye ni, in ba shi, wane ne zai nemi gafarata, in gafarta masa?" [7]

  1. Abu Hurairah narrated that the Messenger of Allah said:
    An karbo daga Abu Huraira (rA) ya ce, Manzon Allah SAW ya ce:

  2. “Our Lord descends every night to the nearest heaven,
    "Ubangijinmu Tabaraka wa Ta'ala yana sauka a sama ta kusa a kowane dare,

  3. until the last third of the night remains, so He says:
    yayin da sulusin karshe na daren ya yi saura, yana cewa:

  4. ‘Who is calling upon Me so that I may answer him?
    "Wane ne zai roƙe ni, in amsa masa,

  5. Who is asking from Me so that I may give him?
    wane ne zai tambaye ni, in ba shi,

  6. And who is seeking forgiveness from Me, so that I may forgive him.’”
    wane ne zai nemi gafarata, in gafarta masa?"

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Rage nuna damuwa ga kyale-kyalin duniya, mai gushewa nan da nan da himmatuwa wajen neman lahira, mai dawwama har abada.
  2. Duk yawan abin duniyar da bawa zai samu; to jin dadi ne wucin-gadi, zai mutu ya bar shi. Ni'ima ta har abada ita ce ni'imar lahira.
  3. Wadannan ni'imomi da aka ambata a nan, a kamata bawa ya kalle su ta fuskar da za su amfane shi, ba kallo irin na sha'awa ba. Idan ya yi haka to za su fi karfin zuciyarsa, har su karkatar da shi daga kan hanyar gaskiya.
  4. Gargadi ga mai saba wa Allah cewa, Allah yana ganin duk aikin da yake yi, kuma zai saka masa a kai.
  5. Kowace daya daga cikin sifofin masu tsoron Allah da Allah ya ambata, sifa ce mai matukar muhimmanci a rayuwa.
    1. Da hakuri ne mumini zai jure wa duk wani radadi, zai guji raki, zai rungumi nauyin da'awa da aikin alheri da ya hau kansa, zai mika wuya ga umarnin Allah SWT.
    2. Da gaskiya ne mumini yake samun daukaka, domin ƙarya rauni ce, kasa fadar gaskiya ma rauni ne.
    3. Da da'a ga Allah ne mumini zai zo da hakkin Allah na bauta masa shi kadai, kuma ya tsare matsayinsa na shi bawan Allah ne, ba bawan wani ba.
    4. Da ciyarwa mumini zai 'yanta kansa daga bauta wa kudi da karantar rowa, ya habaka alaka ta mutuntaka tsakanin mutum da mutum.
  6. Allah ya kinsa wa namiji son haihuwar ɗa namiji. Yakan yi farin ciki da samun sa, da kuma alfahari da yawan 'ya'ya maza.
  7. Halaccin yin tawassuli da imanin mutum da Allah da sauran rukunan imani. Wannan yana karkashin tawassuli da ayyuka na kwarai.

Tarjama da Tafsirin aya 18

Bayan Allah ya yabi bayinsa muminai, sai kuma ya ambaci dalilai na zahiri masu karfi, wadanda suke tabbatar da kadaitakar Allah. Wadannan dalilai su ne; shaidar Allah, inda ya ba da shaidar cewa, babu abin bauta wa da gaskiya sai shi. Sannan ya biyo ta da shaidar mala'ikunsa da ta malamai a cikin bayinsa, wanda kuma shi yake tsaye da adalci cikin dukkanin lamura da kuma dukkan ayyukansa.

Allah kuma ya sake tabbatar da wajabcin a bauta masa shi kadai, ba tar da an hada shi da abokin tarayya ba. Ya kuma bayyana cewa, shi Mabuwayi ne, ba wanda zai iya ja da shi, ko ya gagare shi, kuma Mai hikima ne a cikin duk maganganunsa da ayyukansa.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Girman lamarin Tauhidi, ta yadda Allah shi da kansa ne yake ba da shaida a kai.
  2. Bayanin falalar mala'iku, ta yadda Allah ya ambace su a matsayin mataki na biyu bayansa.
  3. Falalar malamai ta fuskoki daban-daban kamar haka:
    1. Allah ya ware su su zama shaida a kan wani babban al'amari, wanda shi ne Tauhidi.
    2. Allah ya hada shaidarsa tare da shaidarsu da ta mala'iku.
    3. Allah ya kirawo su da sunan 'masu ilimi', wanda hakan yake nuna cewa, lalle sun siffantu da wannan sifa ta ilimi.
    4. Allah ya zabe su suka zama masu shaida, kuma hujja a kan sauran mutane, dole sauran mutane su yi aiki da hujjar da suka bayar, sai ya zamanto duk wanda ya yi aiki da wannan abu da suka yi shaida a kansa; to suna da kamasho na lada a wurin Allah.
    5. Zabo su da Allah ya yi su zamanto masu ba da shaida yana nuna cewa su a wurinsa adalai ne, ba abin suka ba ne, don ba a kafa shaida sai da adali.

Tarjama da Tafsirin aya 19-20

Bayan Allah ya bayyana cewa shi kadai ne ya cancanta a bauta masa, sai kuma ya zo da bayani a kan addinin da za a bauta masa da shi. Allah ya tabbatar da cewa, lalle addinin gaskiya, kuma karbabbe a wurin Allah, shi ne Musulunci, Allah ba zai yarda a bauta masa da wani addinin ba. Sannan ya bayyana dalilin sabanin ma'abota littafi da cewa, ya faru ne bayan an tsayar musu da hujja ta hanyar aiko musu da annabawa da saukar musu da littattafai, kuma abin da ya kai su ga sassabawa shi ne zalunci da ketare haddi da ya rika faruwa a tsakaninsu.

Sai kuma Allah ya kawo batun sakamakon wanda ya kafirce wa ayoyinsa da cewa, Allah zai yi masa hisabi a kan wannan, cikin gaggawa, zai lissafa dukkan ayyukan bayinsa ba tare da bukatar amfani da wata na'ura ta lissafi ba, kuma duk yawansu a lokaci guda, a kuma wuri guda, a dan takaitaccen lokaci. Sannan ita kanta ranar hisabin dab take da zuwa, domin rayuwar duniya gajeriya ce.

Sannan Allah ya karkatar da akalar magana zuwa ga Annabinsa cewa, idan kafirai sun yi jayayya da shi a kan gaskiyar da ya zo musu da ita, to ya fito ya fada musu cewa, shi dai yana yin aikinsa ne ga Allah shi kadai. Ya kuma umarce shi da ya fito ya fada wa Yahudawa da Nasara wadanda Allah ya ba su littafi da kuma mushirikai wadanda ba su da wani littafi: Shin sun mika wuya ga Allah, kuma za su bauta masa shi kadai? Idan sun mika wuya kamar yadda su musulmi suka mika wuya, to sun shiryu, sun hau turbar gaskiya. Idan kuwa suka bijire wa wannan kira da ake yi musu, to ba wani laifi a kan shi Ma'aiki, domin isar da sako ne kawai aikinsa. Allah yana ganin duk bayinsa, ya san wanda zai karbi shiriya da wanda ba zai karba ba, kuma makomar kowa ga Allah take, zai yi wa kowa hisabi bisa aiknsa na alheri ko na sharri.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Musulunci ne kadai addinin da Allah ya yarda a bauta masa da shi, domin shi ne addinin annabawa gaba dayansu.
  2. Rashin adalci shi ne babban abin da yake haifar da sabani da rikici tsakanin al'umma.
  3. Duk mutumin da yake jayayya da kai, ba don ku fahimci gaskiya ba kai da shi, sai don ya tabbatar da son zuciyarsa; to ka rabu da shi, domin jayayya da shi ba ta da sauran amfani.
  4. Ci gaba da sabani bayan bayyanar ilimi da tsayuwar hujja abu ne mai munin gaske.
  5. Shiriya tana da yanayi da kamanni ne iri daya, shi ne hakikanin Musulunci; duk wani abu ba wannan ba; to bata ne ba shiriya ba.

Tarjama da Tafsirin aya 21-22

Allah yana ba da labarin wadanda suka kafirce wa ayoyinsa cewa, ba a nan suka tsaya ba; sun ci gaba da kutsawa cikin shisshiginsu da kafircinsu, har suka kai ga kashe wasu annabawa da manzanni, ba tare da sun yi musu wani laifi ba. Hakanan suka rika kashe bayin Allah na gari masu yin umarni da a yi adalci, kuma a yi kyakkyawan aiki, suke hana mummuna. Kashe irin wadannan bayin Allah shi ne kololuwar girman kai, kmar yadda Manzon Allah ya ce: "Girman kai shi ne watsi da gaskiya da wulakanta mutane."

Arrogance means ridiculing and rejecting the Truth and despising people." [8]

Don haka Allah ya umarci Annabinsa, da ya yi musu albishir da wata azaba mai radadi, sakamakon kafircinsu da miyafun ayyukansu. Allah ya bayyana cewa ayyukan wadannan mutane duk sun rushe, sun lalace, ba abin da zai amfane su a duniya ko a lahira, kuma har ila yau ba za su sami mai taimakon su ba, wanda zai kubutar da su daga azabar Allah.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Wadanda suke kafirce wa ayoyin Allah, kuma suke kashe annabawa da masu wa'azi, Allah ya hada musu azaba iri uku:
    1. Hada su da bacin rai da ciwon damuwa, don haka ya ce: "Yi musu albishir da wata azaba mai radadi."
    2. Gushewa duk wani abu mai amfani a fare su a duniya da lahira gaba daya.
    3. Rashin mai taimako ko agaji a gare su.
  2. Kasancewar sun saba wa Allah ta fuskoki uku, sai ukubarsu ma ta zama iri uku:
    1. Sun kafircewa ayoyin Allah, sai ya ce a yi musu albishir da azaba mai radadi.
    2. Sun kashe annabawa, sai Allah ya rushe daukacin ayyukansu na alheri, ba zai yi musu amfani ba duniya da lahira.
    3. Sun kashe malamai masu wa'azi, sai Allah ya hana musu samun masu taimakon su yayin da azabar Allah ta zo musu, kamar yadda wadannan malamai suka rasa masu taimakon su lokacin da aka zo kashe su.
  3. Malamai masu wa'azi su suke biye da annabawa wajen martaba a wajen Allah.

Tarjama da Tafsirin aya 23-25

A nan Allah yana ba da labarin wadanda aka ba su wani kaso na ilimin littafin da Allah ya saukar, su ne Yahudawa cewa, lokacin da ake kiran su su zo ga hukuncin littafin da suka yi imani da shi, suka yarda da abin da yake cikinsa cewa daga Allah yake, sai wasu daga cikinsu suka rika bijirewa, suna goce wa hukuncin wannan littafin. Kuma abin da ya jawo har suka yi haka shi ne karyar da suka yarda da ita na cewa, Allah ba zai yi musu azaba ba, sai ta 'yan kwanaki kadan kididdigaggu, sai ya fito da su. To wannan karyar ce ta rude su a addininsu, har ma suke ganin cewa, suna iya sabawa hukuncin Allah, ko su bijire masa.

An karbo daga Abdullahi dan Umar (rA) ya ce:
Narrated `Abdullah bin `Umar:

Yahudawa sun je wurin Annabi SAW
The Jews came to Allah's Messenger (ﷺ)

suka fada masa cewa wani namiji da wata mata daga cikinsu sun yi zina,
and told him that a man and a woman from amongst them had committed illegal sexual intercourse.
a Jew and a Jewess were brought to Allah's Messenger (ﷺ) who had committed adultery.

sai Manzon Allah ya ce musu: "Me kuka sani a cikin littafin Attaura dangane da jefe mazinata?"
Allah's Messenger (ﷺ) said to them, "What do you find in the Torah (old Testament) about the legal punishment of Ar-Rajm (stoning)?" [9]
Allah's Messenger (ﷺ) came to the Jews and said: What do you find in Torah for one who commits adultery? [10]

Sai suka ce: "Ai kunyata (shame) su muke yi, kuma a yi musu bulala."
They replied, (But) we announce their crime and lash them."

Sai Abdullahi dan Salam ya ce: "Qarya kuke yi,
Abdullah bin Salam said, "You are telling a lie;

a cikin Attaurah suka bude ta, sai daya daga cikinsu ya sa hannunsa ya danne ayar jefewa,
Torah contains the order of Rajm." They brought and opened the Torah and one of them solaced his hand on the Verse of Rajm
They brought it and recited it until when they came to the verse pertaining to stoning, the person who was reading placed his hand on the verse pertaining to stoning,

ya rika karanta abin da yake gabanta, da abin da yake bayanta.
and read the verses preceding and following it.
and read (only that which was) between his hands and what was subsequent to that.

Sai Abdullahi dan Salam ya ce: "Cire hannunka!"
Abdullah bin Salam said to him, "Lift your hand."
Abdullah b. Salim who was at that time with the Messenger of Allah (ﷺ) said: Command him (the reciter) to lift his hand.

Yana cire hannunsa, sai ga ayar
When he lifted his hand, the Verse of Rajm was written there.
He lifted it and there was, underneath that, the verse pertaining to stoning.

sai kuma dukansu suka ce: "E, gaskiya ya fada, ya Muhammadu, akwai ayar jefe mazinaci a cikin Attaura."
They said, "Muhammad has told the truth; the Torah has the Verse of Rajm.

Sai Manzon Allah ya ce a je a jefe su. Aka jefe su.
The Prophet (ﷺ) then gave the order that both of them should be stoned to death. (`Abdullah bin `Umar said, "I saw the man leaning over the woman to shelter her from the stones."
Allah's Messenger (ﷺ) pronounced judgment about both of them and they were stoned. Abdullah b. 'Umar said: I was one of those who stoned them, and I saw him (the Jew) protecting her (the Jewess) with his body.

Dangane da batun Yahudawa na cewa ba za a sa su wuta ba sai na 'yan kwanaki kadan, Abu Hurairah ya ruwaito cewa, Manzon Allah ya tambayi Yahudawa:

"Su wane ne 'yan wuta?"
"Who are the people of the (Hell) Fire?" [11]

Sai suka ce: "Za mu shiga wuta na wani dan lokaci kadan, sannan sai a cire mu, a sa ku a madadinmu."
They said, "We shall remain in the (Hell) Fire for a short period, and after that you will replace us."

Sai Annabi ya ce musu: "Ku yi mana shiru, wallahi har abada ba za mu maye gubinku a cikinta ba."
The Prophet (ﷺ) said, "You may be cursed and humiliated in it! By Allah, we shall never replace you in it."

