# | English | Hausa |
---|---|---|
1 | US approves $1B arms sale to Nigeria despite rights concerns --AP | Amurka Ta Amince Da Siyarwa Najeriya Makaman Dala Biliyan Daya --VOAHausa, Aminiya |
2 | The Biden administration has given the green light for Nigeria to buy advanced attack helicopters worth nearly $1 billion despite concerns about the country’s human rights record as it battles threats from criminal gangs and extremists in the north. | Gwamnatin Biden ta baiwa Najeriya damar siyan manyan jirage masu saukar ungulu na kai hare-hare na kusan dalar Amurka biliyan 1 duk da damuwar da kasar ke da ita ta zargin take hakkin bil adama yayin da kuma take fama da barazanar kungiyoyin 'yan bindiga da masu tsattsauran ra'ayi a arewacin kasar. |
3 | The State Department on Thursday announced the approval of the $997 million sale of 24 Bell AH-1Z Viper helicopters and related equipment to Nigeria. |
A ranar Alhamis ne ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da amincewa da sayar da dala miliyan 997 na jirage masu saukar ungulu da ake kira Bell AH-1Z Viper guda 24 da makamantansu ga Najeriya. |
4 | The related equipment includes guidance, night vision and targeting systems as well as engines and training support, the department said in a notice to Congress. | Kayayyakin sun haɗa da na’urar hangen nesa da daddare da wasu na’urori da injuna da tallafin horo, in ji sanarwar ga Majalisa. |
5 | The sale went ahead after a November visit to Abuja by Secretary of State Antony Blinken during which he raised concerns about Nigeria’s rights record. | An ci gaba da cinikin ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai Abuja a watan Nuwamba inda ya nuna damuwarsa game da take hakkin bil Adama a Najeriya. |
6 | At the time, though, Blinken also made clear that the United States regards Nigeria as a partner in combating terrorism and Islamic extremism in West Africa and the Sahel, a region along the Sahara Desert stretching across North Africa, and is looking to increase cooperation with it in those areas. | A yayin ziyarar, Blinken ya kuma bayyana cewa, Amurka na daukar Najeriya a matsayin abokiyar kawance wajen yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayin IS a yammacin Afirka da kuma yankin Sahel, yankin da ke gabar hamadar Sahara da ke fadin arewacin Afirka, kuma tana neman kara hadin gwiwa da ita a cikin wadannan yankunan. |
7 | Nigeria’s security forces have long been accused of human rights violations in their operations... | An dade ana zargin jami'an tsaron Najeriya da take hakkin bil'adama a ayyukansu. |
8 | In October 2020, the army opened fire at a demonstration in the country’s economic hub where hundreds were protesting against police brutality, killing 11 people and injuring many others, according to a government-backed panel. | A watan Oktoban 2020, sojoji sun bude wuta a wata zanga-zanga a cibiyar tattalin arzikin kasar kan daruruwan mutane da ke zanga-zangar nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda, inda suka kashe mutane 11 tare da jikkata wasu da dama, a cewar wani kwamitin da gwamnati ke marawa baya. |
9 | During Blinken’s visit on November, he said the U.S. was looking forward to seeing the full results of the investigation and would make a decision on arms sales to Nigeria based in part on the findings and whether those responsible were held accountable. | A ziyarar da Blinken ya kai a watan Nuwamba, ya ce Amurka na fatan ganin cikakken sakamakon binciken kuma za ta yanke shawara kan sayar da makamai ga Najeriya biyo bayan binciken da aka yi na wadanda ke da hannu a lamarin kuma a hukunta su. |
10 | Nigeria is also facing a growing threat from armed gangs and extremist rebels who are now working together in the country’s troubled northwest and threaten to further destabilize an already volatile region. | Har ila yau Najeriya na fuskantar barazana daga kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma 'yan ta’adda masu tsattsauran ra'ayi wadanda a yanzu ke aiki tare a yankin arewa maso yammacin kasar da ke fama da rikici tare da yin barazanar kara dagula al'amura a yankin da ke fama da rikici. |
11 | Nigeria, Africa’s most populous country with 206 million people, has been battling violence in the north and an alliance between the two groups could worsen the crisis, analysts believe. | Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afirka mai yawan mutane miliyan 206, tana fama da tashe-tashen hankula a arewacin kasar. |