Quran/3 > Quran/3/Rijayar_Lemo_Tafsir > Quran/3/Rijayar_Lemo_Tafsir2
Tarjama Da Tafsirin ayoyin 100-101 na Surar Ali Imran
- Ya ku wadanda suka yi imani, idan kuka bi wani bangare na wadanda aka ba wa Littafi, to za su mayar da ku kafirai bayan imaninku. --Quran/3/100
- Ta yaya kuma za ku kafirce, ga shi kuwa ana karanta muku ayoyin Allah, kuma Manzonsa yana tare da ku? Duk kuwa wanda ya riki Allah, to hakika an shiryar da shi tafarki madaidaici. --Quran/3/101
A wadannan ayoyi Allah yana gargadin muminai da cewa, idan suka kuskura suka nuna biyayyarsu ga Yahudawa da Nasara, wadanda suke yi musu hassadar Alqur'ani da Allah ya ba su da falalar Musulunci; to tabbas za su raba su da imaninsu, su mayar da su kafirai suna ji suna gani. Amma Allah ya nuna cewa, da wahala kwarai muminai su yarda su koma kafirci bayan ga Alkur'ani nan kullum suna ji ana karanta musu ayoyinsa, sannan ga Manzon Allah nan a tsakaninsu, yana isar musu duk wani saƙo da aka saukar dominsu. Shi imani idan har ya ratsa ƙoƙon zuciya; to abu ne mai wuyar gaske a iya cire shi, sai dai wani iko na Allah.
Sannan Allah ya bayyana musu wata hanya wadda idan suka bi ta, za su tsare kawunansu daga fadawa ramin kafirci. Wannan hanya ita ce, rike Allah da dogaro da shi, domin shi ne madogara ta samun shiriya. Duk wanda ya koma ga Allah a cikin kowanne hali nasa, ya nemi mafaka a wurinsa, ya dogara da shi dogaro na gaskiya, ya rike addininsa; to hakika wannan an shiryar da shi ga hanya mikakkiya dodar, wadda babu karkata ko kadan a cikinta, ita ce za ta yi masa jagoranci har ta kai shi gidan Aljanna.
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Gargadin Musulmi a kan su yi hattara wajen yarda da maganganun Yahudawa da Nasara da aiki da su, ko kwaikwayon wani tsari nasu na rayuwa, domin zukatansu cike suke da hassada da kullata ga Musulmi, a kullum suna tunanin hanyar da za su bi su raba Musulmi suka yi sakaci suka karbi tsare-tsarensu na rayuwa; to za su iya kai su ga halaka.
- Sanin falalar sahabban Manzon Allah SAW, ta kasancewarsa ya rayu dauke da shi, kuma ya zame musu ƙaƙƙarfar katanga mai kare su daga faɗawa kafirci ko karkace hanyar gaskiya. Wannan ba karamar falala ba ce ga sahabbai; babu wanda ya sami irinta cikin wannan al'umma sai su.
- Riƙo da littafin Allah da sunnar Annabi SAW shi ne babban abin da zai tsare mumini daga kauce wa hanyar Allah, ko fadawa cikin kafirci.
- Idan zaman Annabi SAW a cikin wannan al'umma ya ƙare lokacin rayuwarsa, to ai ayoyin Allah da sunnonin Annabinsa suna nan a tsakanin al'umma, kuma Musulmi a yau ana neman su da aiki da Alƙur'ani da sunna, kamar irin yadda aka nemi musulmin farko da hakan; don haka har yanzu hanyar samun kariya da tsari a fili take.
Tarjama Da Tafsirin ayoyin 102-109
- Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi taƙawa ga Allah haƙiƙanin taƙawa, kuma lalle kada ku mutu face kuna Musulmi. --Quran/3/102
- Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya hada tsakanin zukatanku, sai kuka zamo 'yan'uwan juna a sakamakon ni'imarsa, a da kuma kun kasance a kan gabar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ko kwa shiriya. --Quran/3/103
- A cikinku lalle a sami wata al'umma wadanda suke kira zuwa ga alheri, kuma suke umarni da kyakkyawa, kuma suke yin hani daga mummuna. Wadannan su ne masu rabauta. --Quran/3/104
- Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka sassaba bayan hujjoji sun zo musu. Wadannan kuwa suna da azaba mai girma. --Quran/3/105
- Ranar da wadansu fuskoki za su yi fari, wadansu fuskokin kuma za su yi baki. Amma wadanda fuskokinsu suka yi baki, (ca a ce da su): "Shin ku ne kuka kafirce bayan imaninku? To ku dandani azaba, saboda kafircin da kuka kasance kuna yi." --Quran/3/106
- Amma wadanda fuskokinsu suka yi fari kuwa, to suna cikin rahamar Allah, suna masu dawwama a cikinta. --Quran/3/107
- Wadannan ayoyin Allah ne muke karanta maka su da gaskiya. Kuma Allah ba Ya nufin zalunci ga talikai. --Quran/3/108
- Kuma duk abin da yake cikin sammai da kasa na Allah ne. Kuma zuwa ga Allah ne ake mayar da duk al'amura. --Quran/3/109
A wadannan ayoyi, Allah SWT yana umartar bayinsa muminai da su ji tsoronsa gwargwadon ikonsu, sannan su ci gaba da rike wannan addini ƙam-ƙam har mutuwa ta zo musu. Kuma lalle su haɗa kansu, su zama abu guda a kan gaskiya, su taru su riƙe igiyar Allah, wadda ita ce Alƙur'anin da Manzo ya zo musu da shi da sunnarsa; kada su yarda su rarrabu.