Sannan Allah ya tsawatar da su azabar ranar da za a tattaro su gaba dayansu, yana mai cewa, yaya halinsu zai kasance tare da wadannan miyagun ayyuka nasu, lokacin da za a zatar da hukunci a tsakaninsu, ranar da babu kokwanto a zuwanta, ita ce ranar alkiyama? A wannan rana za a cika wa kowane rai sakamakon aikinsa na alheri ko na sharri, babu wanda za a zalunta ta hanyar a tauye masa ladansa ko a kara masa laifin da ba shi ya yi ba ko a hukunta shi da laifin wani. Allah yana fada a hadisi Qudsi:

"Ya ku bayi na, ni na haramta wa kaina zalunci..."
"O My servants, I have forbidden oppression for Myself..." [12]

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Allah yana iya ba wa bawansa ilimi, amma kuma ya rasa samun dacen aiki da ilimin.
  2. Wajibi ne Musulmi ya yi hattara ya bar guje wa aiki da hukuncin Allah SWT. Dole ya saurara, kuma ya bi, ya sallama.
  3. Burace-burace mummunar dabi'a ce da take jawo wa mutum ya yarda da abin da ba gaskiya ne ba, ya saki aiki da gaskiya.
  4. Mutum duk sanda ya rika ganin shi ba za a saka shi a wuta ba, har ya kai ga qudurce hakan, wannan yana iya kai shi ga tsaurin idon keta dokar Allah da bijire wa gaskiya.
  5. Rudewa da yawan aiki na kwarai alama ce ta karancin hangen nesa, domin ba wai mutum ya yi aikin ba ne muhimmi; muhimmin abu shi ne Allah ya karbi aikinsa. Domin akwai wanda aikinsa na wahala ne kadai, saboda bai cika sharadin karbuwarsa ba ko kuma ya hada shi da abin da zai lalata shi.

Tarjama da Tafsirin aya 26-27

A wadannan ayoyi, Allah yana umartar Annabinsa da ya roke shi, ya girmama sunansa, ya ce: Ya Allah wanda mulkin komai naka ne, kai ne Mamallakin duniya da lahira da duk abin da yake cikinsu, kai kake bayar da mulki ga wanda ka ga dama ka kuma kwace mulki daga wanda ka ga dama; kana daukaka wanda ka ga dama ta hanyar hore masa aikin da'a gare ka ko ta hanyar ba shi mulki da iko ko ka ba shi nasara ko wanin haka. Kuma kana kaskantar da wanda ka ga dama ta hanyar ya zama mai saba maka ko ta hanyar kwace mulkinsa ko dora makiyansa a kansa, ko makamancin haka. Alheri duk yana hannunka. Lalle Allah kai mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagre ka aiwatarwa idan ka ga damar aiwatar da shi.

Yana daga cikin cikakken ikonka ya Allah, ka shigar da dare a cikin yini, kuma ka shigar da yini a cikin dare, watau ka sanya wasu sa'o'in dare a cikin sa'o'in yini, ko wasu sa'o'in yini ka qara su a kan sa'o'in dare. Kuma kana fitar da mai rai daga matacce, kamar fitar da mutum ko dabba mai rai daga ruwan maniyyi ko ka fitar da shuka daga kwayar iri ko kaza daga kwai ko kuma ka fitar da mumini daga kafiri. Hakanan kuma kana fitar da matacce daga mai rai, kamar fitar da ruwan maniyyi daga mutum ko dabba mai rai, ko ka fitar da kwaya daga shuka ko ka fitar da kwai daga kaza ko ka fitar da kafiri daga tsatson mumini. Kuma kana arzuta wanda ka ga dama cikin bayinka da arziki mai yawa, ba tar da kuntata masa ba.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Mulki gaba daya na Allah ne, a wurinsa ne ya kamata a nema, ba a wurin wani, ko wasu ba.
  2. Don Allah ya ba wa mutum mulki ba shi yake nuna ya daukaka shi ba. Zai iya ba shi mulki, amma ya zama a kaskance, wasu ne suka sarrafa shi yadda suke so. Ko kuma Allah ya hana masa ikon tafiyar da mulkin da siyasar al'ummarsa, don haka ya rayu cikin rauni da gazawa. Kamar yadda rashin samun mulki ba ya nuna kaskanci, Allah yakan daukaka wanda ya ga dama ta wasu hanyoyi daban, ba sai ta hanyar mulki ba.
  3. Duk alheri a hannun Allah yake shi kadai, don haka ka nema a wurinsa.
  4. Allah ne mai ba da arziki, shi ne mai hanawa, don haka bawan da ya nema a wajensa, zai samu.
  5. Duk aikin Allah alheri ne, don haka ba a jingina masa sharri, kamar yadda Manzon Allah ya ce: "Alheri duka yana hannunka, kuma ba a jingina maka sharri."


Ayoyi 21-25

  1. Lalle wadanda suke kafirce wa ayoyin Allah, kuma suke kashe annabawa ba tare da hakki ba, kuma suke kashe wadanda suke yin umarni da adalci cikin mutane, to ka yi musu albishir da wata azaba mai radadi. --Quran/3/21
  2. Wadannan su ne wadanda ayyukansu suka lalace a duniya da lahira, kuma ba su da wasu mataimaka. --Quran/3/22
  3. Shin ba ka ga wadannan da aka ba su wani kaso na ilimin Littafi ba, ana kiran su zuwa ga Littafin Allah don Ya yi hukunci a tsakaninsu, sannan sai wani bangare daga cikinsu suna juya baya, suna masu bijirewa.--Quran/3/23
  4. Wannan kuwa saboda su sun ce: "Wuta ba za ta shafe mu ba sai a wadansu 'yan kwanaki kididdigaggu." kuma abin da suka kasance suna kirkira a addininsu shi ne ya rude su. --Quran/3/24
  5. To yaya halinsu zai kasance idan Muka tara su a wani yini da babu shakka game da shi, kuma kowane rai za a saka masa da abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba? --Quran/3/25

Aya ta 26-27

  1. Ka ce: "Ya Allah, Kai ne Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Ka ga dama, kuma Kana kwace mulki daga wanda Ka ga dama, kuma Kana daukaka wanda Ka ga dama, kuma Kana kaskantar da wanda Ka ga dama; duk alheri yana hannun Ka, lalle Kai Mai iko ne a kan komai. --Quran/3/26
  2. "Kana shigar da dare a cikin yini, kuma Kana shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga cikin matacce, kuma Kana fitar da matacce daga cikin mai rai; kuma Kana arzurta wanda Ka ga dama ba tar da lissafi ba." --Quran/3/27

Aya ta 28

  1. Kada muminai su riki kafirai a matsayin masoya su kyale muminai; wanda kuwa duk ya aikata haka, to shi ba komai ne ba a wurin Allah, sai dai in don ku kare kanku ne daga gare su. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa. Kuma zuwa ga Allah makoma take. --Quran/3/28

A wannan aya, Allah ya hana muminai su riki kafirai masoyansu, watau majibinta al'amuransu, suna taimakon su, su yi watsi da 'yan'uwansu muminai. Allah ya bayyana cewa, duk wanda ya yi haka; to babu ruwan Allah da shi. Amma kuma sai Allah ya yi togaciyar lokacin da ake tsoron wani sharrin nasu, to a wannan lokaci za a iya nuna musu kauna da baki, ba da zuciya daya ba, ba kuma tare da taimakon su a kan kafircinsu ko taya su aikata sabon Allah ba.

Sannan Allah ya gargadi muminai game da kansa, watau kada su aikata abin da zai jawo musu fushinsa, yana mai bayyana musu cewa, makomarsu gaba daya zuwa gare shi ne, kuma zai yi musu hisabi a kan ayyukansu.

Daga wadannan ayar, za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Ba a shugabantar da wanda ba Musulmi ba a kan al'umma ta Musulmi.
  2. Ba ya halatta ga mumini ya kudurce kauna da soyayya ta addini ga wanda ba Musulmi ba. Amma kauna ta dabi'a, kamar irin ta d'a da mahaifi, ko miji da mata, wannan babu komai, matukar ba ta kai ga taimaka musu ba kan cutar da Musulmi ko fifita su a kan musulmai.
  3. 'Taqiyya' tana kasancewa ne tsakanin muminai da kafirai, ba a tsakanin musulmai ba, kamar yadda mabiya addinin Shi'a suka dauka.

Aya ta 29-30

  1. Ka ce: "In za ku boye abin da yake cikin kirazanku ko kuma ku bayyana shi, Allah Ya san shi, kuma Yana sane da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kasa. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai." --Quran/3/29
  2. Ranar da kowane rai zai sami sakamakon abin da ya aikata na alheri an halarto da shi, abin da kuwa ya aikata na mummunan aiki, zai so ina ma da a ce tsakaninsa da shi akwai wata tazara mai nisa. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa, kuma Allah Mai tausayi ne (ArRa'uf) ga bayi. --Quran/3/30

Allah SWT yana umartar Manzonsa da ya fada wa muminai cewa, ko da za su boye abin da yake cikin zukatansu na alheri ko na sharri, na soyayya ko na kiyayya, ko kuma su bayyana hakan a maganganunsu ko ayyukansu; to Allah ya san da hakan, kuma zai yi musu sakayya a kai; wanda ya shuka alheri ya girbi alheri; wanda kuma ya shuka sharri ya girbi sharri. Allah shi ne wanda iliminsa ya kewaye da duk abin da yake sama da abin da yake kasa, babu abin da yake boye masa, kuma yana da cikakken iko a kan komai, babu abin da zai gagare shi.

Sannan Allah ya bayyana lokacin wannan sakayyar, watau ranar alqiyama, ranar da kowane rai zai ga abin da ya aikata, kadan ne ko mai yawa, an kawo masa shi cikakke, ba tare da tawaya ba, ko wani canji. To amma abin da mutum ya aikata na sharri, zai rika burin ina ma akwai tazara mai nisa a tsakaninsa da mummunan aikinsa. Sai kuma Allah ya sake jaddada tsoratarwarsa da gargadinsa game da kansa, yana mai bayyana cewa, yana yi musu wannan gargadin ne saboda shi mai yawan rahama ne gare su, mai yawan jin kai.

Daga wadannan ayoyi, za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kira zuwa ga tsarkake zukata daga aikata zunubi da halrto da ilimin Allah a ko da yaushe, don bawa ya rika jin kunyar Ubangijinsa, wanda yake ganin ko'ina a zuciyarsa.
  2. Duk sa'adda mumini ya yi imani da sifar ilimi ta Ubangijinsa, wannan zai gadar masa abubuwa guda biyu:
    1. Zai guje wa sabon Allah, ba zai yarda Allah ya gan shi a wurin da ya hana shi ba.
    2. Zai yi kwadayin biyayya ga Allah, ba zai yarda Allah ya rasa shi a wurin da ya umarce shi ba.
  3. Tuna wa bawa ranar lahira da girman tsorace-tsoracenta, domin abin da bawa ya aikata sai an kawo masa shi a gabansa, an yi masa hisabi a kansa.
  4. Allah ya kirawo wa'azin da yake yi wa muminai a wannan ayar da suna 'gargadi', watau kashedi, domin ana gargadi ga wanda bai riga ya auka cikin hadari ba, domin a hana shi aukawa cikinsa.
  5. Allah ya rufe wannan gargadi nasa da fadarsa: "Allah mai jin kan bayi ne," domin yi wa mutum bayanin yadda lamari yake, yana daga cikin anu'i na tausaya masa.

Aya ta 31-32

  1. Ka ce: "In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin kai. --Quran/3/31
  2. Ka ce: "Ku yi da'a ga Allah da Manzo; to in kuwa kuka juya baya, to lalle Allah ba Ya son kafirai." --Quran/3/32

A wadannan ayoyi, Allah yana umarnin Annabinsa da ya fada wa masu da'awar son Allah da baki, amma ayyukansu suna karyata haka cewa, idan har da gaske suna son Allah, yo alamar da za ta tabbatar da gaskiyar da'awarsu ita ce su bi Manzon Allah, su gaskata shi, su yi masa da'a a kan abin da yake umarni da shi da abin da ya hana, domin son Allah da biyayya ga Manzon Allah abubuwa ne da suke hade ba sa rabuwa. To idan har wannan ya tabbata to a lokacin ne su ma Allah zai so su, kuma ya gafarta musu zunubansu, domin Allah mai gafarta zunubai ne, sai jin kai fa bayinsa.

Sai kuma Allah ya umarci Manzonsa da ya umarce su da su tabbatar da haka; watau su yi wa Allah da'a, kuma su yi wa Manzon Allah da'a; wannan kuwa shi zai fisshe su; idan kuwa har suka bijire wa wannan umarni, to su san da sanin cewa su kafirta, sun jefa kansu cikin fushin Allah, domin Allah ba ya son kafirai.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Dole ne mumini ya bi Manzon Allah cikin duk al'amuran rayuwarsa, tun daga aqida da shari'a da mu'amala, har zuwa dabi'u da halaye, a ayyukansa da maganganunsa.
  2. Son Allah ba kawai cika-baki ba ne ko burga; tsayawa ne qyam a kan sunnar Manzon Allah SAW da bin sa sau da kafa. Wanda ya yi haka kuwa shi ne masoyin Allah, kuma waliyyinsa na gaskiya; wanda kuma ya sab'a haka; to wannan ya tabbata maqaryaci, kuma waliyyin Shaidan.
  3. Wannan ayar tana karya lagon duk wani mai cika-baki da nuna soyayya ga Allah ko ga Manzon Allah bisa ga karya, domin wannan jarrabawa ce a gare shi, idan ya ci jarrabawa; to ya shiga tsarin masoya na gaskiya, idan kuwa ya fadi jarrabawar, to cika-bakinsa ba zai tsinana masa komai ba.
  4. Yin biyayya ga masoyi alama ce mai nuna gaskiyar soyayyarsa gare shi. Duk wanda ya so wani; to zai so abin da wannan masoyin nasa yake so.
  5. A cikin wadannan ayoyi akwai mayar da martani ga masu cewa, ba a aiki da sunna sai idan ta kunshi abin da Alkur'ani ya zo da shi. Wato idan ta kebanta da shar'anta wani hukunci; to ba za a karba ba. Wannan ayar ta tabbatar da yi wa Manzon Allah da'a tashi ta kansa, domin bayan ta yi umarni da da'ar Allah, sai kuma ta sake yin wani umarnin da da'ar Manzon Allah. Da a ce ba a yi masa da'a shi a karan-kansa, sai a cikin abin da ya zo a Alkur'ani, to da ya zamanto imarni da yi masa da'a a nan ba shi da wata fa'ida ke nan.
  6. Allah yana saka wa bawansa da sakamako fiye da aikinsa, don haka a nan ya saka wa mai son sa da soyayyarsa, sannan ya kara masa da gafarta masa zunubansa.

Aya ta 33-37

  1. Lalle Allah Ya zabi Adamu, da Nuhu da iyalan gidan Ibrahimu da iyalan gidan Imrana Ya fifita su a kan sauran talikai. --Quran/3/33
  2. Wata zurriya ce, sashinsu 'ya'ya ne ga sashi. Kuma Allah Mai ji ne, Mai yawan sani. --Quran/3/34
  3. Tuna lokacin da matar Imrana ta ce: "Ya Ubangijina, lalle ni na yi maka bakancen abin da yake cikina ya zamanto 'yantacce, don haka Ka karba daga gare ni, lalle Kai ne Mai ji, Mai yawan sani." --Quran/3/35
  4. To yayin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina, lalle ni na haife ta 'ya mace," kuma Allah ne Ya fi sanin abin da ta haifa "Kuma d'a namiji ba daidai yake da 'ya mace ba; kuma lalle ni na rad'a mata suna Maryamu, kuma lalle ni ina nema mata tsarinka da zurriyartta daga Shaidan korarre." --Quran/3/36
  5. Sai Ubangijinta Ya karbe ta da kyakkyawar karba, kuma Ya yi mata kyakkyawar tarbiyya, kuma Ya danka renonta a hannun Zakariyya; duk lokacin da Zakariyya ya shiga wurinta a dakin ibada, sai ya sami abinci a wurinta, sai ya ce: "Ya ke Maryamu, wannan daga ina kika samu?" Sai ta ce: "Wannan daga Allah ne; lalle Allah Yana azurta wanda Ya ga dama ba tare da lissafi ba." --Quran/3/37

A wadannan ayoyi, Allah yana bayanin irin zabin da ya yi a cikin bayinsa. Watau ya zabi wasu daidaikun mutane, ya kuma zabi wasu iyalai ya yi musu baiwa da falalarsa, ya fifita su a kan al'ummomin zamaninsu, ya ware su don bautar sa shi kadai. Cikin daidaikun mutane, Allah SWT ya zabi Annabi Adamu da Nuhu; a cikin gidaje ko iyali, kuma Allah ya zabi Annabi Ibrahim da iyalinsa da Imrana da iyalinsa. Wadannan zababbu Allah ya sanya nagarta da ayyukan kwarai a cikin zuriyyarsu. Allah shi ne mai cikakken ilimi game da wanda ya cancanci zabinsa a cikin bayinsa, domin shi ne mai ji, kuma mai cikakken sani.

Sannan Allah ya ci gaba da labarin wasu qissoshi guda hudu, masu ban mamaki wanda ya saba da yadda dan'adam ya saba gani.

Allah ya fara da kissar Maryam, mahaifiyar Annabi Isa, yadda ta kasance kebantacciya ga Allah tun lokacin da mahaifiyarta ta dauki cikinta har ta haife ta, ta dimanci zama a wurin bautar Allah. Lokacin da mahaifiyarta ta dauki cikinta, ta yi wa Allah bakance cewa, abin da yake cikinta, za tta sadukar da shi ga Allah don yi masa hidima a masallacin Baitul Maqdis. Ta roki Allah ya karbi wannan bakance nata, domin shi mai jin addu'ar wanda ya roke shi ne, ya karba masa, kuma masani ne ga halin da kowane bawa yake ciki. To tana zaton abin da za ta haifa namiji ne; amma tana haihuwa, sai ta ga mace, sai take neman uzuri a wurin Allah, tana mai cewa, ga shi abin da ta haifa ya zamanto mace, ba namiji ba; mace kuma ba za ta iya yin abin da namiji zai iya ba na hidima da lazimtar wurin ibada a ko da yaushe, saboda raunin da take da shi da kuma larurar da take samun ta a duk wata, watau jinin al'ada. Sannan sai ta sanya wa 'yar tata suna Maryam, ta kuma roki Allah da ya tsare ta har da zuriyar da za ta haifa nan gaba, daga sharrin Shaidan la'ananne.

An karbo daga Abu Huraira:
Abu Huraira reported Allah's Messenger (ﷺ) as saying:
Abu Huraira said,

Babu wani jariri da aka haifa, face sai da Shaidan ya shafe shi lokacin haihuwarsa,
No child is born but he is pricked by the satan
There is none born among the off-spring of Adam, but Satan touches it.

sai ku ji yaro ya fashe da kuka saboda shafar Shaidan, in ban da Maryam da danta (Annabi Isa).
and he begins to weep because of the pricking of the satan except the son of Mary and his mother.
A child therefore, cries loudly at the time of birth because of the touch of Satan, except Mary and her child.

Sai Abu Huraira ya ce: In kun ga dama ku karanta fadar Allah: Lalle ni ina nema mata tsari da zurriyarta daga Shaidan korarre.
Abu Huraira then said: You may recite if you so like (the verse):" I seek Thy protection for her and her offspring against satan the accursed" (iii. 36). [13]
Then Abu Huraira recited: "And I seek refuge with You for her and for her offspring from the outcast Satan" (3.36) [14]

Sai Allah ya karbi addu'arta, kuma ya karbi wannan bakancen da ta yi, kyakkyawar karba, ya taso da Maryamu cikin kyakkyawar tarbiyya, mai ban sha'awa ga kowa, kuma Allah ya dora nauyin kula da ziyara wajen ibadarta, sai kawai ya tarar da abinci iri-iri a wurinta, sai abin ya rika ba shi mamaki, sai yake tambayar ta cewa: "Daga wurin Allah ne, kuma shi Allah yana ba da arzikinsa ne ga wanda ya ga dama, ba tare da lissafi ba."

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Allah yana zaben wasu daga cikin bayinsa, ya yi musu falala ta musamman, don su zama abin koyi cikin ayyukansu da maganganunsu da halayensu.
  2. Dan Adam ba zai taba zama mai 'yanci ba, har sai ya 'yanta kansa daga bautar wani ba Allah ba, ya 'yanta kansa daga bin koyarwar da ta saba da ta Allah, ya rungumi tsarin Allah gaba daya a cikin dukkan al'amuran rayuwarsa.
  3. Mutum ya riƙa neman ko da yaushe Allah ya karɓi aikinsa na ƙwarai, kada ya riƙa ruɗuwa da ayyukansa masu kyau, domin babban abin buƙata shi ne Allah ya karɓa daga gare shi.
  4. Yana da kyau iyaye su rika yi wa 'ya'yansu addu'a tun suna ciki da bayan haihuwarsu, su roƙa musu albarkar Ubangiji, su nema musu tsarinsa daga sharrin Shaitan.
  5. Abin da Allah ya yi wa mahaifiyar Annabi Isa (alaihissalaam), na ba ta abinci da abin sha, ba tare da to fita nema ba, karama ce da Allah ya gudanar a kanta, domin amsa addu'ar mahaifiyarta da kuma ya zama shimfida ga abi da Allah yake niyyar zartar da shi haihuwar Annabi Isa ba tare da namiji ba.
  6. Ba ya halatta wani ya kafa hujja da abin da ya faru ga Maryam, ya zauna a masallaci ba ya fita neman abinci, yana jiran a kawo masa sadaka da sunan yana bauta wa Allah.
  7. Allah SWT ya tabbatar da bambanci tsakanin ɗa namiji da mace da faɗar mahaifiyar Maryam: "Kuma ɗa namiji ba daidai yake da 'ya mace ba." Namiji da mace sun bambanta a ginin halittarsu da ɗabi'arsu da halayensu da mu'amalarsu, har ma da hukunce-hukuncensu a wasu lokuta.
  8. Idan har za ba wani riƙon yaro, to wajibi ne a danƙa shi ga wanda zai yi masa tarbiyya ta ƙwarai, domin ya taso cikin kamala da nagarta.
  9. Yana daga cikin rukunan godiya ga Allah bisa ni'imarsa, bawa ya yi iƙirari da cewa, wannan ni'imar da ya samu daga Allah take, ba yin kansa ba ne.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 38-41

  1. A wannan lokacin sai Zakariyya ya roƙi Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangijina, Ka ba ni zurriyya ta gari daga gare Ka, lalle Kai Mai amsa roƙo ne." --Quran/3/38
  2. Sai mala'iku suka kira shi, lokacin yana tsaye yana salla a cikin ɗakin ibada, (suka ce): "Lalle Allah Yana yi maka albishir da Yahaya, wanda yake mai gaskatawa da wata kalma daga Allah, kuma zai zama shugaba, kuma mai tsare kansa daga mata, kuma Annabi daga cikin salihan bayi." --Quran/3/39
  3. Ya ce: "Ya Ubangiji, ta yaya zan sami ɗa, ga shi tsufa ya riga ya cim mini, kuma ga shi matata juya ce?" Sai ya ce: "Kamar haka ne Allah Yake aikata abin da Ya ga dama." --Quran/3/40
  4. Ya ce: "Ya Ubangiji, Ka sanya mini wata alama." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana yini uku sai dai da nuni. Kuma ka ambaci Ubangijinka ambato mai yawa, kuma ka yi tasbihi yammaci da safiya." --Quran/3/41

Sai kuma a nan Allah ya kawo ƙissa ta biyu, watau ƙissar Annabi Zakariyya, da yadda ya yi masa kyaytar ɗa bayan har ya tsufa, ba tare da haihuwa ba, kuma ga shi matarsa bakarara, ba ta haihuwa.

Lokacin da Annabi Zakariyya ya ga irin karama da baiwar da Allah ya yi wa Maryam sai shi ma ya ji son haihuwa ya dawo masa, ya sa rai ga samun biyan buƙatarsa, duk kuwa da halin da yake ciki na manyanta shi da matarsa. Sai ya ɗaga hannu ya yi addu'a yana cewa: "Ya Ubangijina, ka ba ni zurriyya ta gari daga gare ka, lalle kai mai amsa roƙo ne." Sai ko Allah ya amsa masa addu'arsa, ya aiko wasu mala'iku don su yi masa albishir, suka same shi yana tsaye a masallaci yana salla, suka yi masa wannan albishir da cewa, zai haifi ɗa mai suna Yahya, wanda zai siffantu da siffofi masu girma, domin zai zama Shugaba wanda zai shugabanci mutanensa da halayensa na ƙwarai da iliminsa da addininsa, kuma mai ƙaurace wa mata da duk wani abu da zai tayar masa da sha'awa, mai shagala da bautar Allah, sannan kuma zai zama Annabi daga cikin salihan bayi.

Yayin da Annabi Zakariyya ya ji wanna albishir na samun haihuwa, sai mamakin Ƙudurar Allah ya rufe shi, sai yake tambayar Allah, yana cewa: "Ya Ubangijina, ta yaya zan sami ɗa, alhalin ga shi ni na tsufa, na kai shekarun da ba zan iya haihuwa ba, sannan kuma ga matata bakarara ce da ma can ba mai haihuwa ba ce?" Sai Allah ya amsa masa da cewa, alamar da zai gani ita ce, zai kasa magana da kowa har tsawon kwana uku, ba kuma don rashin lafiya, ko wani abu ya sami harshensa ba. Idan zai yi magana da mutane, sai dai ya riƙa nuni da hannunsa, amma kuma zai iya furta ambaton Allah a lokacin. Don haka Allah ya umarce shi da ya yi ta ambaton Unangijinsa tare da tsarkake shi ta hanyar tasbihi da bautarsa yammaci da safiya.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Duk halittun Allah, har ma da annabawa, masu buƙata ne a wurin Allah, don haka shi kaɗai suke roƙa ya biya musu buƙatunsu.
  2. Idan mutum zai roƙi Allah haihuwa; to ya roƙe shi zurriya ta gari, domin ɗa na gari shi ne zai amfani mahaifansa duniya da lahira.
  3. Yana da kyau idan mutum yana son biyan wata buƙata a wurin Allah; to ya yi riƙo da sabubban wannan bukata, daga cikinsu akwai addu'a.
  4. Yana da kyau mutum ya nemi abin da zai ƙara masa imani.
  5. Yana da kyau idan mutum ya keɓanta, ya bar jama'a; to ya shagalta da yawan ambaton Allah da bautarsa.
  6. Yi wa mutum albishir da samun wani alheri, kamar haihuwa.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 42-44

  1. Kuma ka tuna lokacin da mala'iku suka ce: "Ya ke Maryamu, lalle Allah Ya zaɓe ki, Ya kuma tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan sauran mata na talikai. --Quran/3/42
  2. "Ya ke Maryamu, ki yi ɗa'a ga Ubangijinki, kuma ki rika yin sujada, kuma ki rika yin ruku'u tare da masu ruku'u. --Quran/3/43
  3. Wancan (abin da ya gabata a baya) yana cikin labaru na gaibi da Muke yi maka wahayinsa, kuma kai ba ka wurinsu lokacin da suka jefa alkalumansu don tantance wane ne cikinsu zai karbi renon Maryam, kuma kai ba ka nan tare da su yayin da suke jayayya da juna. --Quran/3/44

A wadannan ayoyi Allah yana shimfida ne game da ƙissa ta uku, wato ta Maryamu da ta haifi Annabi Isa ba tare da namiji ba. Allah ya yi shimfida da bayanin zabin da ya yi wa Maryam don ta zama ita ce wadda Allah zai gudanar da wannan al'amari nasa da ya saɓa wa al'adar da dan'adam ya saba gani, na halittar mutum daga haduwar ɗa namiji da 'ya mace. Allah ya ba wa Annabinsa labarin Maryam lokacin da mala'iku suka kirawo ta, suna faɗa mata cewa, Allah ya zaɓe ta a cikin duka matan zamaninta, ya fifita ta a kansu, ya tsarkake ta da kyawawan halaye da riko da addini. Wannan zabin da aka yi mata, ba karamar ni'ima ce gare ta ba, saboda haka akwai bukatar tayi wa Allah godiya a kai, ta tsarkake da'arta ga Allah, ta zama mai bauta masa a ko da yaushe, kuma ta dinga yin salla tare da masallata.

Allah ya bayyana wa Manzonsa cewa, wadannan labarai da yake ba shi, na gaibu, wadanda shi da mutanensa ba wanda ya san su, amma ga shi yanzu Allah ya sanar da shi su, don tabbatar da shaida da dalili a kan gaskiyar annabcinsa, da ingancin wahayin da ya zo musu da shi. Allah ya ci gaba da faɗa wa Annabi cewa, ba ya wurin lokacin da Annabi Zakariyya da sauran dangin Maryam suka yi taro, suka tattauna batun wanda zai kula da rainonta, har ta kai su ga samun sabani a tsakaninsu game da batun, har sai da aka yi ƙuri'a sannan aka zabi wanda zai rike ta, watau Annabi Zakariyya. Allah ya gaya wa Annabinsa cewa wannan gaibu ne ya yi masa wahayinsa; Allah kuwa shi ne ya kebanta da sanin gaibu yake kuma sanar da wanda ya ga damar sanar da shi.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Falalar Maryam da fifikonta a kan sauran mata.
  2. Allah ya ba da labarin tsarkinta don mayar da martani ga Yahudawa masu tuhumar ta game da haihuwar Annabi Isa.
  3. Idan Allah ya yi wa bawansa wata ni'ima; to yana daga cikin godiya ga Allah bawan ya yawaita ibada.
  4. Annabi bai san gaibu ba, sai abin da Allah ya sanar da shi ta hanyar wahayi.
  5. Annabi ya sami labarin Maryam (AHS) daki-daki kamar haka, tare da cewa, shi ba mai karatu da rubutu ne ba, wani babban dalili ne da yake tabbatar da gaskiyar annabcinsa.
  6. Halaccin yin ƙuri'a yayin da aka kasa warware wani sabani.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 45-51

  1. Ka tuna lokacin da mala'iku suka ce: "Ya ke Maryamu, lalle Allah Yana yi miki albishir da wata kalma daga gare shi, sunansa Almasihu Isa dan Maryam, mai daraja a duniya da lahira, kuma yana cikin bayi makusanta. --Quran/3/45
  2. "kuma zai riƙa yi wa mutane magana tun yana cikin shimfidar jego da kuma lokacin dattijantaka, kuma yana cikin salihan bayi." --Quran/3/46
  3. Sai ta ce: "Ya Ubangiji, ta yaya zan sami ɗa alhalin wani namiji bai kusance ni ba?" Sai ya ce: "Kamar haka ne Allah Yake halittar abin da Ya ga dama. Idan Ya yi nufin wani al'amari, sai Ya ce da shi: "Kasance" Nan take sai ya kasance. --Quran/3/47
  4. "Kuma zai sanar da shi rubutu da hikima da Attaura da Linjila. --Quran/3/48
  5. "Kuma zai aiko shi a matsayin Manzo ga Banu Isra'ila (yana mai cewa): "Lalle ni na zo muku da wata aya daga Ubangijinku; lalle ni zan riƙa mulmula muku taɓo a siffar tsuntsu, sai in yi busa a cikinsa sai ya zama tsuntsu da izinin Allah; kuma zan warkar da wanda aka haifa makaho da mai cutar albaras, kuma in rayar da matattu da izinin Allah; kuma zan riƙa ba ku labarin abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a gidajenku. Lalle a cikin hakan akwai aya a gare ku in har kun kasance muminai. --Quran/3/50
  6. "Kuma zan zama mai gaskata abin da ya gabace ni na Attaura, kuma don in halatta muku sashin abubuwan da aka haramta muku. Kuma na zo muku da wata aya daga Ubangijinku, don haka ku tsoraci Allah, kuma ku yi mini biyayya. --Quran/3/51

A wadannan ayoyi, Allah ya ci gaba da ba wa Annabinsa labarin Maryam, da haihuwar Annabi Isa. Wannan shi ne na uku cikin ƙissoshi hudu masu tattare da abubuwan mamaki. Allah ya fara da mala'ikun da suka zo ga Maryam, suna yi mata albishir na za ta haifi yaro, wanda Allah zai halicce shi da kalmarsa, wato kalmar (kun), 'kasance', sai ya kasance, sunansa Almasihu Isa dan Maryam, Ana jingina shi ga mahaifiyarsa ne domin ba shi da uba. Yaro wanda daga siffofinsa zai zamo mai daraja ne da matsayi a wurin Allah, duniya da lahira, kuma yana cikin makusantan Allah. Daga cikin mu'ujizojinsa kuma, zai riƙa magana da mutane tun yana jariri cikin zanin haihuwarsa, don ya wanke mahaifiyarsa daga zargin ta haihu ba tare da mijin aure ba, kuma ya yi kira zuwa ga bautar Allah shi kadai, ba tare da hada shi da wani abokin tarayya ba. Bayan ya zama dattijo kuma, zai ci gaba da yi wa mutane magana irin ta annabawan Allah masu karantar da jama'arsu abin da Allah ya yi masa wahayi da shi, sannan yana cikin mutanen kirki.

