Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/098 dealing with bandits is a must

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
<small> --[[bbchausa_verticals/098_dealing_with_bandits_is_a_must]]</small>

#

Yarjejeniya da barayin daji ta zamar mana dole [1] Dealing with bandits is a must

1

"Kusan barayin daji ne ke da iko a gaba dayan yankin" "Thieves are in control of the whole area."

2

in ji wani shugaban matasa na ynkin karamar hukumar Shiroro ta jihar Naija said a youth leader of Shiroro Local Government Area (LGA) of Niger State.

3

Ga alama al'ummomin wasu garuruwa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Naija a Najeriya za su ci gaba da yarjejeniyar biyan 'yan bindiga domin su samu damar yin noma a bana.

It seems that the people of some towns in Shiroro Local Government Area (LGA) of Niger State in Nigeria will continue to negotiate with the Armed Forces to be able to farm this year.

4 Tun a bara ne dai Last year,
5 jama'ar wasu kauyuka na yankin karamar, residents of some villages in the area
6 suka fara gwada wata yarjejeniya da ta kunshi bayar da kudi began trying to negotiate a deal to provide money,
7 ko babura motorcycles,
8 ko kayan abinci food
9 ko na masarufi da dai sauransu ga 'yan bindigan da suka addabi yankin. or other necessities to the militants.
10 Su kuma 'yan bindigan su tsahirta wa mutanen komawa kauyukansu, The gunmen then forced the people to return to their villages
11 don su yi aikin gona da damina, to farm in the rainy season,
12 kuma su yi girbi a lokacin kaka. and to harvest in the autumn.
13 BBC ta tattauna da wasu daga cikin mazauna wadannan kauyuka The BBC spoke to some of the residents of these villages
14 domin jin yadda za su yi a wannan lokaci da damuna ke kamawa. to find out what they would do during the rainy season.
15

Rest of the article <> Sauran labarin

  1. Shugaban kungiyar matasan yankin na Shiroro a jihar Naijar, Sani Abubakar Yusuf Kokki, <> Sani Abubakar Yusuf Kokki, president of the Shiroro Youth Association in Niger State,
  2. ya sheda wa BBC cewa yarjejeniyar wani mataki ne <> told the BBC that the agreement was a necessary step
  3. da ya zame wa jama'ar kauyukan da abin ya shafa dole. <> for the people of the affected villages.
  4. Ya ce kusan yankuna na mazabu na siyasa sun kai wurin takwas wadanda gaba dayansu a bara sai da suka gudu daga garuruwnsu gaba daya saboda barayin daji sun mamaye su duka. <> He said almost a dozen (8) constituencies had all fled their villages last year because of ravages by wildlife thieves.
  5. Ya kara da cewa ,''duk wadanda ka ga sun koma sai da aka tsaya aka yi yarjejeniya da barayi kafin ma su yarda mutane su koma wurarensu su je su yi noma.'' <> He added, "All those that you see returning, did not return until there was an agreement with thieves in place. Only then, people would return and farm/cultivate."
  6. Shugaban matasan ya ce wannan yarjejeniya da suka kulla da barayin ta kasance tamkar harshen damo, <> The youth leader said the deal with the thieves was a bit harsh,
  7. domin ta ba su damar su koma su yi noma, <> as it allowed them to return to farming,
  8. amma kuma ta wani bangaren duk da ita, <> but on the other hand,
  9. 'yan bindigar sukan zo su ce a ba su wasu abubuwa kafin su bari a ci gaba da noman. <> the gunmen would come and ask for some things before they allow farming to continue.
  10. Ya ce, kasancewar kungiyoyin barayin wadanda za a iya cewa su ne kawai su ke iko a yankin, <> He also said that at times, these gangs are the only ones running the region.
  11. za ku iya kulla yarjejeniya da wasu gobe <> you can make a deal with some tomorrow
  12. kuma wasu ma su zo su ce <> and some even come and demand
  13. ku ba su wani abu kafin su bari ku zauna har ku ci gaba da rayuwa da ayyukanku. <> that you must give them something before they let you stay and move on with your lives and jobs.
  14. Sai dai Sani Abubakar din ya ce duk da cewa ba su da yadda za su yi a yanzu <> However, Sani Abubakar said that although they had no choice
  15. idan ba bin umarnin barayin ba na wannan yarjejeniya, <> but to follow the orders of the thieves of this agreement,
  16. ba abu ne da zai dore ba: <> it was not sustainable:
  17. ''Mafitar kawai shi ne a tabbatar mana da tsaro.'' <> "The only solution is to ensure our safety."
  18. Sai dai gwamnatin jihar Naijar ta bayyana shakku game da wannan yarjejeniya, <> Furthermore, the Niger State government has expressed doubts about the deal,
  19. kamar yadda sakatarenta, Ahmad Ibrahim Matane yake cewa: <> according to its secretary general, Ahmad Ibrahim Matane:
  20. ''Na farko dai ba mu ma yarda ko kuma mu sa rai ga cewa <> 1st, we do not even believe or expect
  21. wa'yannan mutanen kauyuka suna ma yarjejeniya da 'yan ta'adda ba, <> that villagers are in agreement with the bandits.
  22. na biyu imma akwai shi to ina jin abu ne dan kalilan, <> second, if there is, I think it is a small thing.
  23. na uku Alhamdu Lil-Allahi mai girma gwamnan Najia Alahji Abubakar Sani Bello <> third, thanks to His Excellency governor of Niger Alhaji Abubakar Sani Bello
  24. da kuma hadin kan da muke samu daga gwamnatin tarayya, <> along the cooperation we received from the Federal Government,
  25. jami'an tsaro sun samu nasara sosai, <> the security forces have been very successful,
  26. har yanzu abubuwan nan da muka kara za mu ci gaba da su <> we will still continue to build on these wins
  27. kuma mu kara karfafa su domin mu ga karshen wannan ta'addancin in sha Allahu,'' in ji shi. <> and intensify our efforts in order to bring an end to these crimes, God willing!" he said.
  28. Yarjejeniyar da jama'ar kauyukan na jihar Naija ke cewa suna kullawa da 'yan bindiga, <> The agreement that the villagers of Niger State make with the militants,
  29. don samun damar gudanar da aikin gona <> allow them to farm.
  30. Karin tsokaci ne game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da zame wa al'ummar yankin arewacin Najeriya. <> This further underscores how the security crisis continues to affect the growth of the communities in Northern Nigeria.