An karbo daga Abu Huraira ya ce: Annabi ya ce:
"Lalle Allah ya yarje muku abubuwa uku (3), kuma ya ƙi muku abubuwa uku. Ya yarje muku da ku bauta masa, kuma kada ku haɗa komai da shi, kuma duk ilahirinku ku yi riƙo da igiyar Allah, kada ku rarrabu, kuma ya ƙi muku bin jita-jita da yawan tambaya da ɓarnata dukiya." [Muslim #1715]
Abu Huraira reported Allah's Messenger (ﷺ) as saying:
Verily Allah likes three things for you and He disapproves three things for you. He is pleased with you that you worship Him and associate nor anything with Him, that you hold fast the rope of Allah, and be not scattered; and He disapproves for you irrelevant talk, persistent questioning and the wasting of wealth. https://sunnah.com/muslim:1715a
Sannan Allah ya umarce su da su tuna ni'imarsa da ya yi musu lokacin da suka hadu a kan Musulunci, suka zama 'yan'uwan juna, bayan a da kafin zuwan Musulunci a rarrabe suke, suna gaba da fada da junansu a kan abin da bai taka kara ya karya ba, sai ga shi Allah ya haɗa zukatansu gaba ɗaya sun zama 'yan'uwa masu ƙaunar junansu, kamar yadda ya bayyana hakan a Suratul Anfali, aya ta 62-63.
Kuma Allah ya tunatar da su cewa, suna dab da fadawa ramin wuta, sai Allah ya ceto su, domin babu abin da ya rage musu su fada cikinta sai mutuwa idan har suna cikin wannan hali na kafirci. To kamar irin wannan bayani da ya yi musu filla-filla har suka fahimta; to haka yake fayyace musu sauran ayoyin nasa, don su zame musu fitilar gane hanyar shiriya da gaskiya.
Sannan Allah ya umarci bayinsa da cewa, lalle a sami wata kungiya daga cikinsu, wadanda za su dauki nauyin yin umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna a cikin al'umma; wannan shi ne maganin rabuwar kai a tsakaninsu. Domin duk al'ummar da take rayuwa kara-zube, kowa yana yin abin da ya ga dama, babu mai tsawata masa yayin da ya yi ba daidai ba, to wannan al'umma za ta rasa haduwar kai a tsakanin 'ya'yanta, domin soye-soyen zukatan mutane mabambanta ne. Allah ya bayyana cewa, wadanda suka siffantu da sifar nan ta umarni da kyakkyawan abu, da hana mummuna, su ne masu samun babban rabo a duniya da lahira.
An karbo daga Huzaifa dan Alyaman ya ce, Annabi SAW ya ce: "Na rantse da wanda rai na yake hannunsa, Wallahi, ko dai ku yi umarni da kyakkyawan aiki, ku hana mummuna, ko kuma ba da dadewa ba Allah ya aiko muku da wata ukuba daga gare shi, ku yi ta addu'a ya ki amsa muku!" [Ahmad #23349 da Tirmizi #2169].
Hudhaifah bin Al-Yaman narrated that the Prophet (s.a.w) said: "By the One in Whose Hand is my soul! Either you command good and forbid evil, or Allah will soon send upon you a punishment from Him, then you will call upon Him, but He will not respond to you." https://sunnah.com/tirmidhi:2169
Sai kuma Allah ya hana muminai rarrabuwa, kamar yadda Yahudu da Nasara a gabaninsu suka rarraba a addininsu, bayan hujjoji daga Allah, a ranar da fuskokin 'yan Aljanna za su yi fari, fuskokin 'yan wuta kuma su yi baki. Sai cikin zargi a ce wa masu bakaken fuskoki: "Shin ku ne kuka kafirce bayan imaninku? To ku dandani azaba saboda kafircinku." Amma masu fararen fuskoki, za su kasance ne a cikin rahamar Allah, tare da jin dadin da Allah ya tanadar musu a Aljanna na ni'imomi masu yawa, za su ci gaba da rayuwa a cikinsu har abada.
Sannan Allah ya tabbatar wa Annabinsa cewa; wadancan ayoyi da ya karanta masa su ne gaskiya, kuma tabbas Allah ba wanda yake zalunta cikin halittunsa. Duk abubuwan da suke cikin sammai, da wadanda suke kasa na Allah ne shi kadai, kuma duk al'amura gaba daya gare shi za a mayar da su ranar alkiyama, domin ya saka wa kowa aikin da ya yi; idan ya aikata alheri, ya ga alheri, idan kuwa sharri ya aikata, to ya ga sharri.
