Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 568: Line 568:


Allah then revealed what Confirmed it." Al-Ash'ath then recited the following Verse:--"Verily! Those who purchase a small gain at the cost of Allah's covenant, And their oaths . . . (to) . . . they shall have a painful torment!' (3.77) (See Hadith No. 546) https://sunnah.com/bukhari:2515
Allah then revealed what Confirmed it." Al-Ash'ath then recited the following Verse:--"Verily! Those who purchase a small gain at the cost of Allah's covenant, And their oaths . . . (to) . . . they shall have a painful torment!' (3.77) (See Hadith No. 546) https://sunnah.com/bukhari:2515
Abdullahi dan Abu Aufa yana cewa: Wani mutum a kasuwa, ya tsaya a kan hajarsa yana rantsuwar cewa, an saya da kudi kaza da kaza, alhalin karya yake, don kawaiya zurma wani Musulmi. Sai Allah ya saukar da wannan ayar. [Bukhari #2088].
Babu cin karo tsakanin ruwayoyin nan guda 2, domin zai iya yiwuwa ayar ta sauka a kan kissoshin biyu.
Sannan Allah ya bayyana wa muminai halin wasu mutane daga cikin Yahudu da Nasara cewa, idan suna karanta littafin da aka saukar musu, sai su rika karkata harshensu suna jirkita wasu lafuzan littafin, suna wasa da ma'anoninsa, da nufin ɓatar da muminai, don su zaci cewa maganar Allah ce abin da suke karantawa, alhalin ba ita ba ce; kawai wannan wata bidi'a ce suka shigo da ita a cikin addini. Da wannan aiki nasu, suna yi wa Allah karya ne tare da suna sani.
Sai kuma Allah ya bayyana cewa, ba abu ne mai yiwuwa ba, Allah ya zaɓi wani mutum, ya ba shi littafi da hikima, ya yi masa baiwar annabci, sannan ya rika kiran mutane kan su bauta masa ba Allah ba. Idan har Allah ya yi wa wasu bayinsa irin wannan baiwa; to zai umarce su ne da su zamo malamai na Allah, masu aiki da iliminsu, masu ikhlasie da bautar Allah, suna koyar da mutane ilimi da tarbiyya ta kwarai, saboda littafin Allah ne suke koyarwa.
[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]