Verb
fuskanta | fuskanci | fuskance | fuskanto (faced)
- to face, head for <> gabata ko tunkara, juya.
- Salla ibada ce mai fuskanto bawa zuwa ga daukakar rayuwar lahira da kawar da tunaninsa da dukkan rayuwar duniya da zoginta. [1]
- have an opinion or point of view about <> samun ra'ayi
- Na fuskanci abun duk rashin gaskiya ne. <> I am of the opinion that all of it is false.
- Kotun ICC na fuskantar kalubalen kauracewa <> The ICC court faces boycott challenges. [2]