Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 662: Line 662:
# Yadda imani yake ƙaruwa da ayyuka na ƙwarai, haka shi ma kafirci yake hauhawa da ƙaruwar aikata ayyukan kafirci.
# Yadda imani yake ƙaruwa da ayyuka na ƙwarai, haka shi ma kafirci yake hauhawa da ƙaruwar aikata ayyukan kafirci.
# Tubar mutum ba za ta zama karbabbiya ba a wurin Allah har sai ya bar laifukan da yake aikatawa, ya kuma gyara abin da ya bata a baya.
# Tubar mutum ba za ta zama karbabbiya ba a wurin Allah har sai ya bar laifukan da yake aikatawa, ya kuma gyara abin da ya bata a baya.
#
#Mummunan aiki yana haddasa wani mummuna irinsa, matukar bawa bai dawo kan tafarki madaidaici ba.
#Wanda ya yi ridda ya bar Musulunci har mutuwa ta zo masa bai tuba ba; to ba za a karbi tubansa ba a wannan lokacin.
 
== Tarjama da Tafsirin Aya Ta 92 ==
 
# Ba za ku taɓa dacewa da aiki na alheri ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so, kuma abin da duk kuka ciyar kowane iri ne, to lalle Allah Yana sane da shi.
 
3:92
 
لَن تَنَالُوا۟ ٱلْبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُوا۟ مِمَّا تُحِبُّونَ ۚ وَمَا تُنفِقُوا۟ مِن شَىْءٍۢ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌۭ ٩٢
 
You will never achieve righteousness until you donate some of what you cherish. And whatever you give is certainly well known to Allah.
 
— Dr. Mustafa Khattab, The Clear Quran
 
Never will you attain the good [reward][1] until you spend [in the way of Allāh] from that which you love. And whatever you spend - indeed, Allāh is Knowing of it.
 
— Saheeh International
 
[1]Another meaning is "You will never attain righteousness."
 
Lan tanaloo albirra hattatunfiqoo mimma tuhibboona wama tunfiqoo minshay-in fa-inna Allaha bihi AAaleem
 
— Transliteration
 
Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah, gare shi, Masani ne.
 
— Hausa Translation(Abubakar Gumi)
 
 
Bayan Allah a ayar baya ya yi bayanin cewa, ba zai karbi sadakar kafiri ba, ko da zai ciyar da kwatankwacin cikin duniya na zinari, don ya kuɓutar da kansa daga azabar Allah a ranar alƙiyama, sai a wannan ayar Allah yake kwaɗaitar da muminai kan su ciyar da dukiyarsu, kuma ya bayyana cewa, abin da ya fi son bawa ya yi sadaka da shi, shi ne abin da shi ya fi so; wannan ne zai kai shi matakin samun alheri mai yawa. Allah yana cewa: "Ba za ku kai ga samun alheri mai yawa ba daga Allah, har sai kun yi sadaka da dukiyar da kuke ƙauna a zukatanku. Duk abin da kuka ciyar na dukiyarku; to Allah ya sani, kuma a ranar lahira zai saka wa wanda ya yi haka da cikakken sakamako."


[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]