https://archive.org/details/20230520_20230520_1339/page/n11/mode/1up
- Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilimin tauhidi na Ilahiyya da Rububiyya,
- Mai rahama ya tara dukan/dukka rahamar duniya da rayarwa da matarwa da ciyarwa da shayarwa da tufatarwa. Mai jin k'ai ya tara ni'imar duniya mai dogewa zuwa Lahira kamar imani da na Lahira.
- Mai mallaka ko mai nuna mulkin ranar sakamako, ya had'a dukkan wa'azi.
- Kai muke bauta wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhidin Ilahiyya da ibada amaliyya ko k'auliyya.
- Hanya madaidaiciya, ta had'a dukkan shari'a da hukunce-hukunce.