Hakkin Iyaye - 2020 Ramadan Tafsirul Qur'an Day 12 with Dr Isa Ali Pantami - May 5, 2020
Tambaya/Question: Malam Allah ya jiƙan mahaifanka da rahama. Ameen ya hayyu ya qayyum! Da alaramma, da sauran 'yan uwa duka da ke sauraro. Ya kuma musu sakamako da aljannah maɗaukakiya. Malam menene mafita ga wanda mahaifiyarsa ta bar duniya ta na fushi da shi? A yanzu rayuwa ta masa ƙunshi amma mahaifinsa yana raye. Menene abinda zai yi?
An yi wannan tambaya zuwa ga Sheik Abdul Aziz bin Baaz (rA) a cikin fatawowi da yake amsawa. Ya fara maganar da tausayawa wanda ya samu kansa a wannan hali. Ya ce tozarta haƙƙin iyaye, uwa da uba, wallahi al'amarin yana da hatsari mai girman gaske a ce mutum ya taɓa haƙƙinsu yana ɗa. Taɓa hakkin iyaye yana daga cikin manya-manyan zunubai a wurin Allah. Wanda suka fi kowanne girma. A wani babi ma, daga shirka, sai kuma taɓa hakkin iyaye ake kawowa. Daga an ce shirka sai a ce iyaye. In mutum ya taɓa hakkinsu bayan ya taɓa hakkin Allah na tarayya (association), toh sai na iyaye. Ya ce don haka, yana daga cikin mafi girman zunubai a rayuwa da mutum zai iya aikatawa. Kuma yaddarsu na jawo shiga aljannah. Fushin su akan mutum na jawo masa fushin Allah (sA) tun a nan duniya har zuwa lahira. Don haka ya ce bala'i ya kai bala'i. Fitina ta kai fitina. A ce mutum ya taɓa hakkin iyaye, musamman wadda take uwa, wadda idan ma ana neman lafiyar zunubi, ita ake kyautatawa.
Wani mutum ya sami Abdullahi bin Abbas (rA), ya ce masa: Ni ne na yi zunubi na kuskure, har ya sa kuskuren ya sa ya kashe mutum. Don Allah akwai wani aikin alheri... da idan na yi, Allah zai iya yafe mini wannan zunubi nawa? Sai ya ce za a iya samu. Sai ya ce masa mahaifiyarka tana raye? Sai ya ce masa ba ta raye...
Links
- Darajan Iyaye: https://youtu.be/lrPG43xmWXE
- Cikkakken bidiyon: https://youtu.be/ijF-slliDE0?t=1322
- 2020 Ramadan Tafsirul Qur'an Day 12 with Dr Isa Ali Pantami - May 5, 2020
- Download the clip: https://www.kapwing.com/videos/5eb1b098b1b6280013d2dbac / https://kapwi.ng/c/43kgCaLx
- Karin bayanai game da hakkin iyaye: https://www.alhassanain.com/hausa/articles/articles/family_and_community_library/family_and_child/4haqqin_iyaye/001.html