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Wajibi a kan Musulmi su ƙanƙame ma addinin Musulunci, kar su rabu da shi har zuwa mutuwarsu.
- Wajibi ne Musulmi su hada kai su zama al'umma daya. Hanyar hada kan kuma ita ce rike shari'ar Allah, wadda take kunshe cikin Alkur'ani da sunnar Annabi. Sabananin haka kuma shi ne rarrabuwa, wadda take nufin rike bidi'o'i da son zuciya.
- Tunowa da ni'imomin Allah ga bayinsa, wadanda suka shafi addininsu ko rayuwarsu ta duniya, da gode wa Allah a kansu a zukata da harshe, wannan zai kara musu son Allah, sai shi kuma ya kara musu falalarsa da kyautarsa.
- Kira zuwa ga addinin Allah wani ginshiki ne na tabbatar da tsarin Allah a bayan kasa da kuma murkushe karya da barna da kawar da mummunan aiki da tabbatar da kyakkyawa. To masu irin wannan aiki su ne masu rabauta duniya da lahira.
Tarjama Da Tafsirin ayoyin 110-112
- Ku ne mafi alherin al'umma wadanda aka fitar ga mutane, kuna umarni da kyakkyawan aiki, kuma kuna hana mummuna, kuma kuna yin imani da Allah. Da a ce kuwa Ma'abota Littafi za su yi imani da ya fi alheri a gare su. A cikinsu akwai muminai, amma mafiya yawansu fasikai ne. --Quran/3/110
- Ba za su taba iya cutar da ku ba sai dai cutarwa kadan; kuma in da za su yake ku, sai sun juya muku baya, sannan ba za a taimake su ba. --Quran/3/111
- An hada su da kaskanci a duk inda aka same su, sai dai wadanda suke rike da wani alkawari daga Allah ko wani alkawari daga mutane, kuma sun dawo da wani fushi daga Allah, kuma an hada su da talauci. Hakan kuwa saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyiin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani hakki ba, hakan yana faruwa ne saboda sabo da suka yi, kuma sun kasance suna ketare iyaka.
A wadannan ayoyi, Allah yana magana da wadannan al'umma. Farkon wadanda suka shiga cikin wannan kiran, su ne sahabban Annabi, domin su ne farkon wadanda ayar ta yi magana da su. Wannan matsayi mai girma sun cancance shi ne saboda sun siffantu da yin umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna da kuma imani da Allah. Wannan ne ya sanya suka tsere wa al'ummomin da suka gabace su.
Da a ce Yahudawa da Nasara sun yi imani da Annabi da abin da ya zo da shi daga Ubangijinsa, to da ya fi musu alheri. Sai dai wadanda suka yi imani a cikinsu 'yan kadan ne, da dama daga cikinsu sun ci gaba ne da zama a kan kangare wa Allah da Manzonsa SAW. Wannan shi zai hana su kaunaci muminai sai dai su yi ta gaba da su da kokarin cutar da su duk sanda suka sami dama. Amma dai duk yadda suka kai ga nuna musu kiyayya da kokarin cin zarafinsu, ba za su iya ba in banda cutarwa da fatar baki ba. Idan ma da fada zai hada su da muminai; to ba za su iya taɓuka komai ba sai dai su gudu, kuma ba za a taimaka musu ba, domin kuwa Allah ya hada su da kaskanci da wulakanci a duk inda suke a bayan kasa, ba sa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, sai da wani alkawari daga Allah ko daga mutane. Sannan kuma sun cancanci fushin Allah, kuma ga alamun talauci sun bayyana a tare da su. Irin wannan sakamakon ya faru da su ne saboda kafirce wa ayoyin Allah da suke yi, da kuma kashe annabawa ba tare da wani laifi ba, sai don zalunci kawai. Kuma abin da ya kai su ga wannan hali na kafirci da kisa, shi ne sabon Allah da suke yi da ketare iyakokinsa da shari'arsa.
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Ayar farko tana nuna falalar sahabban Annabi da fifikonsu a cikin wannan al'umma. Duk da cewa ayar ta hada har da sauran muminai wadanda suka zo bayan sahabbai, sai dai sahabban ne aka fara fuskanta da ita, shi ya sa suka fi cancanta da ita. Sannan siffar umarni da kyakkyawan aiki, da hana mummunan aiki da siffar umarni da kyakkyawan aiki, da hana mummunan aiki da siffar imani da Allah, duk sun fi bayyana tare da sahabbai fiye da sauran muminai da za su zo bayansu. An karbo daga Abdullahi dan Abbas ya ce, Manzon Allah ya ce: "Mafi alherin mutane su ne na ƙarnina, sannan wadanda suke bi musu, sannan wadanda suke bi musu..." [Bukhari #3651] The Prophet (ﷺ) said, "The best people are those living in my generation, and then those who will follow them, and then those who will follow the latter. Then there will come some people who will bear witness before taking oaths, and take oaths before bearing witness." (Ibrahim, a sub-narrator said, "They used to beat us for witnesses and covenants when we were still children.") https://sunnah.com/bukhari:3651
- Ya kamata al'ummar Musulmi su