Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/103/RijiyarLemo

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 18:54, 26 March 2022 by Admin (talk | contribs)

Quran/103

Mubuɗin Sura

  1. Sunanta: Wannan Sura ta fi shahara da Suratul Asri amma a wasu littattafan tafsiri da Sahihul Bukhari an kira ta Suratu Wal-Asri.
  2. Sanda aka saukar da ita: Sura ce Makkiyya.
  3. Jerin saukarta: Ita ce Sura ta goma sha uku (13) a jerin saukar surorin Alƙur'ani, ta sauka bayan Suratus Sharhi kafin Suratul Adiyat.
  4. Adadin ayoyinta uku ne (3).
  5. Falalarta: An karɓo daga Abu Madina Ad-Darimi ya ce: "Idan mutum biyu daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) suka haɗu, to ba za su rabu ba har sai ɗaya ya karanta wa ɗayan Suratul Asri sannan su yi sallama da juna. [Abu Dawud]
  6. Babban Jigonta: Duk rayuwa ɗan'adam asara ce idan babu bin Allah a cikinta.
  7. Daga cikin abubuwan da ta ƙunsa akwai:
    1. Tabbatar da tsananin asara ga waɗanda suka kafirce wa Allah suka rungumi saɓon Allah.
    2. Tabbatar da tsira ga muminai masu kyawawan ayyuka masu kira zuwa ga gaskiya.
    3. Falalar haƙuri a kan bin gaskiya da kauce wa ƙarya da jajircewa a kan haka.

Tarjama da tafsirin aya ta 1-3

  1. Na rantse da zamani.
  2. Lalle mutum yana cikin asara.
  3. Sai dai waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna waiyya da haƙuri.

Tafsiri

Allah ya buɗe surar da rantsuwa da zamani wanda ƙunshi dare da rana waɗanda su ne mahallin dukkan ayyukan bayi. Ya yi wannan rantsuwa ne kuwa domin ya tabbatar da cewa, duk wani ɗan'adam yana cikin asara a rayuwa, kowa da gwargwadon tasa asarar.

Sai Allah ya togace wasu bayinsa daga aukawa cikin wannan asara, su ne kuwa waɗanda suka siffantu da siffofi huɗu:

  1. Imani da Allah duk abin da ya umarci bawa ya yi imani da shi, wanda hakan ba zai yiwu ba sai da ilimin sanin Allah.