Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:agony

Discussion page of agony

Glosbe's example sentences of agony [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar agony:
    1. Jesus was in emotional agony and in need of support, but Peter and the others fell asleep repeatedly.
      Yesu yana cikin azaba na motsin rai kuma yana bukatar taimako, amma Bitrus da sauran sun yi barci sau da yawa. [2]

    2. She watched her beloved son die in agony after he was rejected by his people.
      Tana kallo ƙaunataccen ɗanta ya mutu cikin azaba bayan da mutanen garinsu suka ƙi shi. [3]

    3. The agony of this anticipated experience and how it may bring reproach upon his Father is so intense that while Jesus prays, his sweat becomes as drops of blood falling to the ground.
      Azaba da zai fuskanta da yadda ƙila zai kawo kunya ga Ubansa ya yi tsanani har da lokacin da Yesu yake addu’a, guminsa ya yi ƙauri kamar jini da ke ɗiga. [4]

    4. 22:44 —Why did Jesus experience so much agony?
      22:44—Me ya sa Yesu ya sha wahala sosai? [5]

    5. No, the tears that God will wipe out are tears caused by suffering, grief, disappointment, hurt, and agony.
      A’a, hawayen da Allah zai share, hawaye ne da wahala, baƙin ciki, cin mutunci, ɓacin rai, da kuma azaba suke kawowa. [6]

    6. Though Jesus did experience agony before his death, he was not a melancholic individual.
      Ko da yake Yesu ya sha wahala kafin ya mutu, bai nuna cewa yana baƙin ciki a kullum ba. [7]

    7. Never should we forget that the agonizing death that Jesus suffered on the torture stake and the even greater agony that Jehovah endured in watching his beloved Son die are proof of their love for us.
      Kada mu manta cewa mutuwar azaba da Yesu ya sha a kan gungume da kuma azaba mai yawa da Jehovah ya jimre wajen kallon Ɗan da yake ƙauna ya mutu cewa tabbaci ne na ƙaunarsu a gare mu. [8]

    8. Elisha summons the mother and utters the words that must turn her agony into unbridled joy: “Lift up your son.” —Verses 34, 36.
      Elisha ya kira mamar yaron kuma ya furta kalaman da za su mai da baƙin cikinta zuwa farin ciki sosai: Ki “ɗauki ɗanki.”—Ayoyi ta 34, 36. [9]

    9. 13 During his agony on the torture stake, Jesus provided irrefutable confirmation of mankind’s hope.
      13 Sa’ad da yake shan azaba a kan gungumen azaba, Yesu ya ba da tabbaci da ba za a iya ƙaryata ba game da begen ’yan adam. [10]

    10. How did the Father feel as his beloved Son cried out to him in the throes of agony?
      Yaya Uban ya ji yayin da Ɗansa da yake ƙauna ya yi kuka domin ƙunar azaba? [11]

    11. Jesus knew in advance that the noble course that he would take would involve some agony.
      Yesu ya sani tun da fari cewa tafarki mai kyau da zai ɗauka zai ƙunshi shan wasu azaba. [12]

    12. (2 Corinthians 11:28) Jesus was in such agony on the night preceding his death that “his sweat became as drops of blood falling to the ground.”
      (2 Korinthiyawa 11:28) Yesu yana cikin azaba a dare kafin mutuwarsa da “jiɓinsa kuma ya zama kamar manyan ɗararasa na jini, sun[a] fāɗuwa a ƙasa.” [13]

    13. Why is Jesus in agony in the garden of Gethsemane?
      Me ya sa Yesu ya yi baƙin ciki sosai cikin gonar Jathsaimani? [14]

    14. (Ecclesiastes 9:5) It is impossible for the dead, who are “conscious of nothing at all,” to experience agony anywhere.
      (Mai-Wa’azi 9:5) Ba zai yiwu ba matattu, da “ba su san kome ba,” su sha azaba a ko’ina. [15]

    15. In the near future, Jehovah will remove all problems, suffering, and agony.
      Jehobah ya kusan kawo ƙarshen dukan wahala da baƙin ciki. [16]

    16. How her family and friends wished they could simply remove her disease and her agony!
      Iyalinta da abokanta sun ji kamar su samu ikon cire mata ciwon da kuma azabar! [17]

    17. All enemies of God’s Kingdom will then be forced to witness an event that will intensify their agony.
      Dukan maƙiyan Mulkin Allah za su shaida aukuwar da za ta daɗa ruɗar da su. [18]

    18. 6:23) The apostle Paul felt this pain and agony deeply.
      6:23) Manzo Bulus ya yi baƙin ciki sosai don shi bawa ne ga zunubi. [19]

    19. (Hebrews 12:2) Whatever opposition or persecution Jesus had to face —even the agony of the torture stake— he kept his mind on “the joy that was set before him.”
      (Ibraniyawa 12:2) Ko da wace irin hamayya da tsanani da Yesu zai fuskanta—har azaba a kan gungume—ya sa zuciyarsa a kan “farin cikin da aka sa gabansa.” [20]

    20. He suffered such agony over God’s disapproval that he felt like a man whose bones were crushed
      Ya yi baƙin ciki sosai don zunubin da ya yi kuma hakan ya sa ya ji kamar mutumin da aka kakkarya ƙasusuwansa [21]

    21. Why did Jesus experience such agony?
      Me ya sa Yesu ya sha irin wannan azabar? [22]

    22. (Hebrews 5:7) David was convinced that Jehovah observed him and would remember his agony, as if preserving his tears in a skin bottle or inscribing them in a book.
      (Ibraniyawa 5:7) Dauda ya tabbata cewa Jehobah ya lura da shi kuma zai tuna da wahalarsa, kamar dai ya lissafa yawan hawayensa ne ko kuma ya rubuta su cikin littafi. [23]

    23. While in the garden of Gethsemane, Jesus was “deeply grieved” and got “into an agony.”
      Yayin da yake lambun Gatsemani, Yesu ‘ransa ya sha wahala matuƙa’ ya ‘sha azaba.’ [24]

    24. He prayed earnestly, even “getting into an agony.”
      Ya yi addu’a da naciya, “cikin raɗaɗi.” [25]

    25. Reflect for a moment on the agony and suffering that disregard for the Golden Rule has brought on mankind since the rebellion in Eden, instigated by Satan the Devil.
      Ka yi ɗan bimbini bisa azaba da wahala da yasar da Ƙa’idar Ja-Gora ta kawo bisa ’yan Adam, tun tawaye a Adnin da Shaiɗan Iblis ya zuga. [26]


Retrieved June 23, 2019, 12:12 pm via glosbe (pid: 470)