1-5
- Alif Lam Mim. --Quran/2/1
- Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa. --Quran/2/2 3. Wadanda suke yin imani da abin da galibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. 4. Wadanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira. 5. Wadannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo.