Tafsirin ayoyin 1-5 na Surar Ali Imran
Allah ya bude wannan Sura da harrufa kamar yadda ya yi a Baqara, domin bayanin mu'ujizar Alƙur'ani, don nuna babu mai iya kawo kamarsa, duk kuwa da cewa magana ce da ta kunshi haruffa na Larabawa irin wadanda suke rubutu da su. Sannan Allah ya yi bayanin Allantakarsa da cewa, shi ne abin bauta na gaskiya, wanda daga cikin siffofinsa, shi ne Rayayye, mai cikakkiyar rayuwa, wadda ta siffantu da dukkan siffofi na kamala, Tsayayye da Zatinsa, ba shi da bukata a wurin wani cikin halittarsa, kuma shi ne mai tsayawa da taimakon kowa da komai, don haka kowa yana da bukata a wurinsa. Daga cikin taimakonsa da rahamarsa ga bayinsa, shi ne ya aiko musu da Annabi SAW, ya kuma saukar masa da Alkur'ani, wanda yake cike da gaskiya, kuma yake gaskata littattafan da suka gabace shi. Kuma Allah ya saukar da Attaura ga Annabi Musa (alaihissalam) da Linjila ga Annabi Isa (aS) tun kafin saukar da Alkur'ani. Allah ya saukar da littattafan nan ne dukkansu saboda shiriyar da mutane. A cikinsu Allah ya saukar da bin da yake bambancewa tsakanin ƙarya da gaskiya da tsakanin shiriya da ɓata, saboda haka Allah ya yi alkawarin azaba mai tsanani ga wadanda suka kafirce wa ayoyinsa a ranar gobe kiyama. Allah SWT babu wanda zai iya rinjayar sa, kuma babu abin da zai gagare shi, kuma shi mai gaggawar daukar fansa ne ga wanda ya saba masa.
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Kasancewar dalilin saukar ayoyin farko na wanna Sura shi ne jayayyar da Nasaran Najrana suka yi da Annabi SAW dangane da sha'anin Annabi Isa (aS), sai ya zamana ya dace a bude wannan Sura da wadannan haruffa, wadanda suke ishara zuwa ga kalubalantar masu karyata Alkur'ani.
- Faɗar Allah SWT cewa: "Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai shi..." mayar da martani ne ga Nasara masu cewa Annabi Isa (aS) Allah ne.
- Siffofin nan na Allah guda biyu, (Rayayye da Tsayayye da Zatinsa) hada su wuri guda yana nuna siffantuwar Allah da dukkan siffofi na kamala. 'Rayayye' yana nufin kamalar siffofinsa duka, 'Tsayayye da Zatinsa' yana nufin kamalar ayyukansa gaba daya, don haka sun kunshi kamalar Zati, da kamalar ayyuka.
- Attaura da Linjila shiriya ne ga mutane a lokacinsu, amma bayan saukar da Alkur'ani, babu wata shiriya da ta rage sai ta Alkur'ani kadai.
- Musulunci shi ne addinin gaskiya, wanda ya hada bautar Allah shi kadai da kuma imani da annabawan Allah gaba daya.
Tarjama da Tafsirin aya 5-9
A wadannan ayoyin, Allah yana bayanin gamammen iliminsa, wanda ya kewaye komai, don babu wani abu da yake ɓuya a gare shi, a sama yake ko a ƙasa. Shi ne yake halittar ku bisa kamanni daban-daban a cikin iyayenku yadda ya ga dama, don haka shi ne kadai ya cancanta a bauta wa; ba shi da wani abokin tarayya. Shi ne Mabuwayi a cikin mulkinsa; ba mai iya ja da shi ko ya fi karfinsa, kuma shi mai hikima ne a cikin ayyukansa da shari'unsa, babu wani tasgaro a cikinsu ko kadan. Shi ne wanda ya saukar wa wannan Annabi Alkur'ani, wanda ya kunshi ayoyin da suke a fili, ma'anoninsu a bayyane suke, babu wani abu mai rikitarwa tare da su, ma'anoninsu a bayyane suke, babu wani abu mai rikitarwa tare da su, su ne kuma tushen wannan littafi, kuma su ne mafiya yawa a cikinsa. A cikinsa kuma akwai wadansu ayoyi wadanda ma'anarsu take da rikitarwa ga wasu mutane. To amma sai a samu wadansu karkatattun mutane masu cutar kauce wa gaskiya a zukatansu, suna bibiyar wadannan ayoyi masu rikitarwa, suna barin ayoyin da ma'anoninsu suke a fili, ba don su sami wani abu da za su kafa hujja da shi a kan soye-soyen zukatansu. Su kuwa wadannan ayoyi masu rikitarwa, babu wanda ya san hakikanin fassararsu sai Allah. Malamai masu zurfin ilimi na Alkur'ani su ma sukan san tafsirin ma'anonin ayoyin, amma ba za su iya sanin hakikanin al'amarin ba, da yadda karshen zai kasance, domin wannan Allah ne kadai ya san shi. Malamai masu zurfin ilimi sukan shelanta imaninsu da wadannan ayoyi masu rikitarwa. Duk kuma ayoyin na Alkur'ani daga Allah ne, amma ba kowa ne yake wa'azantuwa ba sai masu lafiyayyen hankali.
An karbo daga A'isha (rA) ta ce: "Annabi SAW ya karanta wannan ayar, sai ya ce: "Idan kika ga wadanda suke bibiyar ayoyi masu rikitarwa a cikin Alkur'ani; to su ne wadanda Allah ya ambata, don haka ki guje su." (When you see such verses, avoid them, for it is they whom Allah has pointed out (in the mentioned verses)[1]).
Malamai masu zurfin ilimi addu'a suke yi ko da yaushe, suna rokon Allah kada ya karkatar da zukatansu su saki shiriya bayan Allah ya shiryar da su, ya yi musu rahama, ya kara m usu imani da tsayuwa a kan gaskiya, domin Allah shi ne mai yawan kyauta da ihsani ga bayinsa. Kuma suna addu'a suna cewa:
"Ya Allah, kai ne za ka tara mutane a rana Alkiyama, ranar da babu shakka a zuwanta, domin yin hukunci da sakayya ga kowa a kan aikinsa, don haka ka gafarta mana a wannan ranar, ka yi mana afuwa."
Sun kuma yi Imani da cewa, lalle Allah ba ya saba alkawarinsa na cewa, wanda duk ya yi imani da shi, ya bi Manzonsa; to zai gafarta masa.
An karbo daga Abdullahi dan Amru ya ce, Annabi SAW ya ce:
Abdullah b. Amr b. al-'As reported that he heard Allah's Messenger (ﷺ) as saying:
"Lalle zukatan 'yan'adam duka suna tsakanin yatsu biyu ne
Verily, the hearts of all the sons of Adam are between the two fingers
daga yatsun Allah Mai rahama, tamkar zuciya daya,
out of the fingers of the Compassionate Lord as one heart.
yana sarrafa su yadda ya ga dama."
He turns that to any (direction) He likes.
Sannan sai Annabi SAW ya yi addu'a yana cewa: "Ya Allah Mai sarrafa zukata, ka sarrafa zukatanmu a kan da'arka."
Then Allahs Messenger (ﷺ) said: O Allah, the Turner of the hearts, turn our hearts to Thine obedience. [2]
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Jan hankalin dan'adam a kan ya kyautata halayensa, da ayyukasa, domin Allah Mahaliccinsa yana ganin sa, babu abin da yake ɓuya a gare shi.
- Yana daga cikin alamomin karkacewar zuciya, bibiyar ayoyin Alkur'ani masu rikitarwa, don mutum ya saka kansa ko wasu cikin shakka.
- Idan mai karatu ya yi wakafi a daidai (illallahu) to hakan yana nuna a cikin Alkur'ani akwai abin da babu wanda ya san fassararsa sai Allah. Fassara a nan, ko kuma 'tawili', kamar yadda ya zo a ayar, ana nufin karshen al'amari, ko kuma yadda hakikanin al'amarin zai kasance. A nan akwai jarrabawa da Allah yake yi wa bayinsa game da abubuwan da ba za su iya fahintar su da tsurar hankalinsu ba. Shin za su ce sai sun gano su ta haka, ko kuwa za su sallama wa Allah SWT su tsaya a matsayinsu?
- Babu masu jayayya da abin da ya zo daga Allah sai masu karamin sani, wadanda ba su yi zurfi ba a cikin ilimi. Wannan yana nuna falalar yin ilimin shari'a mai zurfi, domin yana taimakawa wajen samun tsayuwa a kan gaskiya.
- Daga wannan aya za mu fahimci cewa akwai abin da ake kira 'ilimi', akwai kuma kafuwa da zurfi cikin ilimin, don haka mai neman ilimi kada ya hakura da dan kadan, ya yi kokarin kafuwa da zurfi a cikinsa.
- Babu mai amfana da wa'azuzzukan Alkur'ani sai masu hankali. Duk sa'adda hankalin mutum ya karu; to fahintarsa ga Alkur'ani za ta karu, duk sa'adda ka ga ba ya wa'azantuwa da Alkur'ani; to hakan yana nuna karancin hankalinsa ne.
