https://archive.org/details/20230520_20230520_1339/page/n11/mode/1up
- Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin K'ai.
- Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilimin tauhidi na Ilahiyya da Rububiyya,
- Mai rahama ya tara dukan/dukka rahamar duniya da rayarwa da matarwa da ciyarwa da shayarwa da tufatarwa. Mai jin k'ai ya tara ni'imar duniya mai dogewa zuwa Lahira kamar imani da na Lahira.
- Mai mallaka ko mai nuna mulkin ranar sakamako, ya had'a dukkan wa'azi.
- Kai muke bauta wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhidin Ilahiyya da ibada amaliyya ko k'auliyya.
- Hanya madaidaiciya, ta had'a dukkan shari'a da hukunce-hukunce.
- Wadanda aka yi wa ni'ima, ya tara dukkan tarihin mutanen kirki. Wadanda aka yi wa fushi, ya tara dukkan tarihin masu tsaurin kai. B'atattu, ya tara tarihin dukkan mai aiki da jahilci ko b'ata.