Tarjamar Suratul Mulk
- Albarkatun Allah da alheransa sun yawaita, mulki gabaɗaya a hannunSa yake, Shi mai iko ne a bisa dukkan komai. --Quran/67/1
- Shi ne wanda ya halicci mutuwa kuma ya halicci rayuwa, don ya gwada ku, wanene zai kyautata aiki a cikin ku. Shi Mabuwayi ne ƙaƙƙarfa, Mai gafara ga bayinSa waɗanda suka nemi tubanSa. --Quran/67/2
- Shi ne ya halicci sammai guda bakwai (7), wata kan wata, ba tare da wata ta taɓa jikin wata ba. Ba za ka gani ba a cikin halittun da Allah ya yi dangane da wani saɓani ko karkacewa ko illa. Ka mayar da ganin ka sama ka gani, ka duba ga gani, shin za ka samu wani huda ko wani tsaga a jikin sama?
- Sannan ka ƙara mayar da ganin ka sama.