#
|
English [1]
|
Hausa [2]
|
Vocab
|
1
|
Operation Al Aqsa Flood: An attack that jolted the world out of its slumber
|
Operation Al Aqsa Flood: Harin da ya farkar da duniya daga barcinta - TRT Afrika
|
- jolt [3]: ya farkar da, girgiza
|
2
|
Hamas’ ‘Al Aqsa Flood’ operation will forever be considered a turning point [4] in the contemporary history of the Palestinian resistance movement.
|
Harin da Ƙungiyar Hamas ta kai kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, za a ci gaba da ɗaukar shi a matsayin abin da ya sauya al'amurra a tarihin baya bayan nan, na ƙungiyar fafutikar ta Falasdinawa.
|
- op [5], operation: hari
- turning point: matsayin abin da ya sauya al'amurra
- contemporary: baya bayan nan
- movement: ƙungiya
- resistance: fafutikar
- considered: ɗaukar abu a wani matsayi, kallon abu da wani ra'ayi
|
3
|
Planning and executing such an operation targeting the world’s most technologically advanced military state is not a small feat considering Hamas’ limited resources.
|
Tsarawa da kuma aiwatar da irin wannan harin a kan ƙasar da sojojinta suka fi kowaɗanne cigaban fasahar zamani a duniya, ba ƙaramin aiki ba ne, idan aka yi la'akari da ƙarancin kayan aiki da Hamas ke fama da shi.
|
- planning: tsarawa
- advanced: fin cigaba
|
4
|
The attack has shattered the myth and image of Israel as an impenetrably strong state.
|
Harin ya kawar da shaci-faɗi da kuma kallon da ake yi wa Isra'ila, a matsayin ƙasa mai ƙarfin da ba za a iya kai mata hari ba.
|
- myth: shaci-faɗi
- image: kallon da ake yi wa abu
- impenetrable: abin da ba za iya kai wa hari ba ko wucewa ba.
|
5
|
The October 7 attack was not the starting point of the Israel-Palestine conflict. There are reasons why the Palestinian resistance group took the historic decision to launch this unprecedented operation.
|
Harin na 7 ga watan Oktoba, ba shi ne mafarin rikicin Isra'ila da Falasdinawa ba. Akwai dalilai da suka saka ƙungiyar fafutikar ta Falasdinawa ta yanke shawarar mai cike da tarihi, ta ƙaddamar da wannan harin da ba kasafai ake ganin irinsa ba.
|
- starting-point [6]: mafari
|
7
|
Among them are Israel’s ethnic cleansing and genocide it perpetrates against the Palestinian people, the severe human rights violations committed by Israeli occupation forces, Israel’s seizure of Palestinian lands, and, more importantly, the continuous Judaisation of Jerusalem and the Al Asqa Mosque complex.
|
Daga cikinsu akwai kisan ƙare-dangi da kisan-kiyashi da Isra'ila ke yi wa al'ummar Falasdinawa, mummunan take haƙƙin bil adama da sojojin mamaya na Isra'ila ke yi, da ƙwace yankunan Falasdinawa,da kuma mafi muhimmanci, ci gaba da mamayar da Yahudawa ke yi wa Birnin ƙudus da kuma masallacin Birnin Ƙudus.
|
- ethnic cleansing: kisan ƙare-dangi
- genocide: kisan kiyashi
|
8
|
|
|
|