Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 791: Line 791:
A wadannan ayoyi Allah yana umartar Annabinsa da ya tambayi Yahudawa da Nasara, me ya sa suke musanta hujjojin da Allah ya saukar da su a littattafansu masu dauke da tabbatar da gaskiyar annabcin Annabi da gaskiyar abin da ya zo da shi, tare da sun san cewa babu wani aikinsu da zai buya a wurin Allah? Allah yana ganin duk irin ayyukan da suke yi.
A wadannan ayoyi Allah yana umartar Annabinsa da ya tambayi Yahudawa da Nasara, me ya sa suke musanta hujjojin da Allah ya saukar da su a littattafansu masu dauke da tabbatar da gaskiyar annabcin Annabi da gaskiyar abin da ya zo da shi, tare da sun san cewa babu wani aikinsu da zai buya a wurin Allah? Allah yana ganin duk irin ayyukan da suke yi.


Kuma ya umarce shi da ya kara tambayar Yahudawa, me ya sa suke kokarin batar da muminai daga kan hanyar Allah, suke kuma kokarin su ga wannan hanyar ta gaskiya ta karkace, alhalin sun san gaskiyar, kuma sun san munin abin da suke aikatawa?  
Kuma ya umarce shi da ya kara tambayar Yahudawa, me ya sa suke kokarin batar da muminai daga kan hanyar Allah, suke kuma kokarin su ga wannan hanyar ta gaskiya ta karkace, alhalin sun san gaskiyar, kuma sun san munin abin da suke aikatawa? To su sani Allah ba rafkananne ne game da abin da suke aikatawa ba, yana sane da komai, kuma duk zai yi musu hisabi a kai ranar Alqiyama. 
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Fito da hakikanin su wane ne Ma'abota Littafi da fito da siffofinsu a fili a gane su. Suna nuna su masu riko da addini ne, alhalin karya suke, sun riga sun kafirce wa wani abu daga littafin Allah na Alkur'ani. Wanda duk ya kafirce wa wani abu daga littafin Allah; to ya kafirce wa littafin ne gaba dayansa. Da a ce sun yi imani da abin da ya zo a cikin littafinsu, to da sun yi imani da duk wani annabi da aka aiko bayan annabinsu. Domin addini a hakikaninsa guda daya ne, wanda duk ya fahimci addinin gaskiya; to duk wani addini da ya zo daga Allah, zai fahimce shi ya karbe shi.
# Fadar cewa Allah yana ganin duk abin da suke aikatawa, kuma shi ba rafkananne ne game da ayyukansu ba, wannan shi zai razana ya firgita duk wani mayaudarin mutum, kafiri, batacce mai batarwa.
# Hanyar
[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]