(Redirected from wutar)
Noun

f
- wata halitta ko iska mai zafi wadda ake ƙona/gasa/dafa abu da ita. <> wuta is the Hausa term for fire - A chemical reaction that makes heat and flames.
- yaƙi ko rikici ko hargitsi <> bombardment, conflict, surge, crisis.
- wuta ta tashi a tsakanin wasu garuruwa biyu.
- farar wuta - wani abu da ake yin maganin ƙazuwa da shi. <> sulfur.
- Synonym: alkibiri
- aska
- jawaska
- lamba
- ƙoƙiya = wutar raƙumi
- wutar lantarki - haske <> electricity, power.
- Kunna wuta <> Turn on the lights.
- NEPA sun cika ɗauke wuta a Nijeriya. <> The NEPA organization had too many power outages in Nigeria.
- wutar 'yola = wutar bango = wutar fadama; wani irin ƙwaro da aka fi samu da damina wanda in ya tashi yakan ƙyasta wuta da fiffikensa <> glowworm.
- bakin wuta <> blaze.
- wutar dare - wata irin cuta a fatar jikin mutum. <> a skin disease that spreads. Something going viral.
- “They always refer to any inflammation on their body such as rashes, swollen lips, skin burn as “Wutar Dare” (an infection that looks like a burn on the skin). [1]
- A makon da ya gabata ne sai ga wani faifan bidiyo a shafukan abota na internet yana ta yawo kamar wutar dare. [2]
- Yan uwa gaskiya binso inyi magana akan wan nan abinba, sai dai gaskiya yan'uwa al'amarin abin nan na shakiyancin nan cigaba yake sai ruruwa yake kamar wutar dare. [3]
- wutar ciki - hanzari ko gaggawa ko ujila.
- da damansa suna rigan liman wajen ruku'i ko sujuda ko kabbara, saboda tsananin gaggawa da wutar ciki. [4]
- Saratu tace ke kinfiya wutar ciki.
- wutar kargo - wani irin ƙwaro wanda yakan sa hangara. <> a hairy caterpillar causing blisters if touched (bishiyar kargo = a tree, Bauhinia reticulata).
Google translation of wuta
Fire.