Sai Maryam ta amsa da cewa, ta yaya za ta haifi ɗa, alhali ba wani namiji da ya taɓa kusantar ta ta hanyar aure, ko ta hanyar zina? Sai Allah ya mayar mata da amsa cewa, haka dai Allah zai zartar da wannan al'amari da take mamaki, domin da haka Allah yake halittar abin da ya ga damar halitta, kuma babu abin da yake gagarar sa aikatawa, duk sa'adda ya yi nufin samar da wani abu, sai ya ce masa, 'kasance', sai nan take abin ya samu, ba tare da ɓata lokaci ba.

Sannan Allah ya ci gaba da bayanin irin baiwar da ya yi wa Annabi Isa a rayuwarsa ta ilimi da hikimomi iri-iri masu ban musamman bayan girmansa, wadda ita ma take cike da abubuwan ban mamaki, wadanda har ma suka fi haihuwarsa ba tare da uba ba zama abin mamaki. Allah ya ce, ya yi masa baiwar koya masa rubutu da hikima, wadda ta kunshi shari'o'i da siyasar tafiyar da jama'a, ya kuma ba shi ilimin Attaura da Linjila, sannan ya aiko shi zuwa ga al'ummar Banu Isra'ila, yana mai fada musu cewa:

"Lalle na zo muku da wasu hujjoji daga Ubangijinku, wadanda suke tabbatar da gaskiyar abin da nake fada muku cewa ni Manzon Allah ne zuwa gare ku. Hujjojin kuwa su ne, Allah Ya hore mini wasu mu'ujizoji, daga cikin ina iya gina surar mutun-mutumi na tsuntsu da taɓo, sannan in yi busa cikinsa, nan take ya zama tsuntsu mai tashi da izinin Allah, kuma in warkar da mutumin da aka haife shi makaho da mai cutar baras, sannan in tayar da matattu, duk dai da izinin Allah. Bugu da kari kuma zan iya ba ku labarin irin abincin da kuka ci a gidajenku, da abin da kuke ajiyewa, ba tare da na gani da idona ko wani ya ba ni labari ba. Duk wadannan hujjoji ne a gare ku wadanda suke tabbatar muku gaskiyar abin da na fada muku na labarin manzancina gare ku, in har kun kasance masu imani. Sannan kuma ina mai gaskata littafin Attaura da aka saukar a gabanina da kuma Linjila da aka saukar mini. Kuma na zo don in halatta muku wasu abubuwa da aka haramta muku. Na kuma zo muku da wata aya daga Ubangijina, wadda take nuna gaskiyata, don haka ku kiyaye dokokin Allah, ku bi ni a kan abin da nake kiran ku zuwa gare shi. Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, don haka ku bauta masa shi kdai; wannan ita ce hanyar Allah miƙaƙƙiya, wadda za ta kai ku ga samun yardar Allah."

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Alamar mai gaskiya ita ce maganganunsa da ayuukansa su rika yin daidai da na mutane masu gaskiya, kada su rika sabawa da nasu ko da yaushe.
  2. Yana daga cikin hikimar Allah wajen bayar da labarin abubuwan mamaki, ya fara da mafi kankantar abin mamaki, sannan wanda ya ɗara shi, sannan wanda yake gaba da shi, sannan wanda yake gaba da shi, har a zo ga na ƙoli. Kamar a nan an fara da ƙissar Maryam, da dangogin abinci da Zakariyya ya rika samu a wurinta, sai kuma labarinsa na samun haihuwa bayan ya manyanta sosai, ga kuma matarsa bakarara, marar haihuwa, sai labarin haihuwar Annabi Isa ba tare da uba ba, sai kuma aka kawo zancen mu'ujizojo daban-daban, kamar raya matattu da Annabi Isa ya riƙa yi da izinin Allah, da sauransu.
  3. An keɓe zancen maganar da Annabi Isa ya yi wa mutane a lokacin da yake jariri, da kuma lokacin da ya zama dattijo. Lokacin da yake jariri, wannan abu ne da ya saɓa wa al'adar da aka saba gani, kuma alama ce ta annabcinsa. Lokacin da ya zama dattijo kuwa, ana nufin lokacin da yake kiran mutane zuwa ga bautar Allah da bin shari'arsa.
  4. Akwai mayar da martani ga Nasara masu cewa, Isa AS Allah ne, domin da Allah ne da ba zai riƙa canjawa daga yarinta zuwa dattaku ba, domin Allah ba ya caccanzawa.
  5. A shari'o'in annabawan da suka gabata ma an samu tsarin shafe wani hukunci a zo da wani sabo, kamar yadda Annabi Isa ya shafe wasu hukunce-hukuncen Attaura.
  6. Bayani a kan zamantowar Annabi Isa bawa ne na Allah, ba ɗan Allah ba, kuma ba Allah ne ba.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 52-58

  1. To yayin da Isa ya ga alamun kafirci a tare da su, sai ya ce: "Su wane ne za su taimake ni wajen kira zuwa ga Allah?" Sai Hawariyawa suka ce: "Mu ne mataimaka addinin Allah, mun yi imani da Allah, kuma ka ba da shaida cewa, mu Musulmai ne." --Quran/3/52
  2. "Ya Ubangijinmu, mun yi imani da abin da Ka saukar, kuma mun yi ɗa'a ga Manzo, don haka Ka rubuta mu tare da masu shaida." --Quran/3/53
  3. Sai suka shirya makirci, sai Allah Ya mayar musu da martani game da makircinsu; kuma Allah Shi ne Fiyayyen masu mayar da martanin makirci. --Quran/3/54
  4. Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya ce: "Ya kai Isa, lalle Ni Mai karɓar ranka ne, kuma Ni Mai ɗaukaka ka ne zuwa gare Ni, kuma zan tsarkake ka daga (cutarwar) waɗanda suka kafirta, kuma zan ɗora wadanda suka bi ka a kan wadanda suka kafirce maka har zuwa ranar tashin alkiyama; sannan zuwa gare Ni ne makomarku take, sai In yi hukunci a tsakaninku game da abin da kuke saɓani a kansa. --Quran/3/55
  5. Amma wadanda suka kafirce, zan yi musu azaba mai tsanani a duniya da lahira, kuma ba su da wasu mataimaka." --Quran/3/56
  6. Amma kuma wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na gari, to (Allah) zai cika musu ladansu. Kuma Allah ba Ya son azzalumai. --Quran/3/57
  7. "Wannan labari Muna karanta maka shi ne daga ayoyi da kuma Alkur'ani mai hikima." --Quran/3/58

A wadannan ayoyi Allah ya ci gaba da ba mu labarin cewa lokacin da Annabi Isa ya ga alamar bijirewa da kafircewa daga Banu Isra'ila da ƙaryata annabcinsa, sai ya nemi taimako daga zababbu cikin almajiransa, yana mai kiran su da cewa, wane ne zai taimaka masa a kan wannan kira da yake yi zuwa ga addinin Allah? Sai suka amsa da cewa, su za su zama masu taimakon addinin Allah, sannan suka shelanta imaninsu a fili, kuma suka kafa shi shaida a kan Musuluncinsu, suka kuma roƙi Ubangijinsu, suna masu kamun ƙafa da imaninsu da littafin Linjila da ya saukar ga Annabi Isa da kuma biyayyarsu gare shi da cewa, Allah ya rubuta su cikin wadanda suka ba da gaskiya da Kadaitakar Allah da gaskiyar manzannin Allah, kuma suka bi umarninsa, suka kauce wa abin da ya hana.

An karbo daga Abdullah dan Mas'ud ya ce: Manzon Allah ya ce:

"Babu wani annabi gabanina da Allah ya aiko shi cikin wata al'ummarsa sai ya kasance a cikin al'ummar tasa yana da hawariyawa da sahabbai wadanda suke riko da sunnarsa suke kuma koyi da umarninsa..." [Muslim #50]

Never a Prophet had been sent before me by Allah towards his nation who had not among his people (his) disciples and companions who followed his ways and obeyed his command... [15]

Allah kuma sai ya ba da labarin irin makircin da Banu Isra'ila suka ƙulla ga Annabi Isa, na ƙoƙaron hallaka shi. Su suna ƙulla makircinsu, Allah kuma yana shirya musu martani a kan mafi ƙarfi, mafi sani. Don haka sai Allah ya jefa kamannin Annabi Isa a kan daya daga cikinsu, sai suka kama shi suka kashe shi, suna zaton Annabi Isa ne suka kashe. Shi kuma Allah ya jefa masa barci, sannan ya dauke shi zuwa sama. Allah ya fada game da Annabi Isa cewa, zai karbi ransa irin karbar ran mai barci, yana Sannan zai daukaka shi zuwa gare shi da gangar jikinsa da kuma ruhinsa, sannan zai kubutar da shi daga wadanda suka kafirta, ya fitar da shi, ya daga shi zuwa sama, sannan zai sanya mabiyansa su zama su ne masu rinjaye a kan kafirai da karfin hujja da izza da daukaka har zuwa tashin alkiyama. Wadannan mabiyan nasa da Allah yake yi wa wannan alkawari, su ne Nasara, wadanda suka tsaya daidai a kan koyarwarsa har zuwa lokacin aiko Annabi Muhammad, sai kuma Musulmi wadanda su ne mabiya na gaskiya ga Annabi Isa, wadanda Allah ya karfafe su, ya ba su nasara a kan Yahudawa da Nasara da sauran kafirai.

Sai kuma Allah ya fada wa masu sabani cikin lamarin Annabi Isa cewa, dukkansu makomarsu zuwa gare shi take, kuma zai yi hukunci a tsakaninsu game da wannan sabani da suke yi. Hukuncinsa kuwa shi ne, zai yi musu azaba mai tsanani a nan duniya, ta hanyar kisa da dauri da kaskanci da wulakanci da raba su da dukiyoyinsu da kuncin zukata da za su yi ta fama da shi, sannan kuma a lahira su gamu da azabar Jahannama, a lokacin da babu wanda zai taimaka musu, ya kare su daga azabar Allah. Su kuma wadanda suka yi imani, kuma suka yi aiki na kwarai, hukuncinsa a kansu shi ne, zai cika musu ladansu babu ragi ko tawaya a duniya da lahira. A nan duniya ta hanyar ba su nasara kan abokan gabarsu, da izza da rayuwa mai kyau da kyakkyawan ambato da sauransu, a lahira kuwa ya saka musu da gidan Aljanna cikin ni'ima ta har abada. Kuma Allah ba ya son azzalumai, don haka shi kansa babu yadda za a yi ya yi zalunci cikin hukuncinsa.

Sannan Allah ya ce da Annabinsa wadannan labarai da yake ba shi na Annabi Isa da mahaifiyarsa Maryam da sauran kissoshi da aka ambata an karanta masa su ne don su zama hujjoji masu nuna gaskiyarsa da gaskiyar annabinsa, sannan kuma suna daga cikin kissoshin Alkur'ani ne, mai cike da hikimomi, kuma mai yanke hukunci.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Yawan dalilai da karfinsu da yawan mu'ujizoji da bayyanarsu, ba su ne suke sa mutane su karbi gaskiya ba; sai an samu gamon katari daga Allah. Dubi yawan ayoyi da Allah ya gudanar a hannun Annabi Isa, amma wannan bai hana wasu su ci gaba da kafirce masa ba.
  2. Yana daga cikin sunnar annabawa da manzanni, su nemi wadanda za su tallafa wa da'awarsu.
  3. Yana da kyau ga mai da'awa, idan al'amura suka rikice masa, ya nemi taimakon zababbu daga cikin mabiyansa su taimaka masa.
  4. Duk wani mai kira zuwa ga wata manufa ko wata aqida; to dole ne ya kasance yana tare da wasu mataimaka wadanda za su rika tallafa masa wajen da'awarsa.
  5. Duk mai son cin nasara a cikin wani aiki; to dole ne ya yi riko da sababin samun wannan nasarar.
  6. Cin nasara ba yana nufin sai an fafata fada a filin daga ba, addini shi ma nasara ce.
  7. Faɗar Hawariyawa cewa: "Mu ne mataimaka addinin Allah." yana nufin sun yi watsi da duk wata gargajiya da al'ada tasu marar kyau, sun rike addinin Allah shi kadai, don haka yanzu a shirye suke su bayar da iya taimakonsu don samun cin nasarar wannan addini.
  8. Yana da kyau ko da yaushe a rika tuna wa mutane labarin annabawa da manzanni da salihai da suka gabata, domin su san kokarinsu, su so su, su yi musu addu'a, kuma su yi koyi da rayuwarsu.
  9. A cikin wadannan ayoyi Allah ya tabbatar da aqidar dauke Annabi Isa zuwa sama.
  10. Musulunci shi ne addinin annabawa da mabiyansu gaba daya.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 59-63

  1. Lalle misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne; Ya halicce shi daga turɓaya, sannan Ya ce da shi: "Kasance." nan take sai ya kasance. --Quran/3/59
  2. Gaskiya ce daga wajen Ubangijinka, don haka kar ka kasance cikin masu yin kokwanto. --Quran/3/60
  3. To duk wanda ya yi jayayya da kai cikin lamarinsa (Isa) bayan abin da ya zo maka na ilimi, to ka ce: "Ku zo mu kirawo 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matanmu da matanku da mu kanmu da ku kanku, sannan mu ƙasƙantar da kawunanmu cikin addu'a don mu roƙi tsinuwar Allah ta tabbata a kan maƙaryata." --Quran/3/61
  4. Lalle wannan shi ne ba da labari na gaskiya. Kuma babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Kuma lalle Allah Shi ne Mabuwayi, Mai hikima. --Quran/3/62
  5. To idan sun ba da baya, to lalle Allah Yana sane da maɓarnata. --Quran/3/63

A wadannan ayoyi, Allah yana tsayar da hujja a kan Nasara wadanda suke bautar Annabi Isa da sunan shi Allah ne, ko kuma ɗan Allah ne, saboda an same shi ba uba. Allah yana kwatanta musu ba uwa ba uba, Allah ya halicce shi kawai da ƙasa, ya ce masa, 'kasance', sai ya kasance kamar yadda Allah ya yi nifinsa duka abu ɗaya ne a wurin Allah. To idan har suna ganin samuwar Annabi Isa ba uba dalili ne da zai sa su riƙe shi Allah, ko ɗan Allah; to me ya sa ba su yi haka ga Annabi Adamu ba, alhali ga shi samuwarsa ta fi ta Annabi Isa ban al'ajabi?

