Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 740: Line 740:
# Martani ga Yahudawa masu karyata samuwar shafe hukunci a sharia, wato naskhu.
# Martani ga Yahudawa masu karyata samuwar shafe hukunci a sharia, wato naskhu.
# Umartar su da su dauko Littafin Attaura su karanta, wata hanya ce ta kafa wa abokin husuma hujja da abin da ya yi imani da shi kuma ya yarda da shi, wadda ba ta yadda zai iya kauce mata.
# Umartar su da su dauko Littafin Attaura su karanta, wata hanya ce ta kafa wa abokin husuma hujja da abin da ya yi imani da shi kuma ya yarda da shi, wadda ba ta yadda zai iya kauce mata.
#  
#Umartar su da cewa su karanta su da kansu, bai ce 'mu karanta' ba, domin idan da Musulmi ne za su karanta, suna iya cewa ba su yarda ba, su rika tuhumar Musulmi cewa sun yi kari ko ragi a cikin karatun. Don haka su suka karanta da kansu, suka kuma ga gaskiyar a fili.
#Kira zuwa ga bin gaskiya, domin duk sa'adda gaskiya ta bayyana a fili, kuma mutum ya kauce mata; to wannan ya tabbata babban azzalumi. Domin babu zaluncin da ya kai a kirawo shi zuwa ga hukunci da Littafin Allah, sannan ya bijire, saboda girman kai da kangara.
#Mayar da martani ga Yahudawa masu da'awar suna bin addinin Annabi Ibrahimu, amma kuma suna jayayya da Musulmi a kan an halatta musu wasu abubuwa da su aka haramta musu a cikin Littafin Attaura. Domin ai addinin Annabi Ibrahimu bai haramta abubuwan da su aka haramta musu su a cikin Attaura ba. Don haka Musulmi su ne masu bin Addinin Annabi Ibrahimu na gaskiya.
 
== Tarjama da Tafsirin Aya Ta 95-97 ==
 
# Ka ce: "Allah Ya yi gaskiya. Don haka ku bi addinin Ibrahimu, mai karkace wa barna, kuma bai taba zama daya daga cikin mushirikai ba." --Quran/3/95
# Lalle farkon daki da aka tanada don mutane (su yi ibada a cikinsa) shi ne wanda yake cikin Bakka, (daki ne) mai albarka, kuma shiriya ne ga talikai. --Quran/3/96
# A cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, (kuma akwai) Maqamu Ibrahim; wanda duk ya shige shi ya zama amintacce. Kuma lalle Allah Ya wajabta wa mutane ziyarar wannan dakin ga wanda ya sami iko. Wanda kuwa ya kafirce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin talikai. --Quran/3/97
 
A wadannan ayoyi, Allah yana umartar Annabi SAW da ya ce wa Yahudawa, duk abin da Allah ya labarta ko ya shar'anta na hukuncil to gaskiya ne, kamar abin da ya fada musu cewa, babu wani abin da Allah ya haramta musu kafin saukar da Attaura, sai nau'i biyu (2), watau naman rakumi da nonansa. Don haka su zo su bi addinin Annabi Ibrahimu Alaihissalam, idan har su masu gaskiya ne game da tutiyar su ta cewa su jikokinsa ne' domin shi mai kadaita Allah ne, ba ya shirka, ba ya kuma tare da masu yin ta.


[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]