Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
Line 232: Line 232:
# Allah ne mai ba da arziki, shi ne mai hanawa, don haka bawan da ya nema a wajensa, zai samu.  
# Allah ne mai ba da arziki, shi ne mai hanawa, don haka bawan da ya nema a wajensa, zai samu.  
# Duk aikin Allah alheri ne, don haka ba a jingina masa sharri, kamar yadda Manzon Allah ya ce: "Alheri duka yana hannunka, kuma ba a jingina maka sharri."
# Duk aikin Allah alheri ne, don haka ba a jingina masa sharri, kamar yadda Manzon Allah ya ce: "Alheri duka yana hannunka, kuma ba a jingina maka sharri."
==Ayoyi 21-25==
# Lalle wadanda suke kafirce wa ayoyin Allah, kuma suke kashe annabawa ba tare da hakki ba, kuma suke kashe wadanda suke yin umarni da adalci cikin mutane, to ka yi musu albishir da wata azaba mai radadi. --[[Quran/3/21]]
# Wadannan su ne wadanda ayyukansu suka lalace a duniya da lahira, kuma ba su da wasu mataimaka. --[[Quran/3/22]]
# Shin ba ka ga wadannan da aka ba su wani kaso na ilimin Littafi ba, ana kiran su zuwa ga Littafin Allah don Ya yi hukunci a tsakaninsu, sannan sai wani bangare daga cikinsu suna juya baya, suna masu bijirewa.--[[Quran/3/23]]
# Wannan kuwa saboda su sun ce: "Wuta ba za ta shafe mu ba sai a wadansu 'yan kwanaki kididdigaggu." kuma abin da suka kasance suna kirkira a addininsu shi ne ya rude su. --[[Quran/3/24]]
# To yaya halinsu zai kasance idan Muka tara su a wani yini da babu shakka game da shi, kuma kowane rai za a saka masa da abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba? --[[Quran/3/25]]
==Aya ta 26-27==
# Ka ce: "Ya Allah, Kai ne Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Ka ga dama, kuma Kana kwace mulki daga wanda Ka ga dama, kuma Kana daukaka wanda Ka ga dama, kuma Kana kaskantar da wanda Ka ga dama; duk alheri yana hannun Ka, lalle Kai Mai iko ne a kan komai. --[[Quran/3/26]]
# "Kana shigar da dare a cikin yini, kuma Kana shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga cikin matacce, kuma Kana fitar da matacce daga cikin mai rai; kuma Kana arzurta wanda Ka ga dama ba tar da lissafi ba." --[[Quran/3/27]]
==Aya ta 28==
# Kada muminai su riki kafirai a matsayin masoya su kyale muminai; wanda kuwa duk ya aikata haka, to shi ba komai ne ba a wurin Allah, sai dai in don ku kare kanku ne daga gare su. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa. Kuma zuwa ga Allah makoma take. --[[Quran/3/28]]
A wannan aya, Allah ya hana muminai su riki kafirai masoyansu, watau majibinta al'amuransu, suna taimakon su, su yi watsi da 'yan'uwansu muminai. Allah ya bayyana cewa, duk wanda ya yi haka; to babu ruwan Allah da shi. Amma kuma sai Allah ya yi togaciyar lokacin da ake tsoron wani sharrin nasu, to a wannan lokaci za a iya nuna musu kauna da baki, ba da zuciya daya ba, ba kuma tare da taimakon su a kan kafircinsu ko taya su aikata sabon Allah ba.
Sannan Allah ya gargadi muminai game da kansa, watau kada su aikata abin da zai jawo musu fushinsa, yana mai bayyana musu cewa, makomarsu gaba daya zuwa gare shi ne, kuma zai yi musu hisabi a kan ayyukansu.
'''Daga wadannan ayar, za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Ba a shugabantar da wanda ba Musulmi ba a kan al'umma ta Musulmi.
# Ba ya halatta ga mumini ya kudurce kauna da soyayya ta addini ga wanda ba Musulmi ba. Amma kauna ta dabi'a, kamar irin ta d'a da mahaifi, ko miji da mata, wannan babu komai, matukar ba ta kai ga taimaka musu ba kan cutar da Musulmi ko fifita su a kan musulmai.
# 'Taqiyya' tana kasancewa ne tsakanin muminai da kafirai, ba a tsakanin musulmai ba, kamar yadda mabiya addinin Shi'a suka dauka.
==Aya ta 29-30==
# Ka ce: "In za ku boye abin da yake cikin kirazanku ko kuma ku bayyana shi, Allah Ya san shi, kuma Yana sane da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kasa. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai." --[[Quran/3/29]]
# Ranar da kowane rai zai sami sakamakon abin da ya aikata na alheri an halarto da shi, abin da kuwa ya aikata na mummunan aiki, zai so ina ma da a ce tsakaninsa da shi akwai wata tazara mai nisa. Kuma Allah Yana tsoratar da ku kansa, kuma Allah Mai tausayi ne (ArRa'uf) ga bayi. --[[Quran/3/30]]
Allah SWT yana umartar Manzonsa da ya fada wa muminai cewa, ko da za su boye abin da yake cikin zukatansu na alheri ko na sharri, na soyayya ko na kiyayya, ko kuma su bayyana hakan a maganganunsu ko ayyukansu; to Allah ya san da hakan, kuma zai yi musu sakayya a kai; wanda ya shuka alheri ya girbi alheri; wanda kuma ya shuka sharri ya girbi sharri. Allah shi ne wanda iliminsa ya kewaye da duk abin da yake sama da abin da yake kasa, babu abin da yake boye masa, kuma yana da cikakken iko a kan komai, babu abin da zai gagare shi.
Sannan Allah ya bayyana lokacin wannan sakayyar, watau ranar alqiyama, ranar da kowane rai zai ga abin da ya aikata, kadan ne ko mai yawa, an kawo masa shi cikakke, ba tare da tawaya ba, ko wani canji. To amma abin da mutum ya aikata na sharri, zai rika burin ina ma akwai tazara mai nisa a tsakaninsa da mummunan aikinsa. Sai kuma Allah ya sake jaddada tsoratarwarsa da gargadinsa game da kansa, yana mai bayyana cewa, yana yi musu wannan gargadin ne saboda shi mai yawan rahama ne gare su, mai yawan jin kai.
'''Daga wadannan ayoyi, za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Kira zuwa ga tsarkake zukata daga aikata zunubi da halrto da ilimin Allah a ko da yaushe, don bawa ya rika jin kunyar Ubangijinsa, wanda yake ganin ko'ina a zuciyarsa.
# Duk sa'adda mumini ya yi imani da sifar ilimi ta Ubangijinsa, wannan zai gadar masa abubuwa guda biyu:
## Zai guje wa sabon Allah, ba zai yarda Allah ya gan shi a wurin da ya hana shi ba.
## Zai yi kwadayin biyayya ga Allah, ba zai yarda Allah ya rasa shi a wurin da ya umarce shi ba.
# Tuna wa bawa ranar lahira da girman tsorace-tsoracenta, domin abin da bawa ya aikata sai an kawo masa shi a gabansa, an yi masa hisabi a kansa.
# Allah ya kirawo wa'azin da yake yi wa muminai a wannan ayar da suna 'gargadi', watau kashedi, domin ana gargadi ga wanda bai riga ya auka cikin hadari ba, domin a hana shi aukawa cikinsa.
# Allah ya rufe wannan gargadi nasa da fadarsa: "Allah mai jin kan bayi ne," domin yi wa mutum bayanin yadda lamari yake, yana daga cikin anu'i na tausaya masa.
==Aya ta 31-32==


[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]