Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 456: Line 456:
# Ga ku nan ku wadannan kun yi jayayya kan abin da kuke da ilimi a kai, to don me kuma kuke jayayya a kan abin da ba ku da ilimi a kansa? Kuma Allah Yana sane ku ba ku sani ba. --Quran/3/66
# Ga ku nan ku wadannan kun yi jayayya kan abin da kuke da ilimi a kai, to don me kuma kuke jayayya a kan abin da ba ku da ilimi a kansa? Kuma Allah Yana sane ku ba ku sani ba. --Quran/3/66
# Ibrahim bai taɓa zama Bayahude ba, sannan bai taɓa zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin ɓarna ne, Musulmi, kuma bai kasance ɗaya daga cikin mushrikai ba. --Quran/3/67
# Ibrahim bai taɓa zama Bayahude ba, sannan bai taɓa zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin ɓarna ne, Musulmi, kuma bai kasance ɗaya daga cikin mushrikai ba. --Quran/3/67
# Lalle mafi kusancin mutane da Ibrahim su ne wadanda suka bi shi, sai kuma wannan Annabin, da kuma wadanda suka yi Imani. Kuma Allah shi ne Majiɓincin al'amuran muminai.
# Lalle mafi kusancin mutane da Ibrahim su ne wadanda suka bi shi, sai kuma wannan Annabin, da kuma wadanda suka yi Imani. Kuma Allah shi ne Majiɓincin al'amuran muminai. --Quran/3/68

Bayan an kira Ma'abota Littafi zuwa ga addu'ar tsinuwa amma sun ƙi yarda, sannan an kawo musu hujjoji iri-iri wadanda suka nuna bacin addinin da suke kai, sun kuma kasa kare ɓatansu, kuma Allah ya riga ya san yadda Annabi yake maukar tausayin su, yana kwadayin shiriyarsu, sai Allah ya umarce shi da ya kirawo su gaba daya zuwa ga kalma ta bai-ɗaya, wadda kowa da kowa zai daidaita a kanta, kuma za su hada kai a kanta. Wannan kalma ita ce kadaita Allah da bauta, watau kada a bauta wa wani ba shi ba, mala'ika ne, ko wani annabi, ko waliyyi, ko wani gunki. Kada kuma su dauki wasu iayen giji, suna bauta musu ba Allah ba, har su riƙa halatta musu haram ko su haramta musu halal su kuma yarda. To idan sun bijire, sun ƙi yarda da wannan kiran; to ku muminai ku kafa su shaida cewa, ku Musulmi ne, kuma za ku ci gaba da bin wannan addinin da Allah ya zaɓa muku.

Sannan Allah ya fuskantar da maganarsa ga Yahudawa da Nasara cewa, don mene ne suke jayayya game da lamarin Annabi Ibrahim; kowanne yana da'awar cewa a kan addininsa yake, Yahudawa suna cewa shi Bayahude ne, Nasara ma suna cewa shi Banasare ne, alhalin yadda gaskiyar al'amarin take, litafin Attaura da littafin Linjila, ba a saukar da su ba sai bayan mutuwarsa da lokaci mai tsawo. Yanzu ba za su yi aiki da hankulansu ba, su gane cewa, abin da suke fada karya ne? To ga shi yanzu su Yahudu da Nasara suna jayayya a kan abin da suke da ilimi a kansa na al'amarin addininsu, da abin da aka ambata a littafansu. To amma me ya sa zza su rika jayayya a kan abin da ba su da ilimi a kansa na lamarin Annabi Ibrahim, da addinin da ya rayu a kansa? Allah kam iliminsa ya kewaye komai, ya san abin da su ba su sani ba, amma su ba su san komai ba daga abin da Allah ya sani.
Sannan Allah ya fuskantar da maganarsa ga Yahudawa da Nasara cewa, don mene ne suke jayayya game da lamarin Annabi Ibrahim; kowanne yana da'awar cewa a kan addininsa yake, Yahudawa suna cewa shi Bayahude ne, Nasara ma suna cewa shi Banasare ne, alhalin yadda gaskiyar al'amarin take, litafin Attaura da littafin Linjila, ba a saukar da su ba sai bayan mutuwarsa da lokaci mai tsawo. Yanzu ba za su yi aiki da hankulansu ba, su gane cewa, abin da suke fada karya ne? To ga shi yanzu su Yahudu da Nasara suna jayayya a kan abin da suke da ilimi a kansa na al'amarin addininsu, da abin da aka ambata a littafansu. To amma me ya sa za su rika jayayya a kan abin da ba su da ilimi a kansa na lamarin Annabi Ibrahim, da addinin da ya rayu a kansa? Allah kam iliminsa ya kewaye komai, ya san abin da su ba su sani ba, amma su ba su san komai ba daga abin da Allah ya sani.

Allah kuma ya bayyana musu gaskiyar al'amarin Annabi Ibrahim ya karyata maganar cewa shi Bayahude ne, ko Banasare. Allah ya tabbatar da cewa, Annabi Ibrahim tsaye yake ƙyam a kan addinin gaskiya, ba ruwansa da duk wata barna da shirka, yana bin umarnin Allah cikin ikhlasi, kuma ba ya cikin masu hada Allah da wani, masu bautar gumaka.

Sannan Allah ya ambaci wadanda suka fi cancantar su zama tare da Annabi Ibrahim, ya bayyana cewa, su ne wadanda suka bi addininsa, suka kuma bi hanyarsa ta kaɗaita Allah a wajen bauta, wadanda su ne Annabi, da sahabbansa, da muminai da za su zo bayansu. To wadannan su suka fi cancanta su zama masoyansa, majibintansa, kuma Allah shi ne yake jibintar lamarin muminai, ya taimaka musu, ya ba su nasara a kan abokan gabarsu.
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Ya kamata Musulmi ya rika alfahari da cewa, shi Musulmi ne a ko'ina, kuma a gaban kowane ne. Ba kamar yadda wasu raunanan Musulmi suke jin kunyar su ce su Musulmai ne a gaban wadanda ba Musulmai ba.
# Adalci yayin tattaunawa da wanda ba Musulmi ba dole ne, balle kuma tare da wanda yake Musulmi ne.
# Amfanin karantar tarihi, domin zai taimaka wajen rushe ƙarairayi da dama waɗanda suka saɓa wa abin da ya tabbata a tarihi.
# Kafa hujja da hankali a kan gaskiya, kuma duk wani lafiyayyen hankali idan mai shi ya yi amfani da shi; to zai kai shi ga fahimtar gaskiya. Sai dai ba daidai ba ne mutum ya dogara a kan hankalinsa gaba daya, ya watsar da nassi.
# Imani shi ne musabbabin jibinta ta Ubangiji ga bawansa.

[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]