Mubuɗin Sura
- Sunanta: Wannan Sura ta fi shahara da Suratul Asri amma a wasu littattafan tafsiri da Sahihul Bukhari an kira ta Suratu Wal-Asri.
- Sanda aka saukar da ita: Sura ce Makkiyya.
- Jerin saukarta: Ita ce Sura ta goma sha uku (13) a jerin saukar surorin Alƙur'ani, ta sauka bayan Suratus Sharhi kafin Suratul Adiyat.
- Adadin ayoyinta uku ne (3).
- Falalarta: An karɓo daga Abu Madina Ad-Darimi ya ce: "Idan mutum biyu daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) suka haɗu, to ba za su rabu ba har sai ɗaya ya karanta wa ɗayan Suratul Asri sannan su yi sallama da juna. [Abu Dawud]
- Babban Jigonta: Duk rayuwa ɗan'adam asara ce idan babu bin Allah a cikinta.
- Daga cikin abubuwan da ta ƙunsa akwai:
- Tabbatar da tsananin asara ga waɗanda suka kafirce wa Allah suka rungumi saɓon Allah.
- Tabbatar da tsira ga muminai masu kyawawan ayyuka masu kira zuwa ga gaskiya.
- Falalar haƙuri a kan bin gaskiya da kauce wa ƙarya da jajircewa a kan haka.
Tarjama da tafsirin aya ta 1-3
- Na rantse da zamani.
- Lalle mutum yana cikin asara.
- Sai dai waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna waiyya da haƙuri.
Tafsiri
Allah ya buɗe surar da rantsuwa da zamani wanda ƙunshi dare da rana waɗanda su ne mahallin dukkan ayyukan bayi.