Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

sandbox1

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 16:23, 17 July 2017 by Admin (talk | contribs)

Notes to self

  • Special characters reference: Ɓ ɓ Ɗ ɗ Ƙ ƙ Ƴ ƴ
  • f
  • m
  • Be sure to replace all instances of the noun template to the suna template.
  • Swapping links between languages...
  • #REDIRECT Other article
  • Transfer and archive to http://hausadictionary.com/sandbox1


burtsai

  1. kalma mai nuna yatsinewar abu.

burtsatsa

  1. kalma mai nuna hargitsewar gashi ko wani abu.
  2. to drive away. (= kora.)

buruda

Adjective

f / m

  1. mai tsananin jin sanyin ruwa har ya kasa yin alwala.
  2. [bu"ru/+da"] {n.f.}. Excessive susceptibility to cold. e.g. Audu buruda gare shi. (One so affected cannot touch cold water for ceremonial ablutions.)

burudu

Noun

m

  1. abu mai kaushi-kaushi, musamman abawa ko takarda.
  2. albarushin bindiga ko harshashi.
  3. Thick spun cotton thread. (= aburduga; vide arafiya; guzur-guzur.)
  4. yarinyan nan burudun kyau gare ta, this girl has big but good features. (= (Kats.) manya manyan kyau.)
  5. {n.m.} = albaruhi; buruda, baruda.

burude, burud'e, buruɗi

  1. REDIRECT buruɗe

buruɗe

Noun

m

  1. {n.m.}. The terminal inflorescence of maize. <> kan masara

burugu

Noun

m

  1. {n.m.}. A good fodder-grass grown in swamps. <> wata irin ciyawa da ake ba dabbobi.

buruk'u, buruku

  1. REDIRECT buruƙu

buruƙu

Noun

m

  1. A small shrub (= wawa-ka-je-magori). <> wata irin ciyawa.
    1. Ganyen Buruƙa: Ana ɗebo ganyen buruƙu a haɗa da genyen Duman Rafi a tafasa a yi sirace, yana maganin amosani. [1]
  2. A fool, nincompoop. <> wawan mutum, shashasha.

buluƙuƙu, burukuku, buruk'uk'u

  1. REDIRECT buruƙuƙu

buruƙuƙu

Noun

m

  1. wani irin tuwo da ake yi da wake. <> tuwo made out of beans.
  2. wani irin wasan yara. <> a kid's game.
  3. Sandbox1 is another way of spelling buluƙuƙu.

ɓurum

Adverb

  1. mai-baki ɓurum: one with lips sunken in through toothlessness.
    1. rami ya ɓurme ɓurum. <> the earth gave way, revealing a hole beneath.
See also burum

burum

Adverb

  1. {n.m.}. Hugeness (of abdomen); bigness and broadness (of clothing). e.g. zane ne burum da shi {pl. zannuwa ne burum-burum da su}. (Vide burum-burum.) <> girman ciki ko kaurin tufa.
  2. ƙarar fashewar abu. <> the sound of an explosion, e.g.
    1. na ji burum. <> I heard a boom.
  3. burum; ta ci burum, the biter bit (e.g. a thief has his goods stolen from him <> kura ta yi karo da ɓarawo, watau idan ta ci shi ta ci amana, idan ta bar shi ta bar nama.).
See also ɓurum

buruma

Adjective

f

  1. kalma mai bayyana girman abu, musamman jaka {adj.f}. Large, applied to
    1. (a) a bag (burumar jaka = ƙatuwar jaka), or
    2. (b) a large gourd vessel. (burumar buta).
  2. buruma babbar jaka, epithet applied to a gluttonous woman.

burundumi

Adjective

burundumi = m; fem. f = burunduma; burundumai = pl.

  1. {adj.m.} Large, applied to a ewer (tulu), gourd (gora or buta), bag. e.g. burundumin gora, burundumar buta. <> ƙaton abu.

burungu

Noun

m

  1. kirarin kura <> a hyena epithet.
    1. Aljannar dare, kowa ya yi dare, baran ubanki ne

burunguza

  1. {adj. fem.}.
    1. (a) Of poor quality (applied to daddawa, tobacco, &c.). (Vide bunga; butuwa, &c.). <> abu marar daraja.
    2. (b) Very big, e.g. woman or animal. <> ƙatuwar mace ko dabba mai muni.
  2. {n,f.}.
    1. (a) A drum, beaten by travelers on reaching the vicinity of highway robbers; also beaten at wrestling bouts. <> wata irin ganga da ake kaɗa wa 'yan hoto ko 'yan dambe.
    2. (b) A very large woman. <> ƙatuwar mace.
    3. (c) A huge bunch of small ornaments affixed to the face of a horse. (A smaller bunch is called tinjima.) <> wani irin adon fuskar doki.

burunta

Verb

burunta | buruntu

  1. tufka zare.
  2. [bu"ru"ntu/+] {n.m.}. Twisting threads together to make them into two- or three-ply cotton.

buruntumau

Adjective

m

  1. Sandbox1 is another way of spelling burtumau.
  2. fearless person. <> mutum marar tsoro.

bururi

Noun

m

  1. iska da hazo na lokacin hunturu. <> the winter wind and haze. (= buda.)

bururu

Noun

m

  1. kunun ɓarzajjen hatsi. <> {n.m.}. A gruel made with coarsely ground flour. (= (Z.) badam; (Kats.) gwada.)

burus

  1. REDIRECT biris

burushi

See also toothbrush

Noun

Singular
burushi

Plural
burososhi or burusai

Singular
brush

Plural
brushes

a brush

m

  1. The English word brush. (Also barushi; baroshi; buroshi.)
  2. wani abu tsintsiya-tsintsiya mai ƙota da ake ye amfani da shi wajen goge abubuwa kamar takalmi ko haƙori, da shafen fenti.


Verb

Plain form (yanzu)
brush

3rd-person singular (ana cikin yi)
brushes

Past tense (ya wuce)
brushed

Past participle (ya wuce)
brushed

Present participle (ana cikin yi)
brushing

  1. yi burushi.

buruska

Noun

f

  1. [buruska"] {n.f.}. (G. & N.). A wrestling game.

burutsu

Noun

m

  1. aiki mara kyau. <> a poor job.
  2. soki burutsu - zancen mara ma'ana. <> Pointless conversation or irrelevant remarks. (= soki)

burwatsai

Noun

m

  1. {n.m.}. Of unpleasant appearance, especially eyes which are not normal, food made with carelessly ground flour, water with unsettled sediment untidy hair <> kalma mai nuna rashin kintsin abu, musamman gashi. e.g.
    1. gashi ya yi burwatsai.
    2. fura ta yi burwatsai.

Adverb

  1. {adv.}. (Kats.) kana dubana burwatsai, you are looking at me contemptuously. (= shek'ek'e.)
  2. kallon raini <> a disrespectful, patronizing look.

burzu

Noun

m

  1. {n.m.}. A weed of cultivated field, its stem is used in making cotton spindles. <> wata ciyawa mai fitowa a gona.
  2. burzun 'dinya - The stone of the fruit of 'dinya.

bus

English

Noun

Singular
bus

Plural
buses or busses

A bus.
  1. babbar mota. <> (countable) A bus is a vehicle that carries a large number of people on roads.


Verb

Plain form (yanzu)
bus

3rd-person singular (ana cikin yi)
buses

Past tense (ya wuce)
bused

Past participle (ya wuce)
bused

Present participle (ana cikin yi)
busing

Plain form (yanzu)
bus

3rd-person singular (ana cikin yi)
busses

Past tense (ya wuce)
bussed

Past participle (ya wuce)
bussed

Present participle (ana cikin yi)
bussing

  1. (transitive) If you bus people somewhere, you take them there on a bus.
    The children are bused to school every morning.
  2. (transitive) If you bus tables, you take away dirty dishes in a restaurant.

Hausa

  1. kalma mai nuna tsananin busowar warin abu. <> a strong unpleasant odour. {n.m.}. A strong unpleasant odour, e.g.
    1. na ji bus.
  2. ƙarar tusar talo-talo ko wani abu. <> the sound of a turkey's fart.
  3. (Kats.) An exclamation equivalent to 'Go away'.
See also ɓus

ɓus

Adverb

  1. Emphasizes verb 'busa q.v. e.g. an 'busa shi 'bus, it has been pierced right through.

Noun

  1. A kind of sweetmeat made with wheat or rice.
    1. alewa ta yi ɓus, the mixture for making sweets has been over-boiled and will not 'work' properly.
See also bus

b'us

  1. REDIRECT ɓus

busa-goggo

Noun

m

  1. wani irin ciwo a harshe. <> a tongue sore.

busak'i, busaki

  1. REDIRECT busaƙi

bushak'i, bushaki

  1. REDIRECT bushaƙi

bushaƙi

Adjective

bushaƙi = m | bushaƙa / bushaƙiya = f | bushaƙai = pl.

  1. katon mutum mara kintsi.

bushi

Noun

m

  1. ban iska
  2. bushewar da karan dawa ke yi yayin da ta fid da kai kuma kafin ta fara ido. <> {n.m.}. Drying of corn-plants after head has appeared and before grain has formed. (= (Kats.) busau. cf shira.)
  3. busa, bushiri.
  4. {n.m.}. A dry spell in the wet season. (Vide bushe.)
  5. Exclamation of surprise at (a) wind = what a wind!
  6. The name of a plant.

bushino

Noun

m

  1. zancen ƙarya. <> a fabricated or made-up story.
  2. tsananin neman ƙwarewa a kan abu.

bushiri

Noun

m

  1. wata rigar sirdin doki mai launin ja da fari.

buskuɗa

  1. Lie huddled up, especially on the bare ground, or of a number of persons in a small room. (= kusumbuɗa.) <> zama cikin turɓaya da ke kawo ɓacin sutura.
  2. muskuɗa, buskuɗawa.

busku'da, buskuda

  1. REDIRECT buskuɗa

busta

Noun

f

  1. {n.f.}. (Arabic. from Italian.) 1. (a) Post, mail. e.g. an saka takarda a b., a letter has been posted. (b) A mail bag of letters. (Vide kada ta kwana.) (c) Parcel post. <> aike ta gidan waya.
  2. A load of white kola-nuts. (= kataku.) <> bustar goro = kayan goro.

busur-busur

Adverb

  1. {adv.}. Indicates the snund of the rubbing together of fat legs. <> kalma mai nuna tafiyar mai ƙiba.

butaci

Noun

m

  1. {n.m.}. Anything which rises to, and floats on, the surface of a fluid, e.g. bits of bran, wisps of grass, &c. (= firkaki; sururu.) <> dusa-dusa da ke tasowa kan ruwan da aka jiƙa tsaki ko gari.

butari

Noun

m

  1. tsiren da ake yi da tantani.

buta-wuta

Noun

f

  1. wata irin ciyawa.
  2. {n.f.}. 1. A creeper used as a remedy for burns.
  3. The insect faɗa wuta.

butsa-butsa

  1. kalma mai bayyana rashin kintsin abu. <> expresses disorganization and messiness.

butsare

  1. Jib, get out of hand. (= finjire.)
  2. Buck (donkey). <> butsarewa.
  3. daburce ko ƙin sarrafuwa.
  4. yin tawaye ko fanɗarewa.