Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/093 Tim Apple backlash

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
<small> --[[bbchausa_verticals/093_Tim_Apple_backlash]]</small>
Apple boss Tim Cook faces backlash to £73m pay package [1] Shugaban Apple na shan suka kan yawan albashinsa na dala miliyan 99 [2] [3]
1. Investors are being urged to vote against a $99m (£73m) pay package awarded to Apple boss Tim Cook last year. An bukaci masu hannun jari a kamfanin da su kada kuri'ar kin amincewa da albashin dala miliyan 99 (£73m) da aka yanka wa shugaban kamfanin na Apple Tim Cook a shekarar da ta wuce.
2. Institutional Shareholder Services (ISS) said it has "significant concerns" over the size of the award, up from $14.8m the year before. Hukumar da ke kula da harkokin hannun jari (ISS) ta ce tana da damuwa sosai a kan yawan albashin da aka sanya wa shugaban wanda aka kara daga dala miliyan 14.8 a shekarar bara ta 2021.
3. Mr Cook, whose net worth is reportedly more than £1bn, received the pay in shares, salary, and for other costs. Ana biyan Mista Cook, ne wanda arzikinsa jumulla ya kai sama da fam biliyan daya, wannan kudi ta hanyar hannun jari da albashi da kuma daukar dawainiyarsa ta wasu hanyoyin.
4. The BBC has contacted Apple for comment. BBC ta tuntubi kamfanin na Apple domin jin martaninsa.
5. In a letter to shareholders, the ISS said there are "significant concerns" over the "design and magnitude" of the package. A wata wasika da hukumar ta ISS ta aika wa masu hannun jari, ta ce akwai damuwa sosai a kan tsari da kuma girman albashin,
6. "Half of the award lacks performance criteria," ISS said. inda kusan rabin albashin ba shi da alaka da kwazon ko aikin shugaban.
7. Mr Cook, 61, who has often spoken publicly about his concerns over equality and human rights issues, said in 2015 that he would give away his entire fortune before he dies. Mista Cook, mai shekara 61, wanda yake yawan magana a fili a kan damuwarsa kan 'yancin dan-Adam, a 2015 ya ce zai bayar da dukiyarsa gaba daya kafin ya mutu.
8. According to ISS, Mr Cook's pay was 1,447 times more than the wage of an average Apple employee. Hukumar kula da harkokin hannun jarin ta ce albashin Mista Cook, ya ninka albashin yawancin ma'aikatan kamfanin na Apple sau 1,447.
9. His package included $630,600 in personal security costs and $712,500 for personal use of a private jet. Albashin ya hada da dala $630,600 ta masu tsaron lafiyarsa da dala $712,500 ta amfani da jirgin sama na musamman.
10. ISS said the cost of such perks "significantly exceeded" comparable companies last year. Hukumar ta ISS ta ce wadannan kudade sun zarta na wasu kamfanoni sosai, a shekarar da ta gabata.
11. Last year, a US Securities and Exchange Commission (SEC) filing showed that Mr Cook donated almost £7.4m worth of Apple shares to charity, without naming the recipient. A shekarar da ta wuce bayanan hukumar kula da hannun jari ta Amurka ta nuna cewa Mista Cook ya bayar da tallafin kusan fam miliyan 7.4 na hannun jarin kamfanin na Apple, mallakinsa ga wata kungiyar agaji, wadda ba a bayyana sunanta ba.
12. The company behind the iPhone, iPad and MacBook became the first company to hit a $3tn (£2.2tn) stock market value in January before dipping to its current value of $2.8tn (£2.1tn). Kamfanin Apple, wanda ke yin iPhone da iPad da MacBook ya kasance na farko da darajar hannun jarinsa ta kai dala tiriliyan 3 a watan Janairu kafin darajar ta yo kasa zuwa yadda take a yanzu dala tiriliyan 2.8.
13. Apple is due to hold its annual meeting for shareholders in the first week of March. However, shareholder votes are only advisory, while Apple's board decide on pay packages. Kamfanin yana sa ran gudanar da taron shekara-shekarar na masu hannun jarinsa a makon farko na watan Maris. Sai dai kuma kuri'ar masu hannun jari shawara ce kawai, hukumar gudanarwar kamfanince ke da ta cewa a kan albashi.
14.