Overview
- Lesson Title: The Bakassi Peninsula Dispute-This is a report about the Bakassi Peninsula dispute between Nigeria and Cameroon.
- Language: Hausa
- Topic: Economics/Politics
- ILR Level: 1+/2
- ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Reading
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2008
- ObjectID: HAUS_13090
Transcript
Original | Translation |
---|---|
Nijeriya ta mika tsibirin Bakassi ga Kamaru A ran 14 ga wata,Nijeriya ta mika tsibirin Bakassi ga kasar Kamaru,daga nan aka sa aya ga gardamar da ta shafe shekaru da dama da aka yi ta yi tsakanin kasashen nan biyu.Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana cewa muhimmin al'amari ne a duniya,Nijeriya ta zama abin koyi ga sauran kasashe da yankuna na duniya wajen warware gardama kan yankuna. Duk da haka gwamnatin Nijeriya ta fuskanci matsin lamba daga kafofin yada labarai na gida sabo da mika tsibirin Bakassi,shi ya sa tana nan tana sha jarrabawa bayan mikawa. Tsibirin Bakassi yana bakin kudu na tsakanin Nijeriya da Kamaru,fadinsa ya kai muraba'in kilomita dubu,yana da arzukin man fetur da gas.Gwagwarmar da ake yi tsakanin Kamaru da Nijeriya ba ta daina ba domin mallakar wannan tsibirin,har ma aka yi tashin hankali na zubar da jinni. A shekara ta 1994, Kamaru ta gabatar da batun mallakar tsibirin Bakassi ga kotun duniya ta Hague. A watan Oktoba na shekara ta 2002,kotun duniya ta Hague ta tsaida kudurin mayar da tsibirin Bakassi ga Kamaru. Bisa kudurin nan,gwamnatocin kasashen biyu sun daddale yarjejeniyar Green Tree a birnin New York na kasar Amurka a ran 14 ga watan Augusta na shekara ta 2006,daga nan an fara gudanar da shirin mika tsibirin Bakassi. Duk da haka,bisa abubuwan da aka tanada a cikin tsarin mulkin kasa na Nijeriya,an bayyana cewa dole ne kowace yarjejeniya da gwamatin Tarayyar Nijeriya ta daddale da kowace kasa ta sami amincewa daga majalisun dokokin kasa,in ba haka ba ba ta iya fara aiki. A watan Nuwanba na shekara ta 2007,majalisun dokoki na Nijeriya sun yanke shawara cewa yarjejeniyar Green Tree ba ta da amfani bisa dokokin kasa, sabili da haka Nijeriya ba ta iya mayar da tsibirin Bakassi ba. Ko ma a yan kwanakin gabannin bikin mikawa, kotun Tarrayar Nijeriya a birnin Abuja ta bayar da umurni ga gwamnatin Nijeriya da ta kiyaye halin da ake ciki yanzu a tsibirin Bakassi.A sa'I daya,yawancin mutanen Nijeriya suna masus ra'ayi cewa mika tsibiri ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ba ta da karfi domin babu wata kasa a duniya da ta kama gaba ta mika yankinta. Kwanakin baya,wasu kungiyoyin fafitika na Nijeriya sun sha kai hari kan sojojin Kamaru a yankin dab da tsibirin Bakassi. Kuma sun kankama da cewa idan aka mika tsibirin tare da nasara,za su kai Karin hari kan sojojin Kamaru. |
Nigeria hands Bakassi peninsula over to Cameroon On the 14th of this month, Nigeria transferred the Bakassi peninsula to Cameroon, ending a dispute between these two countries that has been ongoing for many years. The General Secretary of the United Nations, Ban Ki-moon, explained that it was a landmark step for the world, and that Nigeria had set an example for other countries and regions of the world for resolving regional disputes. Nevertheless, the Nigerian government is facing pressure from the domestic media for ceding the Bakassi peninsula, and this has placed it in a difficult position following the transfer. The Bakassi peninsula is located at the southern border between Nigeria and Cameroon, covers an area of about 1,000 square kilometers, and is rich in oil and gas resources. The struggle between Cameroon and Nigeria over control of the Bakassi peninsula has continued unabated, resulting in riots and bloodshed. In 1994, Cameroon brought the issue of sovereignty of the Bakassi peninsula before the International Court of Justice in The Hague. In October 2002, the International Court of Justice in The Hague delivered a judgment restoring the Bakassi peninsula to Cameroon. Based on this ruling, the governments of the two countries signed the Greentree Agreement on August 14, 2006 in New York in the U.S., and so began the process of handing over the Bakassi peninsula. However, according to provisions in Nigeria’s constitution, any treaty the federal government of Nigeria enters into with another country must be ratified by the Senate; otherwise it cannot go into effect. In November of 2007, the Nigerian Senate decided that the Greentree Agreement had no basis in the country’s laws, and therefore Nigeria should not cede the Bakassi peninsula. In the days leading up to the transfer ceremony, a Nigerian federal high court in Abuja even ordered the Nigerian government to maintain the status quo with regards to the Bakassi peninsula. Moreover, the majority of Nigerians were of the opinion that ceding the peninsula would demonstrate weakness on the part of Nigeria, since no other country in the world has ever been so coerced into handing over territory. A few days later, Nigerian militants attacked Cameroon’s army in the center of the Bakassi peninsula, and threatened that if the peninsula were transferred, they would carry out further attacks on Cameroon’s army.
|
Glossary
Hausa term | English meaning |
---|---|
tsibirin (Bakassi) | "Island," refering to Bakassi Peninsula |
abin koyi | "Example" |
matsin lamba | "Being crowded" or "in a crisis" means "to be pushed to the limit," "harassed," "constrained," or "harshly criticized." |
na gida | "Local" |
sha jarrabawa | "Go through trials," or "be under criticism" |
tashin hankali na zubar da jini | "Conflicts leading to bloodshed," refers to deadly confrontation. |
daddale yarjejeniyar | "Reach an agreement," "settlement" |
ƙungiyoyin fatitika | "Trouble-making associations" implies armed groups or militia in the context of the text. |
tare da nasara | "With victory," means "successfully" in this context. |
man fetur | "Petrol oil" |
Notes
1. The Bakassi Peninsula is situated in southern Nigeria and Cameroon on the Gulf of Guinea. It is home to a host of small fishing communities of about three hundred thousand people, mostly Nigerian citizens. Soldiers placed by both countries to mark their sovereignty over the peninsula occupy it, too.
Although border diputes are common between the two countries, Bakassi has drawn increasing attention as it becomes public knowledge that it is rich in oil and natural gas, thus being economically strategic. Decades of escalating incidents and clashes have left many dead or wounded, and assaults continue to plague it.
Many countries got involved in mediations with a succession of presidents, mainly on the Nigerian side, to bring an end to the conflict.
http://www.postwatchmagazine.com/files/bakassi_notes.pdf