- Zuciya tana da hali guda biyu, halin daidaita da kuma halin karkata, don haka mutum a ko da yaushe yana bukatar ya rika rokon Allah da kada zuciyarsa ta karkace, domin ba a hannunsa take ba, tana hannun Allah ne, shi ne yake yin yadda ya ga dama da ita, don haka kada mutum ya rudu da kansa, ya dogara a kan imaninsa, sau tari an sami mai imanin da ya tabe, ya saki hanya.
- Idan mutum ya samu kubuta daga fitinar shubuha, da fitinar sha'awa; to ya gama samun manyan bukatunsa biyu na duniya da lahira, su ne shiriya da rahama.
Tarjama da Tafsirin aya 10-11
Bayan Allah SWT ya ambaci ranar lahira, ya kuma tabbatar da cewa, rana ce da babu kokwanto ga zuwanta, ya kuma ambaci halin muminai na neman gafara da afuwar Allah a wannan ranar, sai kuma a wadannan ayoyi Allah SWT ya kawo bayanin kafirai da yadda halinsu zai zamanto a wannan ranar. Allah Ta'ala ya bayyana cewa wadanda suka kafirce wa Allah da ayoyinsa, kuma suka karyata manzanninsa, suka nuna musu kiyayya, kuma suka bijire wa addinin Allah; to wadannan dukiyoyinsu da 'ya'yansu ba za su taɓa yi musu amfani ba, kuma ba za su kubutar da su daga azabar Allah ba, yayin da ta zo musu. Makomarsu ita ce wutar Jahannama, su ne makamashinta da za a rika rura ta, kuma za su dawwama a cikinta har abada, babu ranar fitarsu. Wannan sunnar Allah ce wadda ba ta canzawa. Al'amarin wadannan daidai yake da al'amarin Fir'auna da jama'arsa da sauran al'ummomin da suka karyata Allah da manzanninsa, su ma haka Allah ya halakar da su saboda zaluncinsu, haka da ma Allah yake, mai tsananin ukuba ne ga duk wanda ya bijire masa, ya ki tuba ya dawo gare shi.
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Kada mutum ya rudu da da yawan dukiya ko 'ya'ya ko wani kyale-kyale na duniya, su sa shi ya yi ta saɓawa Allah; ranar da azabar Allah ta zo masa, duk wadannan abubuwa ba za su amfane shi da komai a wurin Allah ba.
- Mumini yana amfana da dukiyarsa da 'ya'yansa a lahira idan ya tafiyar da su kamar yadda Allah ya tsara masa.
- Duk kafirci a wurin Allah iri daya ne, na da da na yanzu, babu bambanci.
- Zunubban bayi su ne suke jawowa Allah ya halaka su, amma ba don zalunci ba. Allah ba azzalumin kowa ba ne. Sunnar Allah yana gudanar da ita a kan kowa a kowane wuri, kuma a kowane zamani, don haka babu inda mai laifi zai gudu ya kubuta.
Tarjama da Tafsirin aya 12-14
A wadannan ayoyi, Allah yana umartar Manzonsa (SAW) da ya faɗawa kafirai cewa, muminai sai sun yi rinjaye a kansu a rayuwarsu ta duniya, sannan idan ranar alƙiyama ta tsaya, a tarkata su gaba daya cikin wutar Jahannama, domin ita ce shimfidar da suka tanadar wa kawunansu tun a nan duniya. Tir kuwa da wannan shimfida.
Allah SWT kuma ya bayyana wa kafirai ko kuma muminai cewa, sun ga alama a fili da ta nuna muminai ne za su yi rinjaye a kan kafirai, kuma Allah ya yi alkawarin zai daukaka addininsa, kuma ya karfafi Manzonsa. Wannan alama ita ce, kungiyoyin mayaka biyu da suka hadu don kafsa yaki a tsakaninsu. Kungiyar farko muminai ne, masu yaki don daukaka kalmar Allah, su ne Annabi da Musulmi a yakin Badar; daya kungiyar kuma kafirai ne, suna yaki ba don Allah ba, su ne Quraishawa kafiran Makka a ranar Badar. A lokacin, muminai suna ganin kafirai a ido, sun ninka su gida biyu, Wannan kuwa ya ƙara musu dogaro ga Allah da neman taimakonsa, wanda yin hakan yana daga cikin dalilan samun nasara. To yadda Allah ya ba wa wadannan muminai 'yan kadan nasara a kan abokan gabarsu masu yawa, akwai darasi da wa'azi ga duk wanda Allah ya ba shi basira da hangen nesa.
Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Da a ce