<small> --[[bbchausa_verticals/098_dealing_with_bandits_is_a_must]]</small>
# |
Yarjejeniya da barayin daji ta zamar mana dole [1] | Dealing with bandits is a must |
---|---|---|
1 |
"Kusan barayin daji ne ke da iko a gaba dayan yankin" | "Thieves are in control of the whole area." |
2 |
in ji wani shugaban matasa na ynkin karamar hukumar Shiroro ta jihar Naija | said a youth leader of Shiroro Local Government Area (LGA) of Niger State. |
3 |
Ga alama al'ummomin wasu garuruwa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Naija a Najeriya za su ci gaba da yarjejeniyar biyan 'yan bindiga domin su samu damar yin noma a bana.
Tun a bara ne dai jama'ar wasu kauyuka na yankin karamar, suka fara gwada wata yarjejeniya da ta kunshi bayar da kudi ko babura ko kayan abinci ko na masarufi da dai sauransu ga 'yan bindigan da suka addabi yankin. Su kuma 'yan bindigan su tsahirta wa mutanen komawa kauyukansu, don su yi aikin gona da damina, kuma su yi girbi a lokacin kaka. BBC ta tattauna da wasu daga cikin mazauna wadannan kauyuka domin jin yadda za su yi a wannan lokaci da damuna ke kamawa. Shugaban kungiyar matasan yankin na shiroro a jihar Naijar, Sani Abubakar Yusuf Kokki, ya sheda wa BBC cewa yarjejeniyar wani mataki ne da ya zame wa jama'ar kauyukan da abin ya shafa dole. Ya ce kusan yankuna na mazabu na siyasa sun kai wurin takwas wadanda gaba dayansu a bara sai da suk gudu daga garuruwnsu gaba daya saboda barayin daji sun mamaye su duka. Ya kara da cewa ,'' duk wadanda ka ga sun koma sai da aka tsaya aka yi yarjejeniya da barayi kafin ma su yarda mutane su koma wurarensu su je su yi noma.'' Shugaban matasn ya ce wannan yarjejeniya da suka kulla da barayin ta kasance tamkar harshen damo, domin ta ba su damar su koma su yi noma, amma kuma ta wani bangaren duk da ita, 'yan bindigar sukan zo su ce a ba su wasu abubuwa kafin su bari a ci gaba da noman. Ya ce, kasancewar kungiyoyin barayin wadanda za a iya cewa sune kawai suke iko a yankin, za ku iya kulla yarjejeniya da wasu gobe kuma wasu ma su zo su ce ku ba su wani abu kafin su bari ku zauna har ku ci gaba da rayuwa da ayyukanku. Sai dai Sani Abubakar din ya ce duk da cewa ba su da yadda za su yi a yanzu idan ba bin umarnin barayin ba na wannan yarjejeniya, ba abu ne da zai dore ba: ''Mafitar kawai shi ne a tabbatar mana da tsaro.'' Sai dai gwamnatin jihar Naijar ta bayyana shakku game da wannan yarjejeniya, kamar yadda sakatarenta, Ahmad Ibrahim Matane yake cewa: ''Na farko dai ba mu ma yarda ko kuma mu sa rai ga cewa wa'yannan mutanen kauyuka suna ma yarjejeniya da 'yan ta'adda ba, na biyu imma akwai shi to ina jin abu ne dan kalilan, na uku Alhamdu Lil-Allahi mai girma gwamnan Najia Alahji Abubakar Sani Bello da kuma hadin kan da muke samu daga gwamnatin tarayya, jami'an tsaro sun samu nasara sosai, har yanzu abubuwan nan da muka kara za mu ci gaba da su kuma mu kara karfafa su domin mu ga karshen wannan ta'addancin in sha Allahu,'' in ji shi. Yarjejeniyar da jama'ar kauyukan na jihar Naija ke cewa suna kullawa da 'yan bindiga, don samun damar gudanar da aikin gona, Karin tsokaci ne game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da zame wa al'umma gaba kura baya sayaki yankin arewacin Najeriya. |
It seems that the people of some towns in Shiroro Local Government Area (LGA) of Niger State in Nigeria will continue to negotiate with the Armed Forces to be able to farm this year. |