Line 502: | Line 502: | ||
A wadannan ayoyi, Allah yana ba da labarin wasu miyagun mutane ne a cikin Yahudawa da Nasara, wadanda suke ta ƙulle-ƙullen makirci ga Musulmi ta hanyar kawo ruɗu na addini ga wasu raunanan Musulmi. Sun yanke shawara a tsakaninsu cewa, su bayyana imaninsu da abin da Manzon Allah ya zo da shi a farkon yini; idan yamma ta yi kuma su kafirce masa. Yin haka shi zai sa masu raunin [[fahinta]] cikin muminai su rika cewa, da a ce gaskiya ne, da wadanda suka yi imani da shi cikin Ma'abota Littafi, ba su yi ridda ba. Manufarsu ita ce Musulmi su watsar da addininsu gaba daya. | A wadannan ayoyi, Allah yana ba da labarin wasu miyagun mutane ne a cikin Yahudawa da Nasara, wadanda suke ta ƙulle-ƙullen makirci ga Musulmi ta hanyar kawo ruɗu na addini ga wasu raunanan Musulmi. Sun yanke shawara a tsakaninsu cewa, su bayyana imaninsu da abin da Manzon Allah ya zo da shi a farkon yini; idan yamma ta yi kuma su kafirce masa. Yin haka shi zai sa masu raunin [[fahinta]] cikin muminai su rika cewa, da a ce gaskiya ne, da wadanda suka yi imani da shi cikin Ma'abota Littafi, ba su yi ridda ba. Manufarsu ita ce Musulmi su watsar da addininsu gaba daya. | ||
Sannan magana | Sannan magana ta dawo kan tattaunawar Yahudawa a tsakaninsu, da irin yadda suke yi wa junansu wasiyya, yayin da wasunsu sika faɗa wa wasu cewa, kada su yarda da kowa idan ba wanda yake bin addininsu ba, kada kuma su yarda su bayyana sirrinsu ga wani Musulmi don kada ya samu irin ilimin abin da suka samu; idan har sun yi haka to za su koye shi, su ma sai su zama masu ilimi ko kuma su riƙe shi a matsayin abin da za su kafa musu hujja da shi a gaban Allah, sai su ba da shaidar cewa, gaskiya ta bayyana gare su, ƙin bi suka yi. Sai Allah ya ce wa Annabinsa ya faɗa musu cewa, shiriya a hannun Allah take, yana bayar da ita ga wanda ya ga dama daga bayinsa. Kuma Allah mai yalwar falala ne, mai yawan kyauta, kuma mai cikakken sani ne game da wadanda suka cancanci a kyautata musu, don haka yana yin kyautarsa ne ga wanda ya cancanta, ya kuma hana wanda bai cancanta ba kuma yana keɓance wanda ya ga dama da rahamarsa, kuma shi ma'abocin falala ne mai yawa. | ||
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Gargadin Musulmin da ake amfani da su don jefa shakka a cikin zukatan raunanansu, ta hanyar yi wa Musulunci tuhumce-tuhumce iri-iri don a ɓata shi a idon 'ya'yansa, a ɓata tarihinsa da koyarwarsa da nassoshinsa. Ta hanyar sunaye wadannan raunanan mutane suke nuna su Musulmi ne, amma suna taka rawa a gefe guda irin ta Yahudawa. | |||
# Wanda duk ya nemi shiriya ba ta hanyar Alƙur'ani da sunna ba; to ya ɓace, domin babu shiriya sai wadda Manzon Allah ya zo da ita. | |||
# Amfanin ba da labarin wannan makirci na Yahudawa na cewa su yi imani da farkon yini, daga ƙarshensa sai su yi ridda. Amfanin fallasa su shi ne: | |||
## Na daya: wannan shirin nasu sun yi ne a boye, ba wani Musulmi da ya san da shi; to yayin da Manzon Allah ya zo yana ba da labarin wannan sirri nasu, hakan ya nuna cewa lalle shi Manzon Allah ne, domin ya ba da labarin wani abu da ba wanda ya san shi sai Allah da ya sanar da shi. | |||
## Na biyu: Bayan Allah ya fallasa wannan mugun shiri nasu; sai ya zama ba zai yi wani tasiri ba a zukatan muminai, don ba don haka ba, da watakila a ga tasirinsa a wurin wasu masu raunin imani. | |||
## Na uku: Za su ji tsoron kara kulla wani makircin irin wannan bayan Allah ya tona asirinsu. | |||
== Tarjama da Tafsirin Aya Ta 75-76 == | |||
# Kuma daga cikin Ma'abota Littafi akwai wanda in da za ka ba shi amana ta dukiya mai yawa, zai dawo maka da ita, daga cikinsu kuwa akwai wanda idan an ba shi amana ta dinare ɗaya, ba zai dawo maka da shi ba, sai fa idan ka tashi tsaye a kansa. Wannan kuwa saboda sun ce: "Babu wani laifi a kanmu (don mun ci dukiyar) bobayin mutane." Kuma suna fadin karya su jingina wa Allah, alhalin su suna sane. | |||
# Ba haka ba ne, duk wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya tsare dokar Allah, to lalle Allah Yana son masu taqawa. | |||
Bayan Allah ya bayyana mana irin karyar da Yahudawa suke yi na cewa an ba su matsayi na ilimi da addini wanda ba wanda aka ba irinsa, da kuma nuna cewa bin addininsu kadai shi ne shiriya, sai Allah a nan ya karyata su, ya nuna su a matsayin maciya amana, wadanda mu'amalarsu da mutane babu gaskiya a cikinta, kamar yadda mu'amalarsu da Allah ita ma babu gaskiya a cikinta ko kadan. | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |