Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
No edit summary
Line 12: Line 12:


== Tarjama da Tafsirin aya 5-9 ==
== Tarjama da Tafsirin aya 5-9 ==
A wadannan ayoyi
A wadannan ayoyin, Allah yana bayanin [[gamammen]] iliminsa, wanda ya kewaye komai, don babu wani abu da yake [[ɓuya]] a gare shi, a sama yake ko a ƙasa. Shi ne yake halittar ku bisa [[kamanni]] [[daban-daban]] a cikin iyayenku yadda ya ga dama, don haka shi ne kadai ya cancanta a bauta wa; ba shi da wani abokin tarayya. Shi ne Mabuwayi a cikin mulkinsa; ba mai iya ja da shi ko ya fi karfinsa, kuma shi mai hikima ne a cikin ayyukansa da shari'unsa, babu wani tasgaro a cikinsu ko kadan. Shi ne wanda ya saukar wa wannan Annabi Alkur'ani, wanda ya kunshi ayoyin da suke a fili, ma'anoninsu a bayyane suke, babu wani abu mai rikitarwa tare da su, ma'anoninsu a bayyane suke, babu wani abu mai rikitarwa tare da su, su ne kuma tushen wannan littafi, kuma su ne mafiya yawa a cikinsa. A cikinsa kuma akwai wadansu ayoyi wadanda ma'anarsu take da rikitarwa ga wasu mutane. To amma sai a samu wadansu karkatattun mutane masu cutar kauce wa gaskiya a zukatansu, suna bibiyar wadannan ayoyi masu rikitarwa, suna barin ayoyin da ma'anoninsu suke a fili, ba don su sami wani abu da za su kafa hujja da shi a kan soye-soyen zukatansu. Su kuwa wadannan ayoyi masu rikitarwa, babu wanda ya san [[hakikanin]] fassararsu sai Allah. Malamai masu zurfin ilimi na Alkur'ani su ma sukan san tafsirin ma'anonin ayoyin, amma ba za su iya sanin hakikanin al'amarin ba, da yadda karshen zai kasance, domin wannan Allah ne kadai ya san shi. Malamai masu zurfin ilimi sukan shelanta imaninsu da wadannan ayoyi masu rikitarwa. Duk kuma ayoyin na Alkur'ani daga Allah ne, amma ba kowa ne yake wa'azantuwa ba sai masu lafiyayyen hankali.
 
An karbo daga A'isha (rA) ta ce: "Annabi SAW ya karanta wannan ayar, sai ya ce: "Idan kika ga wadanda suke bibiyar ayoyi masu rikitarwa a cikin Alkur'ani; to su ne wadanda Allah ya ambata, don haka ki guje su." (When you see such verses, avoid them, for it is they whom Allah has pointed out (in the mentioned verses)[https://sunnah.com/muslim:2665]). 
[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]