Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

sandbox1

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 18:37, 30 July 2017 by Admin (talk | contribs)

ƁɓƊɗƘƙƳƴ Notes to self

cika-saura

==Noun== m

  1. wani irin tsiro mai 'ya'ya masu kacau-kacau. <> a plant with dangling fruits.
  2. adon da ake yi wa doki a goshi mai kacau-kacau. <> horse adornment.
  3. wani irin abu mai kacau-kacau wanda 'yan rawa kan sa a ƙafa.

cikashe

  1. REDIRECT cikasa

cikasu

  1. REDIRECT cikasa

cika-teku

cika+teku

  1. kalma mai nuna yawan abu musamman kudi.

cika-zube

==Noun== m

  1. cinikin furfure wanda za a ba da hatsi daidai cikin tukunyar da za a yi musaya da ita.

cike

See also cika
  1. filled-up, fill, completed.

cikilkishe

==Verb==

  1. cunkushe, cukurkushe, cikinkine <> get out of hand, overwhelm.
    Aiki ya masa cikilkishe.

cikinkine

  1. cunkushe, cikilkishe

cikin-kishiya

==Noun== m

  1. tarnaƙi.
  2. yaudara ko cuta ko zamba. <> cheating, deception.
  3. rashin dahuwa sosai. <> not fully cooked.
  4. aikin da bai yi kyau ba. <> badly done work.
  5. wata tufa mai fari da baƙi. <> a black and white piece of clothing.

cikirkishe

  1. REDIRECT cinkishe

cukurkushe

  1. REDIRECT cinkishe

cikirkita

==Noun== f

  1. wata irin kaza mai gashi butsatsa.

cikisa

  1. cusa

ciko

==Noun== m

  1. outstanding or leftover balance. cikon kudi = subsidy.
  2. ƙarashi. <> A filling up, a filling in, balance.
    1. ciko kaza ya biyo ka <> there is a balance of so much against you.
    2. ya ba ni cikon (cikwan) uku <> he made up the balance by giving me the remaining three.
  3. toshe wani abu musamman rami. <> plugging or fill-in a hole.
  4. abin da ake toshe rami da shi. <> a (hole) plug.
  5. (Grammar) complement.
  6. sayen kaya don sayarwa a wani wuri. <> buy to resale. Buying to sell again at another place, or to put aside till market prices have risen. {pl. cike-cike}.
  7. sayen abinci mai yawa irin wanda saurayi ya ga budurwarsa na ci a hanya ya aika mata gidansu. <> when a boyfriend buys something in bulk that he saw his girl likes. Buying a large amount of any food which a young friend of the opposite sex has been seen eating in public and sending it as a present to the offender.
  8. cikon gari = banzar gari.

==Noun 2==

  1. wani irin askin kwaskwas wanda ake tara suma da yawa a gaban goshi. <> a hairstyle where a long strand of hair is left accumulated on the forehead. a comb over, men's hair style combed forward to point over the forehead.
  2. A kind of embroidery (satin stitch). (= gidan rina.)
  3. (Kats.) A charm to make a person invulnerable.

II. [ci+ko/+] (v.intr.3d). Swell up through expansion. e.g.

  1. (a) tukunya ta ciko <> (i) the pot has become full, e.g. with some food, such as rice, which swells up considerably when cooking. (ii) the pot is very nearly full.
  2. (b) k'urji ya ciko <> the ulcer has started healing up well from the base. (= cike.)
  3. (c) rijiya ta ciko <> the well has an increased depth of water in it.
  4. (d) kogi ya ciko <> the river is in flood. (verbal noun of cika)

cikowa

==Noun== f

  1. crowding, overcrowding.

cikoko

==Noun== m

  1. wani irin kacau-kacau.
  2. ɗan giginya. <> Small, late, nutless fruit of the fan palm. (Vide giginya.)

cilakowa

==Noun==

Tilo
cilakowa

Jam'i
babu (none)

Singular
hornbill

Plural
hornbills

f

  1. wani irin tsuntsu mai jan baki.
  2. wani irin ƙarfe wanda ake yin zanen fata da shi.

ciku

  1. cika <> filled.
    Bankin ya ciku da mutane. <> The bank was filled with people.
  2. cikwi

cikwi

==Noun== m

  1. auduga maras daraja. <> low-quality cotton.
  2. wani irin abinci da ake yi da madara, musamman ta raƙuma. <> food made with milk (especially that of a camel's milk).

cikunkuna

==Noun==

Tilo
ciki

Jam'i
cikunkuna or cikuna

Singular
stomach

Plural
stomachs

  1. The plural form of ciki; more than one (kind of) ciki. <> stomachs.

cikuna

==Noun==

Tilo
ciki

Jam'i
cikunkuna or cikuna

Singular
stomach

Plural
stomachs

  1. The plural form of ciki; more than one (kind of) ciki. <> stomachs.

cikuri

  1. REDIRECT cilakowa

cikwikuya

==Verb== cikwikuya | cikwikuye | cikwikuyi | cikwikuyu

  1. kanannaɗa ko cakuma. <> grab clothes.
    Ya cikwikuya rigarsa. <> He grabbed his shirt.

cikwikuye

  1. REDIRECT cikwikuya

cikwikuyi

  1. REDIRECT cikwikuya

cikwikuyu

  1. REDIRECT cikwikuya

ci ƙadangaru

  1. REDIRECT ci-ƙadangaru

ci kadangaru

  1. REDIRECT ci-ƙadangaru

ci-kadangaru

  1. REDIRECT ci-ƙadangaru

ci-ƙadangaru

==Noun== m

  1. wani irin shaho wanda aka fi samu a arewacin Afrika. <> a type of hawk mostly found in South Africa.

cilakko

  1. REDIRECT cilakowa

cilalu

==Noun== m

  1. wani irin doki mai launin ƙasa-ƙasa. <> a dark brown horse.
  2. A dark dun horse. (= shirwa.)

cilando

==Noun== m

  1. wasan yara na yin fatan ruwan sama zai sauko. <> a kid's game of hoping for rain to fall.

cile

==Noun== m

  1. ƙarshen abu ko ragowa, kamar rake ko rogo ko taba. <> left over food or something such as sugar cane or cigarette buds/ends. Also applied to ends of cassava, etc.
  2. masha cile; mai cin suɗi. <> A cadger of small things. (Cf. 'dan gwazai.)
    1. cile ya ke ci <> he lives on the leavings of others.

cili

==Noun== m

  1. {n.m.}. The boundary marks of a proposed new farm. <> iyakar sabuwar gona.

cililliga

==Noun== m

  1. fatar kunne. <> ear skin, earlobe. The lobe of the ear.
  2. 'yan kunne. <> earrings. Any kind of ear-ring. (= lallaga kunne.)
  3. ƙirinjijiya
  4. A keloid on upper eyelid or supra-orbital region. (= cira IV.)
  5. k'yali q.v.

cilindo

  1. REDIRECT cilando

cilindugum

==Noun== m

  1. ana amfani da shi kamar: gari ya yi cilindugum ; wato...
    1. an tabka ruwa tun safe har dare.
    2. halin da mutum ya faɗa na rashin kuɗi.
  2. Sandbox1 is another way of spelling cilundugum.

cilingoro

==Noun== m

  1. turakun gado wanda aka yi da yumɓau.

cilla

==Verb== cilla | cilli | cillu | cillo (hurled, threw) | cille

  1. harba abu da ƙarfi. <> to hurl, fire, shoot a long way.
    1. Ya cilla kibiya. <> He shot an arrow.
  2. ƙwalla. <> blast-off, yell out, scream.
    1. Ya cilla ihu. <> He screamed loudly.
  3. To rush-off. <> ruga ko zura
    1. Ya cilla a guje. <> He rushed-off.

cilleru

  1. kule

cilli

==Noun== m

  1. a boy's uncircumcised penis. <> loɓar yara.
  2. gurbin da ruwa ke taruwa a tsakiyar rijiya in ruwa ya ƙafe.

cillo

See also cilla
  1. hurled, threw.

cilmi

==Noun== m

  1. {n.m.}. The cover for the mouth of a churn. <> murfin gora.
    Ɗan cilmi

cilundugun

==Noun== m

  1. {n.m.}. Raining hard all day in the height of the wet season. e.g. gari ya yi cilundugun. (= cilindugun; culungudun; tsulungudun.)

cilunko

  1. REDIRECT cilakowa

cim

==Verb==

  1. fulfill, reach, attain, accomplish. <> iske ko taras; ana haɗa shi da ma:
    Ya cim ma burinsa. <> His dream was fulfilled.
  2. {v. invariable; always followed by ma}. overtake. e.g.
    1. na cim ma Audu a hanya; na cim masa. (= tarad da.)
  3. {n.m}. (Z.) A small quantity. e.g.
    ya ba ni cim <> he gave me a little.

