Verb
Plain form |
Third person singular |
Simple past |
Past participle |
Present participle |
- faɗi, faɗuwa, faɗo, faɗa
- sauka, sauko/sakko, yi ƙasa, raguwa
- Before the first rain falls. <> Kafin ruwan fari ya sauko.
- The prices have fallen. <> Farashi ya sakko.
- The rise and fall of prices. <> Hawa da saukar farashi.
- His work has fallen off. <> Kyan aikinsa ya ragu.
- to fall in disgrace <> ɓata kai
- to fall into difficulty. <> shiga wahala
- fall off <> faɗo daga, ɓalla
- The book fell off the shelf. <> Littafin ya faɗo daga kanta.
- (of hair, leaves) fall out of something <> zuba/zubewa, faɗo daga cikin wani abu
- They all fell out of the canoe. <> Dukansu sun faɗo daga cikin kwalekwale.
- (of time) fall on... <> kama
- Sallah falls on Monday. <> Hutun Sallah ya kama ran Litinin.
- (attack) fall upon something/someone <> faɗa/far wa
- Suddenly, the lion fell upon the goat. <> Nan da nan, sai zakin ya far wa akwiyar.
- (come apart) fall apart <> ruguje, ɓaɓɓalle, wargaje
- fall asleep <> yi barci
- fall behind <> bari a baya
- I've fallen behind in my payments <> An bar ni a baya wajen biyan bashi.
- fall short <> yi ƙasa, kasa, gaza
- The rain falls short every year. <> Ruwan sama yakan yi ƙasa kowace shekara.
- The money fell short. <> Kuɗin sun gaza.