Sannan Allah ya shaida wa Annabinsa cewa, wannan labarin da ya ba shi na Annabi Isa gaskiya ce daga Ubangijinsa, don haka kada ya zama cikin masu shakka. Hasali ma idan har wani ya zo yana jayayya da shi cikin lamarin Annabi Isa, bayan abin da ya zo masa na ilimi da gamsasshen bayani a kan wannan batu; to ya faɗa wa masu jayayya da shi cewa, shi da su gaba daya, su fito da 'ya'yansu, da matansu, da su kansu, sai a taru a yi addu'a, Allah ya la'anci makaryaci a tsakaninsu. Sa'ad ɗan Abu Waqqas yana cewa:

"Lokacin da wannan ayar ta sauka, Manzon Allah ya kirawo Aliyyu da Fatima da Hassan da Hussaini, ya ce: "Ya Allah, wadannan iyalaina ne." [Muslim #2404]

when the (following) verse was revealed: "Let us summon our children and your children." Allah's Messenger (ﷺ) called 'Ali, Fatima, Hasan and Husain and said: O Allah, they are my family. [16]

An karbo daga Huzaifa ya ce:

"Wasu mutane su biyu daga mutanen Najarna ɗaya ana ce masa Al-Aqibu, ɗayan kuwa Assayyidu, sun zo ga Annabi suna so su yi tsinuwa tsakaninsa da su (game da sha'anin Annabi Isa),

that Al-'Aqib and As-Sayyid (two of the leaders of the Christians of Najran) came to the Prophet (ﷺ) [17]...

sai ɗayansu ya ce wa ɗan'uwansa: 'Kada ka yi wannan aikin, Wallahi idan ya zamanto Annabi ne da gaske, sannan muka yi tsinuwa tsakaninmu da shi; to da mu da zurriyyarmu ba za mu rabauta ba har abada.' Daga nan sai suka fasa, suka nemi sulhu da Annabi a kan za su ba shi duk abin da ya nema daga gare su na dukiyar sulhu." --Bukhari #4350 & Muslim #2420

Sannan Allah ya ƙara jaddada wa Annabinsa cewa, wannan labari da yake ba shi na Annabi Isa shi ne labarin gaskiya, duk wani labari da ya ci karo da shi, to ba gaskiya ba ne, shi kadai, Mabuwayi da ya gagari kowa da komai, Mai hikima cikin duk ayyukansa.

To idan wadannan sun bijire wa gaskiya, sun riki karya; to sun tabbata mabarnata, Allah kuwa yana sane da su, kuma zai yi musu sakayya a kan ayyukansu.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Halaccin yin mubahala, wato addu'ar tsinuwa tsakanin mai kira zuwa ga gaskiya da masu faɗa da ita, da sharadin ya kasance yana da yaqini a kan abin da zai yi mubahalar a kansa, kuma muhimmin abu ne mai girma, sannan ya zamana ya isar da hujjojinsa ga abokin husuma ya fahimce amma ya yi girman kai.
  2. Duk wanda zai juya wa addinin Allah baya; to wannan mutum mabarnaci ne, ko da kuwa ya kirawo kansa mai gyara.
  3. Halaccin yin la'ana ga duk wanda ya saɓa wa gaskiya, amma ta fuskar aikinsa, ba ta ambaton sunan wani ba.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 64-68

  1. Ka ce: "Ya ku Ma'abota Littafi, ku taho ga wata kalma mai daidaitawa tsakaninmu da ku cewa, kar mu bauta wa kowa sai Allah, kuma kar mu haɗa Shi da wani, kuma kada wani sashi a cikinmu ya riƙi wani sashi a matsayin abin bauta ba Allah ba." Idan kuwa sun ba da baya, to ku ce: "Ku shaida cewa, lalle mu Musulmi ne." --Quran/3/64
  2. Ya ku Ma'abota Littafi, don me kuke yin jayayya game da Ibrahim, alhalin ba a saukar da Attaura da Linjila ba sai bayan shuɗewarsa? Yanzu ba za ku hankalta ba? --Quran/3/65
  3. Ga ku nan ku wadannan kun yi jayayya kan abin da kuke da ilimi a kai, to don me kuma kuke jayayya a kan abin da ba ku da ilimi a kansa? Kuma Allah Yana sane ku ba ku sani ba. --Quran/3/66
  4. Ibrahim bai taɓa zama Bayahude ba, sannan bai taɓa zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin ɓarna ne, Musulmi, kuma bai kasance ɗaya daga cikin mushrikai ba. --Quran/3/67
  5. Lalle mafi kusancin mutane da Ibrahim su ne wadanda suka bi shi, sai kuma wannan Annabin, da kuma wadanda suka yi Imani. Kuma Allah shi ne Majiɓincin al'amuran muminai. --Quran/3/68

Bayan an kira Ma'abota Littafi zuwa ga addu'ar tsinuwa amma sun ƙi yarda, sannan an kawo musu hujjoji iri-iri wadanda suka nuna bacin addinin da suke kai, sun kuma kasa kare ɓatansu, kuma Allah ya riga ya san yadda Annabi yake maukar tausayin su, yana kwadayin shiriyarsu, sai Allah ya umarce shi da ya kirawo su gaba daya zuwa ga kalma ta bai-ɗaya, wadda kowa da kowa zai daidaita a kanta, kuma za su hada kai a kanta. Wannan kalma ita ce kadaita Allah da bauta, watau kada a bauta wa wani ba shi ba, mala'ika ne, ko wani annabi, ko waliyyi, ko wani gunki. Kada kuma su dauki wasu iayen giji, suna bauta musu ba Allah ba, har su riƙa halatta musu haram ko su haramta musu halal su kuma yarda. To idan sun bijire, sun ƙi yarda da wannan kiran; to ku muminai ku kafa su shaida cewa, ku Musulmi ne, kuma za ku ci gaba da bin wannan addinin da Allah ya zaɓa muku.

Sannan Allah ya fuskantar da maganarsa ga Yahudawa da Nasara cewa, don mene ne suke jayayya game da lamarin Annabi Ibrahim; kowanne yana da'awar cewa a kan addininsa yake, Yahudawa suna cewa shi Bayahude ne, Nasara ma suna cewa shi Banasare ne, alhalin yadda gaskiyar al'amarin take, litafin Attaura da littafin Linjila, ba a saukar da su ba sai bayan mutuwarsa da lokaci mai tsawo. Yanzu ba za su yi aiki da hankulansu ba, su gane cewa, abin da suke fada karya ne? To ga shi yanzu su Yahudu da Nasara suna jayayya a kan abin da suke da ilimi a kansa na al'amarin addininsu, da abin da aka ambata a littafansu. To amma me ya sa za su rika jayayya a kan abin da ba su da ilimi a kansa na lamarin Annabi Ibrahim, da addinin da ya rayu a kansa? Allah kam iliminsa ya kewaye komai, ya san abin da su ba su sani ba, amma su ba su san komai ba daga abin da Allah ya sani.

Allah kuma ya bayyana musu gaskiyar al'amarin Annabi Ibrahim ya karyata maganar cewa shi Bayahude ne, ko Banasare. Allah ya tabbatar da cewa, Annabi Ibrahim tsaye yake ƙyam a kan addinin gaskiya, ba ruwansa da duk wata barna da shirka, yana bin umarnin Allah cikin ikhlasi, kuma ba ya cikin masu hada Allah da wani, masu bautar gumaka.

Sannan Allah ya ambaci wadanda suka fi cancantar su zama tare da Annabi Ibrahim, ya bayyana cewa, su ne wadanda suka bi addininsa, suka kuma bi hanyarsa ta kaɗaita Allah a wajen bauta, wadanda su ne Annabi, da sahabbansa, da muminai da za su zo bayansu. To wadannan su suka fi cancanta su zama masoyansa, majibintansa, kuma Allah shi ne yake jibintar lamarin muminai, ya taimaka musu, ya ba su nasara a kan abokan gabarsu.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Ya kamata Musulmi ya rika alfahari da cewa, shi Musulmi ne a ko'ina, kuma a gaban kowane ne. Ba kamar yadda wasu raunanan Musulmi suke jin kunyar su ce su Musulmai ne a gaban wadanda ba Musulmai ba.
  2. Adalci yayin tattaunawa da wanda ba Musulmi ba dole ne, balle kuma tare da wanda yake Musulmi ne.
  3. Amfanin karantar tarihi, domin zai taimaka wajen rushe ƙarairayi da dama waɗanda suka saɓa wa abin da ya tabbata a tarihi.
  4. Kafa hujja da hankali a kan gaskiya, kuma duk wani lafiyayyen hankali idan mai shi ya yi amfani da shi; to zai kai shi ga fahimtar gaskiya. Sai dai ba daidai ba ne mutum ya dogara a kan hankalinsa gaba daya, ya watsar da nassi.
  5. Imani shi ne musabbabin jibinta ta Ubangiji ga bawansa.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 69-71

  1. Wata ƙungiya daga cikin Ma'abota Littafi sun yi burin ina ma sun ɓatar da ku, kuma ba za su batar da kowa ba sai kawunansu, amma ba sa fahimtar hakan. --Quran/3/69
  2. Ya ku Ma'abota Littafi, don me kuke kafice wa ayoyin Allah, alhalin kuna shaidawa (cewa gaskiya ne)? --Quran/3/70
  3. Ya ku Ma'abota Littafi, don me kuke cakuɗa gaskiya da ƙarya, kuma kuke boye gaskiya, alhalin kuna sane? --Quran/3/71

Allah a nan yana gargadin bayinsa muminai ne game da makircin wata kungiya ta Yahudawa da Nasara, wadanda ba su da wani buri a rayuwarsu, sai na ganin Musulmai sun lalace sun bace, sun yi watsi da addininsu na Musulunci, ba don komai ba sai don hassada da suke nuna musu. Sai dai makircinsu su kadai zai ci, domin kansu kawai suke kara batarwa, don haka duk kokarin da suke yi na batar da Musulmi yana komawa ne a kansu, suna kara dulmiya ne cikin bata da taɓewa, amma su ba su san hakan ba.

Sannan Allah ya soki abin da Ma'abota Littafi ke aikatawa, yana cewa, don me suke kafirce wa Alkurani, alhalin sun san gaskiya ne, suna kuma shaidawa a kan hakan, domin sun karanta siffofin Annabi a littattafansu? Kuma don me suke cakuda karya da gaskiya, har a kasa bambancewa tsakaninsu, kuma su boye gaskiya alhalin suna sane da barnar da suke yi?

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Duk azzalumi akan saka masa da irin zaluncinsa, ko a jarrabe shi da irin cutar da yake kokarin ya yi wa wasu.
  2. Mutum yakan makance ya kasa ganin ɓatan da yake ciki.
  3. Wajibi ne a yi taka-tsantsan da mabarnata yayin da suka gauraya ƙarya da gaskiya, kuma kada a ruɗu da daɗin bakinsu.
  4. Kakkausar suka ga duk mai cakuda karya da gaskiya, kuma yake boye gaskiya. Domin ambaton Ma'abota Littafi a nan, ba don ana nufin sai su kadai ba; duk wanda ya yi irin wannan aiki ya shiga cikin wannan sukar.
  5. Taƙarƙarwar da Yahudu da Nasara suka yi wajen ganin sun batar da Musulmi shi ya hana su su bi gaskiya, domin duk sa'adda mutum ya dage kan wani mugun abu; to sai ya manta da abin da wannan abin kan iya haifar masa nan gaba.
  6. Mai boye gaskiya ba shi da wata hanyar yin hakan sai ta fuskoki biyu:
    1. Fuska ta Farko: Ya jeho wani abu mai rikitarwa don ya tabbatar da karya.
    2. Fuska ta Biyu: Ya boye duk wani dalili da zai fito da gaskiya.
  7. Haɗa ƙarya da gaskiya shi ne sanadiyyar ɓacewar al'ummomin da suka gabace mu, kuma shi ne mafarar duk wata bidi'a, domin ita bidi'a, da a ce karya ce tsantsarta; to ba za ta samu karbuwa ba, da kowa ya yi watsi da ita; da kuma a ce gaskiya ce tsantsa, to da ba ta zama bidi'a ba, da ta zama daidai da Sunna. Sai dai an gauraya karya ce da gaskiya wuri guda, sai wasu su kasa gane karyar da ke cikinta.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 72-74

  1. Kuma wata ƙungiya cikin Ma'abota Littafi suka ce: "Ku yi imani mana da abin da aka saukar wa wadanda suka yi imani a farkon yini, kuma ku kafirce a karshen yini, mai yiwuwa ne su dawo (daga rakiyar addininsu). --Quran/3/72
  2. "Kuma kada ku amince da kowa sai wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle shiriya ita ce Allah, domin kar (ku yarda a ce) an ba wani mutum irin abin da aka ba ku, ko kuma ku ba su dama su yi jayayya da ku a wajen Ubangijinku." Ka ce: "Lalle falala a hannun Allah take, Yana bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai yalwa ne, Mai yawan sani. --Quran/3/73
  3. "Yana keɓantar wanda Ya ga dama da rahamarsa, kuma Allah Ma'abocin falala ne wadda take mai girma." --Quran/3/74

A wadannan ayoyi, Allah yana ba da labarin wasu miyagun mutane ne a cikin Yahudawa da Nasara, wadanda suke ta ƙulle-ƙullen makirci ga Musulmi ta hanyar kawo ruɗu na addini ga wasu raunanan Musulmi. Sun yanke shawara a tsakaninsu cewa, su bayyana imaninsu da abin da Manzon Allah ya zo da shi a farkon yini; idan yamma ta yi kuma su kafirce masa. Yin haka shi zai sa masu raunin fahinta cikin muminai su rika cewa, da a ce gaskiya ne, da wadanda suka yi imani da shi cikin Ma'abota Littafi, ba su yi ridda ba. Manufarsu ita ce Musulmi su watsar da addininsu gaba daya.

