Line 625: | Line 625: | ||
# Sai fa wadanda suka sake tuba bayan haka, kuma suka gyara (ayyukansu), to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. | # Sai fa wadanda suka sake tuba bayan haka, kuma suka gyara (ayyukansu), to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. | ||
A wadannan ayoyi, Allah yana bayyana cewa, ba zai shiryar da mutanen da suka yi ridda ba, suka juya wa MUsulunci baya, alhalin da farko sun yi imani, kuma sun tabbatar da cewa, Annabi Muhammad gaskiya ne, saboda hujjoji bayyanannu, kuma gamsassu, masu ƙara tabbatar da gaskiyarsa. Ta yaya irin wadannan | A wadannan ayoyi, Allah yana bayyana cewa, ba zai shiryar da mutanen da suka yi ridda ba, suka juya wa MUsulunci baya, alhalin da farko sun yi imani, kuma sun tabbatar da cewa, Annabi Muhammad gaskiya ne, saboda hujjoji bayyanannu, kuma gamsassu, masu ƙara tabbatar da gaskiyarsa. Ta yaya irin wadannan za su cancanci shiriya? Allah ba ya shiryar da wadanda suka zalunci kawunansu, ta hanyar barin gaskiya bayan sun fahimce ta, suka kama ƙarya bayan sun gane ƙarya ce a fili. | ||
Sannan Allah ya faɗi uƙubar waɗannan azzaluman a duniya da lahira, wadda ita ce la'anar Allah da mala'iku da duk halittun Allah a kansu, kuma za su ci gaba da zama cikin wannan la'anar, da wannan ukubar, har abada, kuma ba za a taɓa sassauta musu azaba ba, kuma ba za a saurara musu ba. | |||
Amma sai Allah ya yi togaciya ta wadanda suka tuba, suka yi ayyuka na kwarai, kuma suka gyara kurakuren da suka yi; to wadannan Allah yana yafe musu, saboda shi mai yawan gafara ne, mai yawan jin kai ga bayinsa masu tuba su gyara. Abdullahi dan Abbas yana cewa: | |||
"Wani mutumin Madina ya musulunta, | |||
"A man from among the Ansar accepted Islam, | |||
daga baya kuma sai ya yi [[ridda]], ya koma shirka. | |||
then he [[apostatized]] and went back to Shirk. | |||
Sannan ya dawo ya yi [[nadama]], sai ya aika wa mutanensa yana cewa: | |||
Then he [[regretted]] that, and sent word to his people (saying): | |||
'Ku tambayar mini Manzon Allah, shin zan iya sake [[tuba]]?' | |||
'Ask the Messenger of Allah [SAW], is there any [[repentance]] for me?' | |||
Mutanensa suka sami Manzon Allah, suka faɗa masa cewa: | |||
His people came to the Messenger of Allah [SAW] and said: | |||
'Wane da ya yi ridda ya yi nadama, kuma ya aiko mu mu tambaya masa cewa, shin zai iya sake tuba?' | |||
'So and so regrets (what he did), and he has told us to ask you if there is any repentance for him?' | |||
Sai wannan ayar ta sauka: 'Ta yaya Allah zai shiryar da mutanen da suka kafirta bayan imaninsu...' har inda ya ce: '...to lalle Allah mai gafara ne, mai jin kai.' Sai Annabi ya aika masa ya zo ya sake shiga Musulunci." [Nisa'i #4068 da Ahmad #2218]. | |||
Then the Verses: 'How shall Allah guide a people who disbelieved after their Belief up to His saying: Verily, Allah is Oft-Forgiving, Most Merciful' was revealed. So he sent word to him, and he accepted Islam." https://sunnah.com/nasai:4068 | |||
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Ɓacewar mai ilimi ta fi ɓacewar jahili muni. | |||
# Jahili ya fi saurin mika wuya yayin da za a fahimtar da shi abin da bai fahinta ba, amma wanda ya sani ya kangare; to wannan yana da wuya ya dawo kan hanya. | |||
# Tubar bawa ba ta cika, har sai ya gyara barnar da ya yi a baya, ko da ta hanyar bayyana cewa abin da yake kai a baya ɓata ne, don ire-irensa su dawo, su ma su taba. Ko kuma idan ya ja wasu zuwa ga wannan ɓatan; to dole ne ya bayyana musu abin da suke a kai ɓata ne. | |||
# Duk wanda Allah ya yi wa wata ni'ima, sannan ya kafirce masa; to Allah na iya karbe wannan ni'imar daga hannunsa. | |||
# Wanda ya yi ridda, sannan daga baya ya tuba, ya gyaru; to Allah zai karbi tubansa a duniya da lahira. | |||
# Tuba yana kankare laifin da mai tuba ya yi a baya, ko da kuwa kafirci ne. | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |