- Name: This Surah takes its name, An Nur, from verse 35. <> Sunanta: Wannan Sura ana kiran ta ne da 'Suratun Nur' tun zamanin Manzon Allah ﷺ. Hakanan sunanta yake a cikin bugun Alƙur'ani da littattafan tafsiri da na hadisi. Ba ta da wani suna biyu.
- Revelation place: Medina <> Sanda aka saukar da ita: Duk malamai ra'ayinsu ya haɗu a kan cewa wannan Sura Madaniyya ce, watau an saukar da ita ne bayan hijirar Annabi ﷺ.
- Jerin Saukarta: Ita ce Sura ta ɗari (100) a jerin saukar surorin Alƙur'ani, ta sauka bayan Suratun Nasri gabanin Suratul Hajji a ra'ayin masu ganin Suratul Hajji Madaniyya ce.
- Adadin ayoyinta: a lissafin mutanen Madina da Makka sittin da biyu ne (62), amma a lissafin sauran malamai sittin da huɗu ne (64).
- Babban jigonta: Babban jigon wannan Sura shi ne ƙoƙarin tabbatar da tarbiyya a cikin al'ummar Musulmi ta hanyar kame kai da nisantar duk abubuwan da za su lalata kyakkyawar tarbiyya da zamantakewar al'umma da umarni da duk abubuwan da za su gyara halaye da tsaftace zukata.
- Daga cikin abubuwan da ta ƙunsa akwai:
- Bayanin hukuncin mazinaci da mazinaciya.
- Hukuncin yi wa Musulma kamammiya ƙazafi.
- Hukuncin li'ani tsakanin ma'aurata biyu.
- See also Category:Quran/24