Sannan magana ta dawo kan tattaunawar Yahudawa a tsakaninsu, da irin yadda suke yi wa junansu wasiyya, yayin da wasunsu sika faɗa wa wasu cewa, kada su yarda da kowa idan ba wanda yake bin addininsu ba, kada kuma su yarda su bayyana sirrinsu ga wani Musulmi don kada ya samu irin ilimin abin da suka samu; idan har sun yi haka to za su koye shi, su ma sai su zama masu ilimi ko kuma su riƙe shi a matsayin abin da za su kafa musu hujja da shi a gaban Allah, sai su ba da shaidar cewa, gaskiya ta bayyana gare su, ƙin bi suka yi. Sai Allah ya ce wa Annabinsa ya faɗa musu cewa, shiriya a hannun Allah take, yana bayar da ita ga wanda ya ga dama daga bayinsa. Kuma Allah mai yalwar falala ne, mai yawan kyauta, kuma mai cikakken sani ne game da wadanda suka cancanci a kyautata musu, don haka yana yin kyautarsa ne ga wanda ya cancanta, ya kuma hana wanda bai cancanta ba kuma yana keɓance wanda ya ga dama da rahamarsa, kuma shi ma'abocin falala ne mai yawa.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Gargadin Musulmin da ake amfani da su don jefa shakka a cikin zukatan raunanansu, ta hanyar yi wa Musulunci tuhumce-tuhumce iri-iri don a ɓata shi a idon 'ya'yansa, a ɓata tarihinsa da koyarwarsa da nassoshinsa. Ta hanyar sunaye wadannan raunanan mutane suke nuna su Musulmi ne, amma suna taka rawa a gefe guda irin ta Yahudawa.
  2. Wanda duk ya nemi shiriya ba ta hanyar Alƙur'ani da sunna ba; to ya ɓace, domin babu shiriya sai wadda Manzon Allah ya zo da ita.
  3. Amfanin ba da labarin wannan makirci na Yahudawa na cewa su yi imani da farkon yini, daga ƙarshensa sai su yi ridda. Amfanin fallasa su shi ne:
    1. Na daya: wannan shirin nasu sun yi ne a boye, ba wani Musulmi da ya san da shi; to yayin da Manzon Allah ya zo yana ba da labarin wannan sirri nasu, hakan ya nuna cewa lalle shi Manzon Allah ne, domin ya ba da labarin wani abu da ba wanda ya san shi sai Allah da ya sanar da shi.
    2. Na biyu: Bayan Allah ya fallasa wannan mugun shiri nasu; sai ya zama ba zai yi wani tasiri ba a zukatan muminai, don ba don haka ba, da watakila a ga tasirinsa a wurin wasu masu raunin imani.
    3. Na uku: Za su ji tsoron kara kulla wani makircin irin wannan bayan Allah ya tona asirinsu.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 75-76

  1. Kuma daga cikin Ma'abota Littafi akwai wanda in da za ka ba shi amana ta dukiya mai yawa, zai dawo maka da ita, daga cikinsu kuwa akwai wanda idan an ba shi amana ta dinare ɗaya, ba zai dawo maka da shi ba, sai fa idan ka tashi tsaye a kansa. Wannan kuwa saboda sun ce: "Babu wani laifi a kanmu (don mun ci dukiyar) bobayin mutane." Kuma suna fadin karya su jingina wa Allah, alhalin su suna sane.
  2. Ba haka ba ne, duk wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya tsare dokar Allah, to lalle Allah Yana son masu taqawa.

Bayan Allah ya bayyana mana irin karyar da Yahudawa suke yi na cewa an ba su matsayi na ilimi da addini wanda ba wanda aka ba irinsa, da kuma nuna cewa bin addininsu kadai shi ne shiriya, sai Allah a nan ya karyata su, ya nuna su a matsayin maciya amana, wadanda mu'amalarsu da mutane babu gaskiya a cikinta, kamar yadda mu'amalarsu da Allah ita ma babu gaskiya a cikinta ko kadan.

Allah ya bayyana cewa, a cikin ma'abota Littafi akwai mai amana, wanda idan da za ka ba shi amanar dukiya komai yawanta, ba zai ci komai daga cikinta ba, zai dawo maka da ita kamar yadda ka ba shi. Daga cikinsu kuma akwai maci amana wanda da za ka ba shi dan kudi kadan, kamar Dinari daya; to ba zai taɓa dawo maka da kayanka ba, sai ka yi tsayuwar daka a kansa, ka matsa masa, sannan zai dawo da shi.

Sai kuma Allah ya bayyana dalilin wannan mugun hali nasu da cewa, saboda suna riyawa ne cewa, ba su da wani laifi don sun ci dukiyar wadanda ba Yahudawa ba, wato suna nufin Musulmi. Watau a nan sun hada laifuka biyu: Laifin cin dukiyar haram da kuma laifin halatta haram. To wannan ita ce karyar da suka yi wa Allah, alhalin sun san karya suke.

Sannan Allah ya rushe wannan da'awar tasu, da cewa, al'amarin ba haka yake ba. Duk wani Bayahude ko Banasare idan ya cika alkawarin da Allah ya yi da su, ya yi imani da Annabi SAW da Alkur'anin da ya saukar masa, ya kiyaye dokokin Allah ta hanyar aikata abin da aka umarce shi da barin abin da aka hana shi; to lalle ya sani Allah yana son masu taqawa cikin bayinsa.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. A cikin Ma'abota Littafi da mushrikai za a iya samun masu amana, don haka ana iya ba wa ɗayansu amanar dukiya. Ya halatta Musulmi ya dauki kafiri mai amana aikin likitanci, domin wannan yana daga cikin karbar labarin abin da suka sani na sha'anin duniya. Wannan ya halatta, sai dai idan an hango wata barna; to sai a kauce mata. Duk da halaccin yin haka amma mu'amala da Musulmi mai amana ta fi.
  2. Wanda duk ya yi wa Allah karya yana sane, ya fi girman zunubi, fiye da wanda ya yi masa karya bisa ga rashin sani.
  3. Wanda duk ya cika alkawarin da ya daukar wa Allah, ya guji karya ko yaudara; to Allah zai so shi, ya yi masa rahama duniya da lahira.
  4. Cika alkawarin Allah ya kunshi alkawarin da ke tsakaninsa da bawansa na bauta masa, da ba shi hakkokinsa, da kuma alkawarin da ke tsakanin bawa da sauran 'yan'uwansa bayi.
  5. Tsoron Allah da bawa zai siffanta da shi, shi ne zai sa Allah ya so shi.
  6. Duk wata mu'amala mai kyau da bawa zai yi; to ya yi domin neman yardar Allah, da haka ne Allah zai saka masa da soyayyarsa gare shi.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 77-80

  1. Lalle wadanda suke musanya alkawarin Allah da rantse-rantsensu da wani dan farashi ƙanƙani, wadannan ba su da wani rabo a lahira, kuma Allah ba zai yi musu magana ba, kuma ba zai dube su (duba na rahama) ba a ranar alkiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi. --Quran/3/77
  2. Kuma lalle daga cikinsu akwai wani bangare da suke karkatar da harshensu lokacin karanta Littafin (Attaura), don ku yi zaton yana cikin Littafin, alhali kuwa ba ya cikin Littafin, kuma za su rika cewa, shi (wahayi ne saukakke) daga wurin Allah, alhalin kuwa ba daga wurin Allah yake ba, kuma za su rika faɗar ƙarya suna jingina wa Allah, alhalin suna sane. --Quran/3/78
  3. Bai dace ba ga wani mutum wanda Allah zai ba shi littafi da hukunci da annabci, sannan ya ce wa mutane: "Ku zama bayina ba na Allah ba," sai dai (ya ce): "Ku zamo malamai na Allah saboda abin da kuke karantarwa na littafi, kuma saboda abin da kuka kasance kuna karantawa." --Quran/3/79
  4. Kuma ba zai umarce ku da ku riki mala'iku ko annabawa a matsayin iyayengiji ba; yanzu zai umarce ku da kafirci ne bayan kuna Musulmi? --Quran/3/80

A wadannan ayoyi, Allah yana ba da labarin irin uƙubar da ya tanadar wa wadanda suke karya alkawarin da suka yi tsakaninsu da shi, su canja shi don wani abu na duniya da bai taka kara ya karya ba, maimakon su yi biyayya ga Annabi, su yi imani da shi, sai su rika rantsuwar karya don su samu wani abin duniya. Allah ya ce, wadannan ne ba su da wani rabo na alheri a lahira, kuma Allah ba zai yi magana da su ba, kuma ba zai dube su ba, sannan ba zai tsarkake su daga zunubansu ba, kuma suna da wata azaba mai radadi.

Abdullahi dan Mas'ud ya ce: Wanda ya yi rantsuwa don ya ci wata dukiya da ba tasa ba; to zai haɗu da Allah yana mai fushi da shi. Sai Allah ya gaskata wannan magana tasa, ya saukar da wannan ayar: "Lalle wadanda suke musanya alkawarin Allah da rantse-rantsensu da wani dan farashi ƙanƙani,..." har zuwa karshen ayar.

Abdullah (bin Mas'ud) said, "Whoever took a false oath in order to grab somebody's property will meet Allah while Allah will be angry with him." Allah revealed the following verse to confirm that:--"Verily! Those who purchase a small gain at the cost of Allah's covenant And their oaths...a painful torment." (3.77)

Abu Wa'il ya ce: Sai Al-Ash'as dan Qais ya fito gare mu ya ce: Me Abu Abdurrahman yake fada muku (yana nufin Ibn Mas'ud)?

Al-Ash'ath bin Qais came to us and asked as to what Abu Abdur-Rehman (i.e. Ibn Mas'ud) was telling you."

Sai muka fada masa. Sai ya ce: "Gaskiya ya fada, a kaina wannan ayar ta sauka. Mun yi rigima da wani mutum a kan wata rijiya, sai muka je gaban Annabi SAW domin ya yi mana hukunci,

We related the story to him. On that he said, "He has told the truth. This verse was revealed about me. I had some dispute with another man regarding a well and we took the case before Allah's Messenger (ﷺ).

sai Manzon Allah ya ce: "Kawo shaidunka biyu, ko kuma shi ya rantse."

Allah's Messenger (ﷺ) said (to me), "Produce two witnesses (to support your claim); otherwise the defendant has the right to take an oath (to refute your claim).'

Sai na ce: In dai haka ne; to fa shi zai rantse ba tare da ya damu ba.

I said, 'The defendant would not mind to take a false oath."

Sai Manzon Allah ya ce: "Duk wanda ya yi rantsuwa don ya cancanci wata dukiya alhalin ƙarya yake; to zai haɗu da Allah alhalin yana mai fushi da shi."

Allah's Messenger (ﷺ) then said, 'Whoever took a false oath in order to grab someone else's property will meet Allah, Allah will be angry with him.'

Sai Allah ya gaskata wannan magana, ya saukar da wannan ayar. [Bukhari #2515-2516 da Muslim #136].

Allah then revealed what Confirmed it." Al-Ash'ath then recited the following Verse:--"Verily! Those who purchase a small gain at the cost of Allah's covenant, And their oaths . . . (to) . . . they shall have a painful torment!' (3.77) (See Hadith No. 546) https://sunnah.com/bukhari:2515

Abdullahi dan Abu Aufa yana cewa: Wani mutum a kasuwa, ya tsaya a kan hajarsa yana rantsuwar cewa, an saya da kudi kaza da kaza, alhalin karya yake, don kawaiya zurma wani Musulmi. Sai Allah ya saukar da wannan ayar. [Bukhari #2088].

Babu cin karo tsakanin ruwayoyin nan guda 2, domin zai iya yiwuwa ayar ta sauka a kan kissoshin biyu.

Sannan Allah ya bayyana wa muminai halin wasu mutane daga cikin Yahudu da Nasara cewa, idan suna karanta littafin da aka saukar musu, sai su rika karkata harshensu suna jirkita wasu lafuzan littafin, suna wasa da ma'anoninsa, da nufin ɓatar da muminai, don su zaci cewa maganar Allah ce abin da suke karantawa, alhalin ba ita ba ce; kawai wannan wata bidi'a ce suka shigo da ita a cikin addini. Da wannan aiki nasu, suna yi wa Allah karya ne tare da suna sani.

Sai kuma Allah ya bayyana cewa, ba abu ne mai yiwuwa ba, Allah ya zaɓi wani mutum, ya ba shi littafi da hikima, ya yi masa baiwar annabci, sannan ya rika kiran mutane kan su bauta masa ba Allah ba. Idan har Allah ya yi wa wasu bayinsa irin wannan baiwa; to zai umarce su ne da su zamo malamai na Allah, masu aiki da iliminsu, masu ikhlasie da bautar Allah, suna koyar da mutane ilimi da tarbiyya ta kwarai, saboda littafin Allah ne suke koyarwa. Hakanan kuma ba zai umarce su su rika bauta wa mala'iku ko annabawa, ba Allah ba. Domin babu yadda za a yi ya umarce su da su kafirce wa Allah bayan sun musulunta, sun mika wuya ga Allah.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Wanda ya tilasta wa mutane su bi maganarsa, su yi masa ɗa'a a kowanne hali; to ya zama mai kiran su ne su bauta masa, ba Allah ba.
  2. Ya kamata mutum ya zama mai koyar da ilimi, kuma malami na Allah, domin duk malamin da ba na Allah ba; to iliminsa na banza ne ba zai amfane shi da komai ba.
  3. Bayanin kafircin wadanda yake bauta wa mala'iku ko annabawa ko waliyyai ko kuma malamai.
  4. Karya alkawari da yarjejeniya yana daga cikin manya-manyan abubuwan da suke kawo matsala a zamantakewar al'umma, shi ya sa Allah ya yi alkawarin narko mai tsanani ga wadanda suke karya alkawali.
  5. Malami ba shi ne wanda ya cika ƙwaƙwalen mutane da ilimi ba kawai, a'a dole sai ya hada da yi musu tarbiyya ta kwarai.
  6. Allah ya tsoratar da masu sayen wani abin duniya da alkawarin da ke tsakaninsu da Allah. Malamai masu boye gaskiya don wani abin duniya sun shiga cikin wannan gargadi.
  7. Hukuncin alkali ba ya halatta haram. Don haka ko alkali ya yi hukuncin danka dukiyar wani ga wanda ba tasa ba, saboda abin da ya bayyana gare shi na dalilai, to wannan ba ya halatta masa wannan abin.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 81-82

  1. Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya yi alkawari da annabawa cewa: "Duk irin abin da Na ba ku na littafi da wata hikima, sannan sai wani Manzo ya zo muku mai gaskata abin da yake tare da ku, to lalle ku yi imani da shi, kuma lalle ku taimake shi." Ya ce: "Shin kun yarda da hakan, kuma kun dauki alkawarina a kan hakan?" Suka ce: "Mun yarda da haka." Ya ce: "To ku shaida, kuma Ni ma Ina tare da ku cikin masu shaidawa." --Quran/3/81
  2. To duk wanda ya juya baya bayan wannan, to wadannan sune fasikai. --Quran/3/82

A wadannan ayoyi Allah yana tunatar da Annabinsa lokacin da ya dauki alkawari mai karfi tsakaninsa da annabawa cewa, duk da annabcin da ya aiko su da shi da littattafai da hikima da ya ba su, sannan daga baya ya aiko da wani manzo ya zo musu, su da al'ummominsu, yana tabbatar da gaskiyar da suka zo da ita, to wajibi ne su yi imani da shi su gaskata abin da ya zo da shi, su taimaka masa. Ana nufin Manzon Allah Muhammadu SAW. Sannan Allah SWT ya ƙara ƙarfafa musu cewa, sun yarda da wannan alƙawari, kuma sun riƙe shi da ƙarfi?! Dukkansu suka amsa da cewa, sun yarda kuma sun tabbata. Sai Allah ya kafa su da su zama masu shaidar kansu da kansu akan haka da kuma al'ummominsu. Duk kuma wanda ya bijire bayan wannan alƙawari da ya ɗauka; to masu yin haka su ne fasikai, wadanda suka fita daga ɗa'ar Allah.

