Toggle menu
24K
665
183
158.3K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/114

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Category:Quran/114

Arabic-English recitation of Quran/114

114

Rijiyar Lemo's Tafsir ɗin 114 - Suratun Nasi

Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Jefa mummunan waswasi a cikin zukatan bayi wani makami ne na shaiɗanun na aljanu da mutane.
  2. Babban makamin bawa don magance waswasin Shaidan shi ne ambaton Allah (ﷻ).
  3. Tawassuli da kamun ƙafa da Rububiyy ar Allah don samun kariya daga duk wani sharri na ɓoye, na mutum da na aljan.
  4. Gwagwarmaya tsakanin ɗan’adam da Shaidan ba za ta kare ba har zuwa tashin alƙiyama, don ɗan’adam ba ya da wani makamin yakiar Shaidan da karya shi sai ta hanyar riƙo da hanyar Allah da yawan ambaton sa da tsayawa a kan iyakokinsa.

From these ayats, we'll understand the following: Quran/114/GoogleTranslate

  1. Hurling evil whispers in the hearts of the servants is a tool of the devils of the jinns and mankind.
  2. The

Links for Surat An-Nas (The Mankind)

  1. http://quran.com/114
  2. http://www.masjidtucson.org/hausa/Surah_114.pdf
  3. https://archive.org/details/SurahAlNaas114-Mankind-MiracleDreamTafseer-NoumanAliKhan, Audio 1, Audio 2
  4. http://www.islamicstudies.info/tafheem.php?sura=114&verse=1&to=6
  5. Quizlets https://quizlet.com/subject/quran-114/
    1. https://quizlet.com/_1m6bz6
    2. https://quizlet.com/za/342599723/114-surah-naas-flash-cards/
  6. https://www.youtube.com/watch?v=U6u8WTn-LeY

  1. قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ Qul a’uzu birabbinnas <> Say: I seek refuge in the Lord of mankind <> Ka ce: Ina neman tsari ga Ubangijin mutane.
    Say, "I seek refuge in the Lord of mankind, = Say, ˹O Prophet,˺ “I seek refuge in the Lord of humankind, <> Ka ce "Ina neman tsari ga Ubangijin mutane." = Ka ce, "Ina neman tsari ga Ubangijin mutane." --Qur'an 114:1
  2. مَلِكِ النَّاسِ Malikinnas <> The Owner/King/Sovereign/Master of mankind <> Mamallakin / sarkin mutane.
  3. إِلَٰهِ النَّاسِ Ilahinnas <> The God of mankind <> Abin bautawar mutane.
  4. مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ Min sharril waswasil khannas <> From the evil of the retreating whisperer = from the evil of the lurking (see also: Quran/81/15 and the Qur'an corpus) whisperer <> Daga sharrin mai sanya wasuwasi, mai ɓoyewa/sulalewa/nokewa
  5. الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ Allaziyu waswisu fee sudoorinnas <> Who whispers evil into the hearts/breasts/chests of mankind <> Mai sanya wasuwasi cikin sadarin/ƙirzan/ƙirazan mutane.
  6. مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ Minal jinnatu wannas <> From among the jinn and mankind <> Daga aljanu/aljannu da na mutane.

114 Suratul Nasi

Mabuɗin Sura:

  1. Sunanta: Wannan Sura ta shahara da suna Suratun Nasi, amma a hadisai da yawa an kira ta da Suratu Ƙul A'uzu Bi Rabbin Nas kamar yadda ya gabata a Suratul Falaƙ.
  2. Sanda aka saukar da ita: Sura ce Makkiyya a wurin yawancin malamai.
  3. Jerin saukarta: Ita ce Sura ta ashirin da ɗaya (21), ta sauka bayan Suratul Falaƙ kafin Suratul Ikhlas.
  4. Adadin ayoyinta: 6.
  5. Falalarta: Dubi hadisan falalar Suratul Falaƙ.
  6. Dalilan saukarta: Dubi dalilin saukar Suratul Falaƙ.
  7. Babban jigonta: Tana nuna neman tsarin Allah (swt) da kariyarsa daga sharrin Shaiɗan da waswasinsa tare da duk wani ɓoyayyen sharri.

Tafsiri

Allah (swt) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (saw) da ya nemi tsarin Ubangijin mutane, kuma Sarkinsu mai cikakken iko da yin yadda ya ga dama da su, abin bautarsu na gaskiya wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai shi kaɗai.Ya yi masa tsari daga sharrin Shaiɗan wanda ke jefa waswasinsa ga ɗan'Adam idan ya gafala ya manta da ambaton Allah, mai noƙewa ya ja baya duk sanda ɗan'Adam ya ambaci Allah. Yana jefa waswasinsa cikin zukatan mutane. Kuma wannan shaiɗani ana samun sa cikin mutane kamar yadda ake samun sa a cikin aljannu.

Ayoyin