cima

==Noun== f

  1. abinci. <> (staple) food.
    1. tafo, ga irin cimarka. <> come and see the kind of thing you eat.
    2. doya, cimar mutanan kudu, <> yam, the food of southerners!
    3. nama, cimar zaki, <> flesh, thou food of the lion!
    4. Ita cimar Audu ce. <> She's Audu's type of woman.
  2. sarkin gida. <> {n.m.}. (A Barebari word, but common in Daura.) A person put in charge of house and possessions by a house-holder. (= moyi.)
  3. wani irin abin yankan dawa. <> An instrument for cutting off the heads of cut corn.

cimaɗa

  1. damu, tsangwama. <> {n.f.; 4e of no.1}. pestering.
  2. {v.tr.1e}. to pester, annoy. (= dami.)

cimada

  1. REDIRECT cimaɗa

cima'da

  1. REDIRECT cimaɗa

ci maɗauki

==Noun== m

  1. ya da kai.
  2. {n.m.}. pestering. e.g.
    ci maɗauki gare shi.

cimaka

  1. REDIRECT cima

cimau

==Noun== f

  1. wata irin kanwa. <> A kind of potash (the water-soluble part of the ash formed by burning plant material; used for making soap, glass and as a fertilizer).

ci-ma-zune

f / m

  1. malalacin mutum.

cimbi

  1. ganji.

shackles

==Noun==

Singular
shackle

Plural
shackles

Tilo
takunkumi

Jam'i
takunkumai

  1. The plural form of shackle; more than one (kind of) shackle. <> takunkumi.
    Let me free you of these shackles. <> Bari na kwance ma wannan takunkumin.

==Verb==

Plain form (yanzu)
shackle

3rd-person singular (ana cikin yi)
shackles

Past tense (ya wuce)
shackled

Past participle (ya wuce)
shackled

Present participle (ana cikin yi)
shackling

  1. The third-person singular form of shackle.

cimbulum

==Noun== m

  1. ƙwari masu lalata kabewa ko rogo da sauransu. <> insects or other organisms harmful to cultivated plants or to animals.

cimbilu

==Noun== m

  1. cim baya; cim mutunci.
  2. wata irin cutar shanu. <> E. Coli. mad cow disease. the cattle disease black-quarter.

cimbus

==Adverb==

  1. {adv.}. In dense mass. e.g. pustules, germinated seed. <> kalma mai nuna yawan abu.

cimcimtu

==Noun== m

  1. tuɓe riga a sassauto ta a ɗaure a gindi kamar yadda 'yan-kama ke yi. <> Letting a garment slip from the shoulder and securing it round the waist.

cimfa

  1. REDIRECT cirin

cimma

==Noun== m

  1. {n.m.}. Brackish water. (= ruwan zartsi.)

cimmanta

==Verb==

  1. abu ya ragu ko ya ƙanƙance. <> reduce, shrink.

cimola

==Noun==

Tilo
cimola

Jam'i
cimololi

f

  1. wata tsuntsuwa mai dogon wuya da baki.

cimra

  1. cura.

cin arabi

  1. zalunci.

cin baki

==Noun== m

  1. goatskin lining around the hole on a garaya lute.
  2. kalmasa ko ɗinkin da ake yi wa gefen zane ko tabarma.

ci naka

==Noun== m

  1. askar yin shasshawa. <> {n.m.}. A tattooing knife. (= bera.)

cin baya

==Noun== m

  1. backbiting, backbite. <> munafunci ko gulma.

cinci

  1. REDIRECT cici

cincim

  1. tinjim

cincime

  1. ƙaƙaya.

cincin

==Noun== m

  1. wani irin abinci da ake yi da garin fulawa a haɗa da ƙwai da sukari a soya cikin mai. <> small crunchy cupcake pastries or doughnuts.
    1. cincin mai sukari <> sweet cupcake.
    2. cincin nama <> meat pie.
  2. matuƙa

cincingiri

  1. cecekuce

cincirindo

==Noun== m

  1. taruwar jama'a da yawa a wuri guda. <> a large crowd, gathering of large numbers in one place.
  2. dense crowd of people causing congestion; a collection of horses; a swarm of flies.

cin-dawo

==Noun== m

  1. wasan gasa da ake yi tsakanin 'yan matan amarya da ango. <> a wedding game between the bridesmaids and groomsmen.

cindo

==Noun== m

  1. ƙarin ɗan yatsa a hannu ko a ƙafa. <> a sixth or additional (usually deformed) finger.
  2. A person with such finger.

Cindo

==Proper Noun==

Proper noun
sandbox1

f / m

  1. laƙabin da ake yi wa mutum mai 'yan yatsu shida. <> Given name of a person with six fingers.