Jabir ɗan Abdullahi ya ruwaito cewa, Manzon Allah ya ce: "Da a ce ɗan'uwana Musa yana nan da ransa, da babu abin da zai fisshe shi, dole sai yi min biyayya." [Ahmad #5195].

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Falalar Annabi Muhammadu SAW a kan sauran annabawa.
  2. Annabawa gaba dayansu bayi ne na Allah, masu bauta masa da bin umarninsa.
  3. Idan ya zamana wajibi ne a kan annabawa su yi imani da Annabi SAW; to imanin al'ummominsu da shi ya fi zama wajibi a kansu.
  4. Babu wata hanyar samun yardar Allah, sai ta hanyar bin Manzon Allah, ko da kuwa annabawa ne, da a ce suna da rai lokacin aiko Annabi Muhammad SAW; to sai sun yi imani da shi.
  5. Wannan aya tana matsayin martani ga masu cewa Khadir yana nan da ransa bai mutu ba. Domin da wannan magana gaskiya ce, da ya zama wajibi a kansa ya bayyana a zamanin Annabi SAW, ya yi imani da shi, ya yi jihadi tare da shi, ya taimaka masa.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 83-85

  1. To shin yanzu wani addini suke nema ba na Allah ba, alhalin duk wanda yake cikin sammai da ƙasa gare Shi ne ya mika wuya yana so ko yana ƙi, kuma zuwa gare Shi za a komar da su? --Quran/3/83
  2. Ka ce: "Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar wa Ibrahimu da Isma'ila da Ishaq da Yaqoob da jikokin Yaqoob, da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba wa annabawa dafa Ubangijinsu; ba ma nuna bambanci a kan daya daga cikinsu, kuma mu muna masu mika wuya gare Shi."
  3. Duk kuma wanda ya nemi (bin) wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za karba daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru.

A wadannan ayoyi, Allah yana bayyana cewa, duk wanda ya nemi wani addini ba Musuluncin da Allah ya aiko Annabinsa Muhammad sa shi ba; to ya yi aikin banza. Allah yana sukar duk wanda ya nemi wani addini ba na Allah ba, kuma ba shari'arsa ba, alhalin duk wadanda suke sama da wadanda suke ƙasa, gare shi suka mika wuya, sun so hakan, ko ba su so ba, duk suna karkashin ikonsa ne, shi ne mai sarrafa su yadda ya ga dama. Kuma idan suka mutu zuwa gare shi ne makomarsu take, zai yi wa kowa hisabi da gwargwadon aikinsa.

Allah kuma ya fuskantar da maganarsa zuwa ga Annabi, yana umartar sa da ya gaya wa wadanda suke neman wani addini daban ba Musulunci ba cewa, mu mun yi imani da Allah da Alkur'anin da aka saukar mana, da kuma sunnah, da duk abin da Allah ya saukar wa annabawansa - Annabi Ibrahim da 'ya'yansa, Annabi Isma'ila da Annabi Ishaq da Yaqoob dan Ishaq, da kuma abin da aka saukar wa annabawan Banu Isra'ila, wadanda suka fito daga zurrriyar 'ya'yan Annabi Yaqoob, su goma sha biyu (12). Hakanan mun yi imani da littafin Attaura da Allah ya saukar wa Annabi Isa da kuma mu'ujizojin da Allah ya ba su domin tabbatar da gaskiyarsu. Mun yi imani da duk annabawa gaba dayansu, da abin da aka saukar musu na littattafai daga Ubangijinsu, ba za mu bambanta tsakaninsu ba wajen imani, ta hanyar yin imani, ta hanyar yin imani da wasu, mu kafirce wa wasu; mu gaba dayanmu ciki da waje, mun mika wuya ga Allah, ba za mu yarda da wani addini in ba Musulunci ba.

Sannan Allah ya bayyana cewa, duk wanda ya bi wani addini ba na Musulunci ba; to ba za a taɓa karbar sa daga gare shi ba, kuma a lahira yana cikin hasararru, wannan kuma ita ce hasara ta hakika, domin ya wahalar da kansa a kan abin da bai amfane shi ba.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Musulunci shi kadai ne addini a wurin Allah. Wanda ya bi wani addini ba Musulunci ba; to Allah ba zai kaɓe shi daga wurinsa ba.
  2. Dole ne a kan duk wani mai furuci, ya furta imaninsa da Allah da bakinsa, kamar yadda yake wajibi a kansa ya ƙudurce a zuciyarsa.
  3. Imani da Allah shi ne asali, duk sauran abubuwa da bawa yake imani da su rassa ne nasa, shi ya sa Allah ya gabatar da shi a nan.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 86-89

  1. Ta yaya Allah zai shiryar da mutanen da suka kafirta bayan imaninsu, kuma bayan sun shaida cewa, Manzon gaskiya ne, kuma hujjoji sun zo musu? Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai.
  2. Wadannan sakamakonsu shi ne, la'antar Allah za ta tabbata a kansu da ta mala'iku da mutane gaba daya.
  3. Suna masu dawwama a cikinta, ba za a sassauta musu azaba ba, kuma ba za jinkirta musu ba.
  4. Sai fa wadanda suka sake tuba bayan haka, kuma suka gyara (ayyukansu), to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

A wadannan ayoyi, Allah yana bayyana cewa, ba zai shiryar da mutanen da suka yi ridda ba, suka juya wa MUsulunci baya, alhalin da farko sun yi imani, kuma sun tabbatar da cewa, Annabi Muhammad gaskiya ne, saboda hujjoji bayyanannu, kuma gamsassu, masu ƙara tabbatar da gaskiyarsa. Ta yaya irin wadannan za su cancanci shiriya? Allah ba ya shiryar da wadanda suka zalunci kawunansu, ta hanyar barin gaskiya bayan sun fahimce ta, suka kama ƙarya bayan sun gane ƙarya ce a fili.

Sannan Allah ya faɗi uƙubar waɗannan azzaluman a duniya da lahira, wadda ita ce la'anar Allah da mala'iku da duk halittun Allah a kansu, kuma za su ci gaba da zama cikin wannan la'anar, da wannan ukubar, har abada, kuma ba za a taɓa sassauta musu azaba ba, kuma ba za a saurara musu ba.

Amma sai Allah ya yi togaciya ta wadanda suka tuba, suka yi ayyuka na kwarai, kuma suka gyara kurakuren da suka yi; to wadannan Allah yana yafe musu, saboda shi mai yawan gafara ne, mai yawan jin kai ga bayinsa masu tuba su gyara. Abdullahi dan Abbas yana cewa:

  1. "Wani mutumin Madina ya musulunta,
    "A man from among the Ansar accepted Islam,

  2. daga baya kuma sai ya yi ridda, ya koma shirka.
    then he apostatized and went back to Shirk.

  3. Sannan ya dawo ya yi nadama, sai ya aika wa mutanensa yana cewa:
    Then he regretted that, and sent word to his people (saying):

  4. 'Ku tambayar mini Manzon Allah, shin zan iya sake tuba?'
    'Ask the Messenger of Allah [SAW], is there any repentance for me?'

  5. Mutanensa suka sami Manzon Allah, suka faɗa masa cewa:
    His people came to the Messenger of Allah [SAW] and said:

  6. 'Wane da ya yi ridda ya yi nadama, kuma ya aiko mu mu tambaya masa cewa, shin zai iya sake tuba?'
    'So and so regrets (what he did), and he has told us to ask you if there is any repentance for him?'

Sai wannan ayar ta sauka: 'Ta yaya Allah zai shiryar da mutanen da suka kafirta bayan imaninsu...' har inda ya ce: '...to lalle Allah mai gafara ne, mai jin kai.' Sai Annabi ya aika masa ya zo ya sake shiga Musulunci." [Nisa'i #4068 da Ahmad #2218].

Then the Verses: 'How shall Allah guide a people who disbelieved after their Belief up to His saying: Verily, Allah is Oft-Forgiving, Most Merciful' was revealed. So he sent word to him, and he accepted Islam." https://sunnah.com/nasai:4068

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Ɓacewar mai ilimi ta fi ɓacewar jahili muni.
  2. Jahili ya fi saurin mika wuya yayin da za a fahimtar da shi abin da bai fahinta ba, amma wanda ya sani ya kangare; to wannan yana da wuya ya dawo kan hanya.
  3. Tubar bawa ba ta cika, har sai ya gyara barnar da ya yi a baya, ko da ta hanyar bayyana cewa abin da yake kai a baya ɓata ne, don ire-irensa su dawo, su ma su taba. Ko kuma idan ya ja wasu zuwa ga wannan ɓatan; to dole ne ya bayyana musu abin da suke a kai ɓata ne.
  4. Duk wanda Allah ya yi wa wata ni'ima, sannan ya kafirce masa; to Allah na iya karbe wannan ni'imar daga hannunsa.
  5. Wanda ya yi ridda, sannan daga baya ya tuba, ya gyaru; to Allah zai karbi tubansa a duniya da lahira.
  6. Tuba yana kankare laifin da mai tuba ya yi a baya, ko da kuwa kafirci ne.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 90-91

  1. Lalle wadanda suka kafirta bayan imaninsu, sannan suka ƙara zurfi cikin kafirci, to ba za a karbi tubansu ba, kuma wadannan su ne batattu. --Quran/3/90
  2. Lalle wadanda suka kafirta, kuma suka mutu alhali suna kafirai, to ba za a karbi cikin ƙasa na zinari daga daya daga cikinsu ba, ko da zai fanshi kansa da shi. Wadannan suna da wata azaba mai radadi kuma su da wasu mataimaka.

A wadannan ayoyi, Allah yana bayanin ukubar wadanda suka yi imani, sannan daga baya suka yi ridda, suka kafirta, sannan suka yi ƙara nutsawa cikin kafirci, suka kuma zauna a haka, har suka mutu cewa, Allah ba zai taɓa karɓar tubansu ba, domin su ne suka zaɓi su bar hanyar gaskiya, su bi hanyar ɓata.

Sannan Allah ya kara tabbatar da cewa, wadanda suka kafirta, kuma suka mutu a kan kafirci, ba su tuba ba; to Allah ba zai karbi aikin da suka yi ba, ko da kuwa zai yi sadaka da kwatankwacin cikin ƙasa na zinariya domin ya kusanci Allah da wannan sadakar, Allah ba zai karba ba, ko kuma ya ce zai fanshi kansa da wannan, to Allah ba zai karba ba. Sakamakon wadannan a lahira shi ne azabar wuta mai radadi, kuma babu wanda ya isa ya kubutar da su daga wannan azabar.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Yadda imani yake ƙaruwa da ayyuka na ƙwarai, haka shi ma kafirci yake hauhawa da ƙaruwar aikata ayyukan kafirci.
  2. Tubar mutum ba za ta zama karbabbiya ba a wurin Allah har sai ya bar laifukan da yake aikatawa, ya kuma gyara abin da ya bata a baya.
  3. Mummunan aiki yana haddasa wani mummuna irinsa, matukar bawa bai dawo kan tafarki madaidaici ba.
  4. Wanda ya yi ridda ya bar Musulunci har mutuwa ta zo masa bai tuba ba; to ba za a karbi tubansa ba a wannan lokacin.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 92

  1. Ba za ku taɓa dacewa da aiki na alheri ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so, kuma abin da duk kuka ciyar kowane iri ne, to lalle Allah Yana sane da shi.

3:92

لَن تَنَالُوا۟ ٱلْبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُوا۟ مِمَّا تُحِبُّونَ ۚ وَمَا تُنفِقُوا۟ مِن شَىْءٍۢ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌۭ ٩٢

You will never achieve righteousness until you donate some of what you cherish. And whatever you give is certainly well known to Allah.

— Dr. Mustafa Khattab, The Clear Quran

Never will you attain the good [reward][1] until you spend [in the way of Allāh] from that which you love. And whatever you spend - indeed, Allāh is Knowing of it.

— Saheeh International

[1] Another meaning is "You will never attain righteousness."

Lan tanaloo albirra hattatunfiqoo mimma tuhibboona wama tunfiqoo minshay-in fa-inna Allaha bihi AAaleem

— Transliteration

Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah, gare shi, Masani ne.

— Hausa Translation(Abubakar Gumi)


Bayan Allah a ayar baya ya yi bayanin cewa, ba zai karbi sadakar kafiri ba, ko da zai ciyar da kwatankwacin cikin duniya na zinari, don ya kuɓutar da kansa daga azabar Allah a ranar alƙiyama, sai a wannan ayar Allah yake kwaɗaitar da muminai kan su ciyar da dukiyarsu, kuma ya bayyana cewa, abin da ya fi son bawa ya yi sadaka da shi, shi ne abin da shi ya fi so; wannan ne zai kai shi matakin samun alheri mai yawa. Allah yana cewa: "Ba za ku kai ga samun alheri mai yawa ba daga Allah, har sai kun yi sadaka da dukiyar da kuke ƙauna a zukatanku. Duk abin da kuka ciyar na dukiyarku; to Allah ya sani, kuma a ranar lahira zai saka wa wanda ya yi haka da cikakken sakamako."

An karbo daga Anas dan Malik ya ce:

  1. "Abu Talha mutumin Madina ne mai yawan dukiya; abin da kuma ya fi kauna cikin dukiyarsa ita ce gonarsa mai suna Bairuha, tana kallon masallacin Annabi.
    Abu Talha had the greatest wealth of date-palms amongst the Ansar in Medina, and he prized above all his wealth (his garden) Bairuha', which was situated opposite the Mosque (of the Prophet (ﷺ) ).

  2. Hasali ma Annabi yakan shiga cikinta ya sha ruwanta mai dadi.
    The Prophet used to enter It and drink from its fresh water.

  3. To lokacin da wannan ayar ta sauka... sai Abu Talha ya ce:
    When the following Divine Verse came:--(3.92) Abu Talha got up saying.

  4. "Ya Manzon Allah, Allah yana cewa: 'Ba za ku taba dacewa da aiki na alheri ba, har sai kun ciyar daga abin da kuke so...', "
    "O Allah's Messenger (ﷺ)! Allah says, 'You will not attain piety until you spend of what you love,'

  5. ni kuma a cikin dukiyata na fi son Bairuha, don haka na bayar da ita sadaka don Allah,
    and I prize above al I my wealth, Bairuha' which I want to give in charity for Allah's Sake,

  6. ina fatan alherinta da ajiyayyen ladanta a wurin Allah Ta'ala
    hoping for its reward from Allah.

  7. don haka ya Ma'aikin Allah, ka saka ta inda Allah Ta'ala ya nuna maka.
    So you can use it as Allah directs you."

  8. Sai Annabi ya ce: "Taɓdi! Wannan fa dukiya ce mai riba.
    On that the Prophet (ﷺ) said, "Bravo! It is a profitable (or perishable) property. (Ibn Maslama is not sure as to which word is right, i.e. profitable or perishable.)

  9. to lalle na ji abin da ka ce, amma ni ina ganin ka yi kyautarta ga danginka mafi kusanci da kai shi ya fi riba."
    I have heard what you have said, and I recommend that you distribute this amongst your relatives."

  10. Sai Abu Talha ya ce: "Ya Ma'aikin Allah! Zan yi hakan,
    On that Abu Talha said, "O Allah's Messenger (ﷺ)! I will do (as you have suggested)."

  11. Sai Abu Talha ya raba wa danginsa da 'ya'yan baffanninsa wannan gonar. [Bukhari #2769, Muslim #998, Ahmad #12461]
    So, Abu Talha distributed that garden amongst his relatives and cousins. https://sunnah.com/bukhari:2769

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kwaɗaitar da muminai a kan su nemi alheri, ta hanyar gabatar da soyayyarsu ga Allah a kan soyayyarsu ga dukiyoyinsu. Yayin da suka haƙura da abin da ransu yake so, suka fitar da dukiyarsu suka bayar don Allah; to zukatansu za su tsarkaka daga cutar rowa da bautar dukiya.
  2. Abin da yake shiga rai sosai shi ne mutum ba ya son rabuwa da shi, don haka bayar da shi sadaka yana nuna karfin imanin mai yin hakan.
  3. Yayin da mawadata za su rika bayar da dukiyarsu da suke so ga talakawa, wannan zai kawo gyaruwar al'umma, kuma ya kara dankon zumunta tsakanin mawadata da talakawa marasa abin hannu, sai rayuwa ta yi kyau ga kowa da kowa.
  4. Yin sadaka don Allah, domin Allah ya san komai da ke cikin zukatan bayinsa, kuma zai yi musu sakayya gwargwadon abin da suka kudurce na ikhlasi ko hashinsa.
  5. Allah ya neme mu da mu ciyar da wani abu na dukiyarmu wanda muke so, ba duka ba. Wannan yana daga cikin rahamar Allah da tausayinsa ga bayinsa, wajen dora musu abin da za su iya dauka, ba wanda zai gagare su ba.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 93-94

  1. Duk wani abinci ya kasance halal ne ga Banu Israila sai abin da shi Isra'ilu ya haramta wa kansa tun kafin a saukar da Attaura. Ka ce: "To ku zo da Attaura, sai ku karanta ta in kun kasance masu gaskiya.
  2. To duk wanda ya kirkiri karya ya jingina wa Allah bayan wannan, to wadannan su ne azzalumai.

Allah a wadannan ayoyi yana ba da labarin cewa, kafin a saukar da Attaura ga Annabi Musa, duka wani nau'i na abinci halal ne ga Banu Isra'ila su ci, sai nau'i guda ɗaya wanda shi Isra'ilu, wato Annabi Yaqoob ya haramta wa kansa, ba Allah ne ya haramta masa ba, sannan daga baya 'ya'yansa su ma suka yi koyi da shi, suka haramta wa kawunansu cin wannan nau'i na abinci. Wannan kuwa shi ne naman rakuma da nononsu. To bayan saukar da Attaura, sai Allah ya haramta musu abin da ya ga dama a cikinta, ya kuma halatta musu abin da ya ga dama. Don haka wannan hukuncin ya shafe wancan hukunci na halatta musu komai, sai rakuma da nononsu. Sai Allah Ta'ala ya umarci Annabinsa da ya nemi Yahudawa su dauko littafin Attaura su karanta idan abin da suke fada gaskiya ne, wanda kuma ba za su gan shi ba. To bayan Allah ya tsayar musu da hujja, sai ya fada musu cewa, duk wanda ya kuskura ya yi masa karya bayan wannan bayanin da suka ji; to wadannan su ne azzalumai.

Abdullahi bin Abbas yana cewa: Wata kungiyar Yahudawa sun je gaban Annabi suka ce: "Ya Baban Alqasim, za mu tambaye ka wasu abubuwa, ka ba mu amsarsu, domin babu wanda ya san su sai annabi."

Daga cikin abin da suka tambaye shi, sun ce:

"Wane abinci ne Isra'ilu (Jacob) ya haramta wa kansa tun kafin a saukar da Attaura?"

“What did Jacob forbid himself of food?”

Sai Annabi ya ce: "Na hada ku da Allah, shin kun san cewa, Isra'ilu (Annabi Yaqoob/Jacob) ya dade yana rashin lafiya mai tsanani, sai ya yi bakance na cewa, idan Allah ya ba shi lafiya to zai haramta wa kansa abin shan da ya fi so da abincin da ya fi so, kuma abincin da ya fi so shi ne naman rakuma. Abin shan da ya fi so kuma shi ne nononsu?"

Sai Yahudawan nan suka ce: "Gaskiya ne, haka ne." [Ahmad #2471 da Tafsirin Tabari #7420, da Almu'ujamaul Kabir 12:246 #13012].

3.93 Abbas - Tanwîr al-Miqbâs min Tafsîr Ibn ‘Abbâs
(All food was lawful unto the Children of Israel) all food that is lawful for Muhammad and his community today was lawful for the Children of Israel, the sons of Jacob, (save that which Israel) Jacob (forbade himself) by the way of vows, ((in days) before the Torah was revealed) before the revelation of the Torah to Moses, Jacob forbade himself the meat and milk of camels. When this verse was revealed, the Prophet (pbuh) asked the Jews: “What did Jacob forbid himself of food?” They said: “he did not forbid himself any type of food, and whatever is forbidden for us today, such as the meat of camels and other things, was already forbidden on all prophets, from Adam to Moses (pbut). It is only you who make such things lawful”. And they claimed those things were also forbidden in the Torah. Hence Allah said to Muhammad (pbuh): (Say) to them: (Produce the Torah and read it (unto us)) where they are made forbidden (if ye are truthful) in your claim. But they failed to produce the Torah and knew they were liars since there was nothing in the Torah to substantiate their claim.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Martani ga Yahudawa masu karyata samuwar shafe hukunci a sharia, wato naskhu.
  2. Umartar su da su dauko Littafin Attaura su karanta, wata hanya ce ta kafa wa abokin husuma hujja da abin da ya yi imani da shi kuma ya yarda da shi, wadda ba ta yadda zai iya kauce mata.
  3. Umartar su da cewa su karanta su da kansu, bai ce 'mu karanta' ba, domin idan da Musulmi ne za su karanta, suna iya cewa ba su yarda ba, su rika tuhumar Musulmi cewa sun yi kari ko ragi a cikin karatun. Don haka su suka karanta da kansu, suka kuma ga gaskiyar a fili.
  4. Kira zuwa ga bin gaskiya, domin duk sa'adda gaskiya ta bayyana a fili, kuma mutum ya kauce mata; to wannan ya tabbata babban azzalumi. Domin babu zaluncin da ya kai a kirawo shi zuwa ga hukunci da Littafin Allah, sannan ya bijire, saboda girman kai da kangara.
  5. Mayar da martani ga Yahudawa masu da'awar suna bin addinin Annabi Ibrahimu, amma kuma suna jayayya da Musulmi a kan an halatta musu wasu abubuwa da su aka haramta musu a cikin Littafin Attaura. Domin ai addinin Annabi Ibrahimu bai haramta abubuwan da su aka haramta musu su a cikin Attaura ba. Don haka Musulmi su ne masu bin Addinin Annabi Ibrahimu na gaskiya.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 95-97

  1. Ka ce: "Allah Ya yi gaskiya. Don haka ku bi addinin Ibrahimu, mai karkace wa barna, kuma bai taba zama daya daga cikin mushirikai ba." --Quran/3/95
  2. Lalle farkon daki da aka tanada don mutane (su yi ibada a cikinsa) shi ne wanda yake cikin Bakka, (daki ne) mai albarka, kuma shiriya ne ga talikai. --Quran/3/96
  3. A cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, (kuma akwai) Maqamu Ibrahim; wanda duk ya shige shi ya zama amintacce. Kuma lalle Allah Ya wajabta wa mutane ziyarar wannan dakin ga wanda ya sami iko. Wanda kuwa ya kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin talikai. --Quran/3/97

A wadannan ayoyi, Allah yana umartar Annabi SAW da ya ce wa Yahudawa, duk abin da Allah ya labarta ko ya shar'anta na hukuncil to gaskiya ne, kamar abin da ya fada musu cewa, babu wani abin da Allah ya haramta musu kafin saukar da Attaura, sai nau'i biyu (2), watau naman rakumi da nonansa. Don haka su zo su bi addinin Annabi Ibrahimu Alaihissalam, idan har su masu gaskiya ne game da tutiyar su ta cewa su jikokinsa ne' domin shi mai kadaita Allah ne, ba ya shirka, ba ya kuma tare da masu yin ta.

Sannan Allah ya ba da labarin cewa, farkon dakin da aka gina shi domin mutane su bauta masa a cikinsa, kuma su yi ɗawafi su yi salla, su yi i'itikafi shi ne Ɗakin Ka'aba. Ɗakin Allah ne mai alfarma da ke garin Makka, mai ɗimbin albarka da abubuwan amfani masu yawa, na addini da na rayuwa, kamar riɓanyar lada a wurinsa da kuma arziki mai ɗimbin yawa da Allah ya kawo a garin, kuma shiriya ne ga ɗaukacin talikai, musamman zamantowarsa alƙibla ga Musulmi baki daya lokutan sallolinsu. Kuma shi ne wurin hajjinsu da umurarsu. To amma Yahudawa da Nasara masu tutiyar su ne a kan addinin Annabi Ibrahim Alaihissalam, sai ga shi ba sa zuwa Dakin da ya gina domin aikin hajji da umara, wanda hakan yake nuna sun yi hannun riga da shi, ba su da addininsa.


An karbo daga Abu Zarri ya ce: Na tambayi Manzon Allah SAW cewa wane masallaci aka fara ginawa a bayan ƙasa?

I heard Abu Dharr saying: I asked the Messenger of Allah (ﷺ) about the mosque that was first set up on the earth.


Sai ya ce: Masallaci mai alfarma.

He said: Masjid Harim.


Sai na ce: "Sai kuma wanne?" Sai ya ce: "Masallacin Qudus."
I said: Then which next? He said: The Masjid al-Aqsa.


Sai na ce: "Shekaru nawa ne a tsakaninsu?"

I said: How long is the space of time between the two?


Sai ya ce: "Shekaru arba'in (40). Sannan duk inda salla ta kama ka bayan haka; to ka fuskance shi a sallarka, a nan falalar take." [Bukhari #3366 da Muslim #520]

He said: Forty years. He (then) further said: The earth is a mosque for you, so wherever you are at the time of prayer, pray there. https://sunnah.com/muslim:520b

A cikin wannan Dakin akwai dalilai bayyanannu masu nuna kadaitakar Allah da hikimarsa da adalcinsa da girman Qudirarsa da sauran siffofinsa madaukaka, da kuma wasu alamomi masu nuna girman darajar wannan Dakin, daga cikinsu har da wuraren da Annabi Ibrahim ya tsaya domin aikin hajji, kuma duk wanda ya shiga cikinsa; to ya aminta daga duk wani abin ƙi. Allah ya farlanta zuwa wannan Daki domin gabatar da aikin hajji ga duk wanda Allah ya ba shi iko, na lafiya da guziri da abin hawa. Amma duk wanda ya karyata hajji ko ya bijire, to ya sani Allah mawadaci ne, ba ya bukatar hajjinsa, ba ya ma da bukata a wurin dukkan talikai.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Dakin Ka'aba shi ne farkon daki da Allah ya tannade shi a bayan kasa don ibada. Don haka wajibi ne a kan kowane Musulmi ya girmama shi.
  2. Wajibi ne a kan kowane Musulmi da Allah ya hore masa damar zuwa hajji, ya gaggauta zuwa, kada ya yi jinkiri.
  3. Allah cikakken mawadaci ne, ba shi da bukatar komai a wurin halittunsa, amma duk halittunsa mabukata ne a wajensa.
  4. Allah ba ya farlanta wa bayinsa abin da ya fi karfinsu. Duk wani umarni ko hani da Allah zai nemi bawansa da shi to sai idan ya san yana da iko a kansa, idan ba shi da iko; to ya fadi daga kansa.

Tarjama da Tafsirin Aya Ta 98-99

  1. Ka ce: "Ya ku Ma'abota Littafi, don me kuke kafirce wa ayoyin Allah, kuma Allah Mai ba da shaida ne ga abin da kuke aikatawa?" --Quran/3/98
  2. Ka ce: "Ya ku Ma'abota Littafi, don me kuke kange wanda ya yi imani ga hanyar Allah, kuna son ta zamo karkatacciya, kuma ku da kanku masu shaida ne, kuma Allah ba gafalalle ne game da abin da kuke aikatawa ba?" --Quran/3/99

A wadannan ayoyi Allah yana umartar Annabinsa da ya tambayi Yahudawa da Nasara, me ya sa suke musanta hujjojin da Allah ya saukar da su a littattafansu masu dauke da tabbatar da gaskiyar annabcin Annabi da gaskiyar abin da ya zo da shi, tare da sun san cewa babu wani aikinsu da zai buya a wurin Allah? Allah yana ganin duk irin ayyukan da suke yi.

Kuma ya umarce shi da ya kara tambayar Yahudawa, me ya sa suke kokarin batar da muminai daga kan hanyar Allah, suke kuma kokarin su ga wannan hanyar ta gaskiya ta karkace, alhalin sun san gaskiyar, kuma sun san munin abin da suke aikatawa? To su sani Allah ba rafkananne ne game da abin da suke aikatawa ba, yana sane da komai, kuma duk zai yi musu hisabi a kai ranar Alqiyama.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Fito da hakikanin su wane ne Ma'abota Littafi da fito da siffofinsu a fili a gane su. Suna nuna su masu riko da addini ne, alhalin karya suke, sun riga sun kafirce wa wani abu daga littafin Allah na Alkur'ani. Wanda duk ya kafirce wa wani abu daga littafin Allah; to ya kafirce wa littafin ne gaba dayansa. Da a ce sun yi imani da abin da ya zo a cikin littafinsu, to da sun yi imani da duk wani annabi da aka aiko bayan annabinsu. Domin addini a hakikaninsa guda daya ne, wanda duk ya fahimci addinin gaskiya; to duk wani addini da ya zo daga Allah, zai fahimce shi ya karbe shi.
  2. Fadar cewa Allah yana ganin duk abin da suke aikatawa, kuma shi ba rafkananne ne game da ayyukansu ba, wannan shi zai razana ya firgita duk wani mayaudarin mutum, kafiri, batacce mai batarwa.
  3. Hanyar Allah mikakkiya ce ɗoɗar, ba ta da wata karkata ko kadan; duk kuma wata hanya wadda ba ta Allah ba; to karkatacciya ce.
  4. Allah ya zargi masu kange wanda ya yi imani su hana shi bin hanyar gaskiya, tare da cewa sun hana kafirai ma bin gaskiyar, domin karkatar da mumini daga Musulunci zuwa ga kafirci ya fi muni fiye da karkatar da kafiri, domin da ma shi a karkace yake, sabanin mumini wanda shi raba shi da gaskiya aka yi, aka ingiza shi cikin kafirci; wannan kuwa ya fi muni a wurin Allah.